Abu ne mai matuÆ™ar kyau na sama ya lura da buÆ™atu da muradun zucin waÉ—anda ke Æ™asa da shi. Ya ba shi damar fitar da waÉ—annan muradu ta hanyar sake masa fuska da ba shi damar bayyana tunani da ra’ayoyinsa. Wannan zai taimaka wa lafiyar Æ™waÆ™walwar yara da bunÆ™asar kaifin basirarsu. (Sani, A-U. 2023)
Wata hanyar gane muradu da buÆ™atun zuci na yara ita ce lura da alamomi da za su iya nunawa yayin da kawaici da kunya da sauran tanade-tanaden al’ada suka dabaibaiye Æ™warin guiwarsu. (Sani, A-U. 2023)
Tauye tunani da muradun matasa ba tare da bayyana musu dalilin hakan da kuma yi musu ishara da mafifin zaɓi ba, na iya haifar musu da daƙushewar kaifin tunani da sallama rayuwa da fafutukan samun nagartaccen gobe da kuma sakankancewar da ka iya kaiwa ga wofantar zuciya. (Sani, A-U. 2023)
Tara dukiyar da rayuwa da mutuwa ba za su amfana da ita ba, abu ne mai wahalar bayani a matsayin hankali ko hauka! (Sani, A-U. 2023)
Abu mafi burgewa a duniya bai dogara kan halin farin ciki da walwala da kake ciki ba, ya fi dogara kan adadin mutane da sauran halittu da ke samun farin ciki da sauƙin rayuwa dominka - ballantana a lahira! (Sani, A-U. 2023)