Cite this article as: Sani, A-U. & Adamu, S. (2023). Daga Hausar Rukuni Zuwa Ɓoyayyiyar Al’ada: Keɓaɓɓen Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 115-123. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.013.
Abu-Ubaida Sani
Department of Languages and Cultures
Federal University, Gusau, Zamafara, Nigeria
Sani Adamu
Prince International Schools Gusau, Zamfara, Nigeria
+2348135366284
Tsakure
Wannan bincike ya ta’allaƙa ne kan nazarin Hausar teloli. Manufar binciken
shi ne nazartar ire-iren kalmomi da jimloli da teloli ke amfani da su ta hanyar
ba su ma’anonin da suka bambanta da maganar yau da kullum. Kadadar binciken ta
taƙaita a garin Gusau da ke
jahar Zamfara. An yi amfani da tattaunawa a matsayin babbar hanyar tattara
bayanai. A bisa haka ne aka yi hira da teloli daban-daban da ke garin Gusau.
Binciken ya gano cewa, akwai kalmomi da jimloli daban-daban da telolin ke
amfani da su waɗanda suka bai wa ma’anonin da
suka bambanta da na gama-gari. Waɗansu kuwa sukan kasance ƙirƙira ce kai tsaye. Binciken ya kalli wannan a matsayin wani abinci a fagen
nazarin harshe da al’ada. Kundace su da
nazartar su mataki ne na bunƙasa harshe tare da taskacewa da daidaita al’ada musamman yayin fito da tasirin amfani da iren-iren waɗannan Hausar ta rukuni ga zamantakewa.
Fitilun
Kalmomi: Telololi, Hausar Rukuni, Harshe, Al’ada
1.0 Gabatarwa
Masu azancin magana sukan ce "tun kafin a
haifi uwar mai sabulu balbela tana da farinta." Hausawa al'umma ce wadda tun tuni suke da tsarin tattalin arziki. Wannan ne ya
sa sana'o'i suka yi tasiri a gidajen Hausawa. Da wuya a da can
a samu wani gidan Hausawa a ƙasar Hausa da ba su da sana’a.[1] Duk da
haka, sana’o’in sukan samu sauye-sauye musamman sakamakon tasirin zamani da
shirye-shiryen game-duniya.
A ɓangare guda kuwa, sana'ar ɗinki sana'a ce wadda take tafiya tare da zamani. Tana samun sauye-sauye kamar yadda
zamani yakan
sauya. Akan samu sauyi dangane da kayayyakin da ake ɗinkawa ko kayan aiki da sauran
abubuwa da suka shafi sana’ar kai tsaye ko a kaikaice. Wannan ne ma ya
sa duk mai son ya yi
dogon zamani a ɗinki, to dole ne sai ya tafi tare da zamani.[2]
Tuni aka samu
Hausar rukuni a tsakanin maɗinka
biyo bayan buƙatu na al’adar
zamantakewa da hulɗayya. A
waɗansu lokutan,
Hausar teloli ta shafi aikin sana’ar ɗinki kai tsaye, wato tun daga kan kayan aikin ɗinki zuwa aiwatar da ɗinkin da kuma kayayyakin da ake ɗinkawa. A waɗansu lokutan kuwa, buƙatun sakayawa da sirrinta zance ne yakan samar da
Hausar teloli. A bisa la’akari da
haka ne wannan takarda ta ɗora sana’ar
ɗinki a faifan nazari musamman domin ƙwanƙwance abin da ke
da akwai cikin Hausar teloli.
Kai tsaye,
tambayoyin da nazarin ke son amsawa su ne (i) Ga Bahaushen yau, me ake nufi da ɗinki kuma yaya ake aiwatar da shi? (ii) Waɗanne nau’ukan maɗinka ake da su a farfajiyar binciken? (iii) Yaya
yanayi da misalan Hausar telolin farfajiyar binciken suke? (iv) Mene ne tasirin
wannan Hausar a muhallin harshe da al’ada Bahaushiya?
1.1 Dabarun
gudanar da bincike
Kasancewar
kadadar binciken ba ta tsallake al’ada da harshen Bahaushe ba, bai zama dole a
yi amfani da Baturen ra’i wajen gudanar da shi ba. A maimakon haka, an ɗora shi a kan hanyar gudanar da bincike da ta dace da Bahaushiyar al’ada.[3] Ya gudana ne a
kan tunanin Bahaushe na “kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.” A fahimtar
wannan ra’ayi, ba abin mamaki ne ba idan
aka samu waɗansu keɓaɓɓun
al’adu da kuma harshe na musamman a wurin maɗinka. Ma’ana ke nan su ma za su yi “kukan gidansu”
na sana’ar ɗinki.
Dangane da
farfajiyar bincike kuwa, yana da kyau a lura da cewa ko a cikin ƙasar Hausa, akan
samu bambance-bambance game da yadda ake gudanar da waɗansu sana’o’i daga wuri zuwa wuri. Farfajiyar wannan bincike ta taƙaita ne a cikin ƙwaryar garin Gusau. Binciken
ya mayar da hankali kan Hausar teloli a garin Gusau ta fuskar:
i.
Kayan aiki
ii.
Yanayin gudanar da ayyuka
iii.
Sunayen ayyuka
iv.
Sakaya zance (ɓad-da-bami)
Domin samun sauƙin aikin, an
kasa muhallin binciken zuwa sassa uku wato (i) Gusau ta Yamma da ta haɗa da Birnin Ruwa da Ƙofar Yarima (Bakin
Silma) da Bakin Tsohuwar Kasuwa da yankin Sabon Fegi, (ii) Gusau ta Tsakiya da
ta haɗa da Sabon Gari da
Mutuwa Geji (Mortgage) da Bakin Total da Tashar Magami, (iii) Gusau ta Gabas da
ta ƙunshi
Tudun Wada da Unguwar Gwaza da Samaru da Hayin Malam Sani da Damɓa.[4] An tuntuɓi Teloli daban-daban daga waɗannan yankuna domin samun ingantattun
bayanai daga tushe. Kasancewar daga cikin telolin akwai waɗanda ba su da ilimin karatu da rubutu na boko, an zaɓi tattaunawa a matsayin hanyar tattara
bayanai.
2.0 Teloli
a garin Gusau
Kalmar tela ararriya
ce daga harshen Ingilishi. A gadajjiyar al’ada, Bahaushe na kiran wanda ke
sana’ar[5] ɗinki da suna “maɗinki.” A jam’i kuma sai ya ce “maɗinka.” A ƙasar Hausa a yau, ararriyar kalmar wato “tela” ta karaɗe ko’ina. Da zarar an ambace ta, hankalin mai
sauraro zai koma kan ɗinki
irin wanda ake aiwatarwa a zamanin yau.
Ɗinki na ɗaya daga cikin daɗaɗɗun
sana’o’in Bahaushe gadaddu. Alhassan da wasu, (1982 p. 54-55) sun bayar
da ma'anar ɗinki na
gama-gari a matsayin hanyar "haɗa sawaye
da wani abu saƙaƙƙe a
mayar da shi tufa ko wani abin sawa a jiki da taimakon zare da allura ko ƙayar aduwa ko basilla."
A cikin wannan
bincike, an mayar da hankali ne kan ɗinkin
tufafi a keɓance. Ta
la'akari da ma’anar gama-gari da aka bayar tare da yin la’akari da zamananci,
za a iya cewa ɗinki sana'a
ce ta amfani da hikima wajen sarrafa yadi zuwa abin suturta jiki ko ƙawa, tare da
taimakon keken ɗinki da
sauran kayan aiki.
A ɓangare guda kuwa, teloli sun kasu zuwa rukunoni da dama. Akwai manyan
abubuwa biyu da za a iya la’akari da su yayin tattauna rabe-raben teloli. Za a
iya la’akari da nau’ukan kayan aikin da teloli ke amfani da su domin bayyana
rabe-rabensu. Bayan haka, za a iya la’akari da muhallin gudanar da aiki.
2.1 Rabe-Raben
teloli ta la’akari da kayan aiki
Teloli na amfani
da kayayyakin aiki daban-daban yayin aiwatar da sana’arsu. Wannan ya kama tun
daga kan keken ɗinki
zuwa ƙananan
kayan aiki irin su almakashi da zare da sauransu. Duk da haka, babban abin
la’akari a wannan rukuni shi ne nau’ukan kekunan da maɗinkan sukan yi amfani da su. Yayin da aka yi
la’akari da nau’ukan kayan aiki, ana iya raba maɗinka zuwa rukunoni kamar haka:
A-
Telolin Taka-Taka: Waɗannan su ne waɗanda sukan yi amfani da keken ɗinki
wanda ake takawa da ƙafa. Wani lokaci akan yi
amfani da keken ɗinkin tare da taimakon wani ɗan injin idan akwai wutar lantarki ko
janareta mai ba da
hasken wutar lantarki. Akan samu maza da mata a cikin nau’in waɗannan teloli. An samu babban sauyi a wannan rukunin teloli bayan
samuwar wani nau’in keken ɗinki mai
suna indostura. Wannan
keke ba ya aiki sai da wutar lantarki.
B-
Telolin Barnina/Fonis: Waɗannan teloli ne masu aiki da wani keken ɗinki da ake kira fonis. Suna yi wa wuyan riga ko wani sashe na tufafi aiki. Suna yin aiki na mata da na maza. Wannan keken ba ya aiki sai da wutar
lantarki ko na janareta.
C-
Telolin Cunko:
Waɗannan telolin suna yin amfani da wani
keke wanda ya bambanta da fonis ta fuskar yanayin saƙar ɗinkinsu da kuma sifar keken. Keken cunko yana da wani sitiyari a ƙasa. Su ma suna aikin maza da mata.
D-
Telolin Sama:
Teloli ne masu kamance da na cunko amma zubin ɗinkin da suke yi ya bambanta da
nasu. Aikin sama yana da kamance da ɗinkin hannu. Shi ma akan yi na maza da na mata. Tamkar
dai keken cunko,
shi ma ba ya aiki sai da
wutar lantarki ko na janareta. Sannan yana da sitiyari ƙasa kamar na keken cunko.
2.2 Rabe-Raben
teloli ta la’akari da muhallin aiki
Muhalli ko wurin gudanar
da aiki wani abin la’akari ne yayin bayyana rabe-raben teloli. A ƙarƙashin wannan, za
a iya samun manyan rukunonin teloli guda uku kamar haka:
A-
Telolin Girke:
Su ne telolin da suke zaune wuri guda. Idan mutum ya sayi yadi zai tafi ya same su wurin da suke. Sukan
zauna a shago ko rumfa
idan kasuwa ce, ko kuma a cikin gidaje.
B-
Telolin Tafi-Da-Gidanka: Waɗannan teloli ne waɗanda ba su da tsayayyen wurin zama inda za a
same su domin ba su aiki. Sukan zagaya da keken ɗinkinsu a kafaɗa ko a saman abin hawa. Sau da dama
sukan kasance tafe suna shelanta "Ga tela ya zo!" Mafi akasarin ayyukansu sun keɓanta ga gyaran tufafin da suka yage
ko kuma ɗinkin kalo (tamfol). Mafiya yawan waɗannan telolin maza ne.
C-
Teloli 'Yan Ci-Rani: Su ne masu tashi daga garuruwansu zuwa wasu garuruwa ko ƙasashe domin neman ayyukan ɗinki. A irin wannan rukuni akan samu telolin
tafi-da-gidanka da kuma na girke.[6]
Ko bayan waɗannan rabe-rabe, akwai ta fuskokin da za iya kallon
kashe-kashen maɗinka.
Misali, ana iya dubawa ta fuskar jinsi. A nan za a samu (i) maɗinka maza da (ii) maɗinka mata. Ana kuma iya dubawa ta fuskar jinsin waɗanda ake yi wa ɗinki. A ƙarƙashin rukunin ana iya samun (i) maɗinkan mata da (ii) maɗinkan maza da kuma (iii) maɗinkan tarayya. Bayan haka, ana iya duba abin da maɗinkan ke samarwa domin bayar da rabe-rabensu. A nan
ne za a iya samun (i) maɗinkan haɗi da (ii) maɗinkan aiki.
1.3 Tarayyar
teloli
Duk da
kasancewar teloli sun rabu zuwa rukunoni daban-daban, akwai ta fuskokin da suka
yi tarayya. Daga ciki akwai:
i.
Kowane tela ya ɗauki ɗinki a
matsayin sana’a.
ii. Kowane tela yana yin ɗinki ne domin samun abin
masarufi, don kawar da
lalurorin yau da kullum da sukan bijiro.
iii. Duk suna mu'amula da yadi, don samar
wa al'umma tufafi ko ingantawa ko gyara ko ƙawata tufafin.
iv. Duk suna amfani da keken ɗinki don ɗinki ko gyara ko yin kwalliya ga yadi ko wani ƙyalle da aka kawo masu aiki.
v. Sukan rufa wa juna asiri idan buƙatar hakan ta
taso.
vi. Sukan yi aiki daidai da buƙatun mutane.
vii. Suna da Hausa
ta musamman (sakayayyiyar hanyar sadarwa a tsakaninsu).[7]
3.0 Hausar
teloli
A nan, Hausar teloli na nufin nau’in Hausa ta musamman da take bambanta da sananniyar Hausa ta fuskar kalmomi ko jimloli, wacce kuma ake samun ta a tsakanin teloli. Za a tattauna Hausar telolin garin Gusau ƙarƙashin muhimman rukunoni guda biyu wato (i) kalmomi da (ii) jimloli.
3.1 Kalmomin
Hausar teloli a garin Gusau
Jadawali na 1 da
ke ƙasa yana
ɗauke da jerin waɗansu kalmomin da telolin garin Gusau sukan yi amfani
da su.
Jad 1: Kalmomin
Hausar telolin Gusau da ma’anoninsu
Kalma |
Ma’anar Asali |
Sabuwar
Ma’ana |
Tsokaci |
Hassan/ Hassan Bala |
Sunan Mutum |
Mutumin da ya cika son banza (mai son kansa) dangane da abubuwa. |
Ana amfani da wannan furuci domin a yi wa wani tela hannunka mai sanda.
Da zarar tela ya fahimci cewa kwastoma Hassan Bala ne, to lallai ba zai
sakankance da shi ba. Zai yi ƙoƙarin tabbatar
da cewa haƙƙinsa ya fito. |
Raɓawo |
Zaurance ne (ɓarawo) |
Mutumin da ya cika son banza (mai son kansa) dangane da abubuwa. |
Ana amfani da wannan furuci domin a yi wa wani tela hannunka mai sanda.
Da zarar tela ya fahimci cewa kwastoma Hassan Bala ne, to lallai ba zai
sakankance da shi ba. Zai yi ƙoƙarin tabbatar
da cewa haƙƙinsa ya fito. |
Badakuwa |
- |
Yanayi ne inda
tela yake taya tela ɗan
uwansa domin su tsuga tsada ga kwastoma. |
Yayin da tela ya ambaci kalmar, tela ɗan uwansa zai fahimci cewa wancan
telan na buƙatar su haɗa baki
domin kwastoma ya amince da abin da za su faɗa masa, ko da kuwa ba gaskiya za su faɗa masa ba. |
Karatu |
Duba jerin baƙaƙe da wassula
tare da ayyana furucinsu a zuci ko furta su da baki |
A bai wa wanda ya kawo ɗinki haƙuri domin an yi masa rashin gaskiya. |
Tela na iya yi wa kwastoma karatu. Kuma yakan iya yin ishara ga ɗan uwansa tela da ke kusa domin ya
taya shi yin karatun. Misali, idan tela ya ambaci cewa: “Dole sai da karatu,”
to ɗan uwansa da
ke kusa na iya fahimtar cewa yana so ne ya taya shi ba da haƙuri ga
kwastoma. |
Sakin Layi |
1. Kaucewa
daga kan wata hanya/turba |
Yin shaidar zur game da rashin gama
wa wani ɗinkinsa. |
Tela na iya kare ɗan
uwansa ta hanyar yin shaidar zur. Misali, yana iya faɗa wa kwastoma cewa: “Ɗazun nan yake
magana cewa, yau zai kammala ɗinkinka.” |
Gauniyya/ Gauni |
Gawurta ko
tsanani |
Warin ƙashi |
An fi amfani da wannan lafazi yayin gulmar wani ko wata mai warin ƙashi da ya/ta
shigo shago. Tela na faɗa wa ɗan uwansa wannan kalma domin an karar
da shi cewa mai warin ƙashi ya shigo. |
Tushen
Bayani: Hira da teloli
3.2 Jimlolin
Hausar teloli a garin Gusau
A nan yana da
kyau a fahimci cewa, da dama daga cikin jimlolin Hausar teloli na da dangantaka
ta kai tsaye da kalmomin. A irin wannan yanayi, akan sanya kalmomin ne a cikin jimloli
yayin magana. A ɓangare
guda kuwa, akan samu jimloli kai tsaye a matsayin wani ɓangare na Hausar teloli. Dangane da kalmomin da aka kawo
a jadawali na 1 da ke sama, za a iya amfani da su cikin jimloli kamar haka:
Jad 2: Misalan yadda ake amfani
da kalmomin teloli cikin magana
Kalma |
Misalin Jumla |
Ma’ana |
Hassan/Hassan Bala |
Maza, Hassan Bala ya zo? |
Wannan ɓarawo
ne. |
Raɓawo |
Maza, ka ga raɓawo? |
Wannan ɓarawo
ne. |
Badakuwa |
Maza, akwai badakuwa. |
A taya ni tsuga tsada a wannan. |
Karatu |
Don Allah ku taya ni karatu. |
Don Allah ku taya ni bayar da haƙuri. |
Sakin layi |
Sakin layi fa kawai na yi. |
Ban tabbatar da gaskiyar lamarin ba, kawai na faɗa ne. |
Gauniyya/Gauni |
Yau mun samu gauniyya. |
Wani mutum ko wata mata ko waɗansu
mutane masu warin ƙashi sun shigo. |
Tushen
Bayani: Hira da teloli
A ɓangare guda kuwa, akwai jimloli kai tsaye da teloli sukan
yi amfani da su. Sukan bai wa waɗanan jimloli
ma’anoni na musamman wanda hakan ne ya mayar da su keɓantattu kuma na rukunin telolin. Yana da kyau a lura
cewa, misalai da aka kawo a jaddawali na biyu (Jad 2) da ke sama, kalmomi ne
aka yi misalin yadda ake amfani da su cikin jimloli. Hakan na nufin cewa, ana
iya amfani da su cikin waɗansu
sigogin jimloli na daban.
Jad 3: Jimlolin Hausar telolin Gusau da ma’anoninsu
Jumla |
Ma’anar Asali |
Sabuwar Ma’ana |
Nama ya tsiro masa a
ido. |
Tsokar nama ya yi tsiro a cikin idon mutum. |
Bacci ya ci ƙarfin tela har ya hana shi aiki. |
Ya tafi lazumi. |
Ya tafi yin addu’a. |
Ya tafi ya kwanta domin yin bacci. |
Ya yi fakare. |
Ya yi sakaƙe/kurum. |
Ya tara kayan mutane da yawa bai ɗinka ba, kuma ya gudu. |
Laho ne. |
Rago ne. |
Ba ya zuba mai a janareta sai wani ya zuba ya tayar da janaretan sai shi
kuma ya lalaɓo ya yi amfani da shi. |
3.3 Alamomi
Bayan furucin
baki, teloli sukan yi amfani da alamomi domin sadarwa. Amfani da alamomi
sananne ne kuma sababben al’amari. A wannan bagire, teloli sukan yi amfani da
ire-iren alamomin bisa manufofi mabambanta, ba kamar yadda aka san su a
maganganun yau da kullum ba. Waɗansu
daga cikinsu su ne:
A. Shafa
kai
A sadarwar yau
da kullum, shafa kai na nuni ga jin kunya. Ga telolin Gusau kuwa, idan tela ya
shafa kai to yana ishara ne ga ‘yan uwansa teloli cewar bai kammala aikin
kwastoman da ya zo ba. Hakan zai ba da damar ‘yan uwan aikin nasa su ƙirƙiri hanyar da za
su ɓullo wa
kwastoman domin ba shi uzuri.
B. Ƙulli/Ɗauri
Ɗaurewa ko ƙulle igiya ko
tsumma ko leda, da sauransu, ba ɓoyayyen
al’amari ba ne. Abu ne da ake gudanarwa yau da kullum. Sannan ba dole ne ya
kasance yana da wata ma’ana ta musamman ba. Ga teloli kuwa, akwai nau’ukan ƙulli da ake yi
wa kaya da ke ba da ma’ana ta
musamman. Misali, tela na iya yin salon ɗauri a kayan kwastoma domin nuna wa sauran abokan aikinsa cewa ko mai kayan
ya zo kada a ba shi su domin mai kayan bai biya kuɗin aiki ba.
3.4 Kalmomi
masu alaƙa da nau’in ɗinki
Wani ɓangare kuma na Hausar telolin garin Gusau shi ne
abin da ya shafi nau’ukan ɗinki.
Kowanne daga cikin rukunonin teloli da ake da su, suna da keɓantattun kalmomi da suka shafi nau’in aikinsu.
Wannan ya haɗa tun
daga kan kayan aiki zuwa yanayin gudanar da aikin, har abin da ya shafi
kayayyakin da ake samarwa. Za a kalli waɗannan kalmomi ƙarƙashin waɗansu rukunonin teloli da ake da su a garin Gusau.
3.4.1 Kalmomin
telolin taka-taka
An kawo taƙaitaccen bayani
game da telolin taka-taka a ƙarƙashin A da ke ƙasan 2.1 a sama.
Akwai kalmomi da suka fi keɓanta ga
waɗannan teloli. An
kawo waɗansu
daga ciki a ƙarƙashin
jadawali na 4 da ke ƙasa.
Jad 4: Kalmomin
telolin taka-taka:
Kalma |
Ma’anar Asali |
Sabuwar Ma’ana |
Keke |
Laulawa |
Keken Ɗinki |
Guru |
Abin da ake ɗinkawa
da fata a ɗaura a
damatsa domin kariya ko buwaya. |
Bel ɗin da
yake juya keken ɗinki,
ko kuma nau'un ɗinki. |
Raƙumi |
Nau’in dabba |
Wani dogon ƙarfe da ke tare da gyaren ƙasa. |
Takalme |
Takalmi |
Abin da yake danne ƙyalle yayin ɗinki. |
Buzuzu |
Wani nau’in ƙwaro |
Wani abu a fuskar keke wanda zare kan shiga cikinsa yayin ɗinki. |
Baka |
Ɗan ice
mai lanƙwasa da ake ɗaurawa
zare mai ƙarfi wanda cikinsa ake ɗana kibiya domin harbawa. |
Ƙarfen
keken ɗinki
ne da ke yin sama da ƙasa yana jan zare yayin ɗinki. |
Haƙori |
Sashe ne na cikin baki masu zubin fararen ƙasusuwa da ke
jere sama da ƙasa, waɗanda
da su ake taunar abinci. |
Wani ƙarfe mai kamar haƙori mai jan yadi idan ana ɗinki. |
Laka |
Ƙashin
gadon baya. |
Wani ƙarfe ne a ƙasan keke mai noti ko ƙusa. |
Ƙundu |
Ciki ko tumbi |
Wani ƙarfen keke ne zagayayye wanda a kan sa ƙoshiya a ciki. |
Giya |
Barasa – abin sha da ke saka maye |
Ƙarfen keke ne a gefen dama wanda ake ribas da shi. |
Hannu |
Ya shafi wani sashe na jikin mutum |
Ƙarfen keke ne a gefen dama wanda ake ribas da shi. |
Kwabo |
Nau’in kuɗi da
aka taɓa
amfani da shi a Nijeriya |
Wani ƙarfe ne mai ɗan faɗi na wajen haƙori. |
Fuska |
i. Duba fuskar mutum ko dabba. ii. Ɓangaren da ke gaba na wani abu kamar gida. |
Ƙarfen keke ne a gefen hagu, na ɗauke da buzuzu wanda ya rufe gaban
keken. |
Doki |
Nau’in dabba da ake hawa |
Bodin keken ɗinki, wato gun da ake ɗora kan keken |
Sanda/ Sanduna |
Busasshen dogon itace da yawanci ake ferewa a gyara |
Dogayen ƙarafunan da ke ɗauke da takalme ko allura. |
Tushen
bayani: Hira da teloli
Bayan waɗannan, akwai kuma kalmomi da ke da alaƙa da nau’ukan ɗinki da
telolin taka-taka ke yi. Sun haɗa da:
‘Yar-Shara: Nau'in riga ce wadda ba ta da hannuwa. Tun tuni Bahaushe na da wannan
nau’in riga. Duk da haka, akwai sauye-sauye na kwalliya da salo da ake yi wa
rigar a zamanance.
‘Yar-Bunguɗu: Nau’in riga ce
da hasashe ya nuna cewa ta samo asali ne daga fasahar telolin Bunguɗu.
Buba: Nau’in
rigar mata ce marar kwalliya da ke da zagayayyen wuya.
Ɗan-Itori:
Nau’in wando ne da ake yi wa ƙarin hantsa har ƙasa.
Adda: Waɗansu ƙyallaye ne da ake ƙara wa babbar
riga ko riga ‘yar-shara
a gaba da baya.
Sace: Babbar
riga ce mai kama da ‘yar shara wadda ake yi wa ƙari.
Tsefewa:
Warware ɗinki
(misali, warware wani ɗinki da
aka yi domin gyarawa)
3.4.2 Kalmomin
telolin barnina (fonis)
Telolin Barnina
wato Fonis na da sunaye na musamman da suka shafi nau’ukan ɗinkunan da suke samarwa da matakan gudanar da ɗinkunan. Sun haɗa da:
Jad 5: Kalmomin
telolin barnina (fonis) da ma’anoninsu:
Kalmomi |
Ma’anonin da maɗinka
suka ba su |
Kika |
Nau'in ɗinki ne mai kama da haƙori. |
Kwashe |
Ɗinki ne mai ɗan tsawo da faɗi. |
‘Ya’ya |
Ɗigagga ne da ake yi domin gyaran ɗinki. |
Sharaba |
Wata tufkar zare ce
wadda ake sa wa aiki. |
Singa |
Ɗinki ne mai kama da na taka-taka. |
Zubi |
Wannan na nufin fitar
da sigar aikin da za a yi. |
Ɗauri |
Yin ɗinkin sama na kwashe |
Ciko |
Yin kwalliyar aiki
bayan zubi |
Fulawa |
Fitar da kwalliya
masu kama da fulawa a
jikin ɗinki |
Zaga-Zaga |
Nau’in ɗinki kwashe ne da ake yin
sa wara-wara |
Madogara:
Hira da teloli
3.4.3 Kalmomin telolin cunko da aikin sama
Telolin Cunko da
na Aikin Sama na da kalmomi na musamman da suke amfani da su. Waɗannan kalmomi sun shafi yanayin aikinsu da kayan
aikinsu da kuma nau’ukan kayayyaki da suke ɗinkawa. Za a iya lura da cewa, kai tsaye kalmomin na
da ma’anoni na musamman, saɓanin waɗanda aka san su da su a magana ta yau da kullum. Daga
cikin kalmomin akwai:
Harshe: Ƙarfe ne a
fuskar keke wanda shi yake motsa keken.
Sitiyari: Wani ɗan ƙarfe ne mai ƙululu a ƙasan keke. Da shi ake sarrafa keke lokacin aiki.
Satila: Ɗan ƙarfe ne wanda
shi ke rarrabewa tsakanin zaren ƙasa da na sama.
Dawakai: Ƙarafa ne gaba da
baya waɗanda sukan
sarrafa keken ɗinki
gaba ɗaya.
Baka: Telar
(keken) sama ne kawai
ke da shi. Ƙarfen keke ne da ke jan
zare.
Guiwa: Sunan ƙarfe ne wanda ke sarrafa dawakai.
Buzuzu: Abu ne da ke sarrafa saƙar keke.
Kunne: Wani ƙarfe ne wanda ke saman fuskar telar (keken)
sama.
Korkoro: Wani ƙarfe ne mai kwararo wanda ake zura
zare a cikinsa.
Ƙundu: Ƙarfen keke ne
wanda yake ƙarƙashin keken
ɗinki inda ake sarrafa zaren ɗinki.
Aska: Sunan
ɗinki ne da ake yi wa babbar riga.
Wundi: Aiki ne da akan yi wa wata riga mai
zagayayyen wuya
Kaftani: Aiki ne da ake yi wa wuyan rigar maza.
Zabuni: Sunan kaya guntaye (marasa tsayi) waɗanda mafi akasari jinin sarauta kan
sa. Akan yi musu cunko
ko aikon sama.
Timbuktu: Sunan wani nau’in aikin cunko ne.
Buba: Aikin
cunko ne na mata.
4.0 Sakamakon
bincike
Wannan bincike ya gano cewa, telolin suna da wata
hanyar sadarwa a
tsakanin junansu, wadda idan mutum bai san wannan sirrin magana ba, to ba zai iya fahimtar saƙon da ake isarwa ba. Duk da haka, salailai da
sigogin da ake furta maganganun sun bambanta daga shago zuwa wani shago. Haka
kuma, akan samu bambancin ma’anar kalmomi tsakanin nau’ukan teloli daban-daban
da ake da su. Hakan kuma na faruwa ne musamman sakamakon bambancin kayan aiki
da yadda ake gudanar da aikin.
Waɗansu daga cikin kalmomi da jimlolin da ake samu
cikin Hausar teloli sun kasance akwai su a Hausar yau da kullum. Bayan an ɗauke su, sai aka ba su waɗansu ma’anoni na daban. Misalansu sun haɗa da “ƙundu” da “kunne” da “buzuzu” da
sauransu. Wannan kuwa ya yi daidai da iƙirarin hanyar da aka ɗora aikin ta “kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.”
Kuma hakan ya bayyana cewa, teloli sun samar da kuka na musamman a gidansu,
wato sana’ar ɗinki. Bayan
su kuwa akwai waɗanda ƙirƙira ce kai
tsaye, wato ba a san kalmar ba a Hausar gama-gari. Daga cikin misalansu akwai “sharaba” da “dinga.”
Lura da waɗannan bayanai, ana iya taƙaita cewa:
a.
Hausar teloli na iya bambanta da
sananniyar Hausa ta fuskar kalmomi ko jimloli.
b.
Kalmomin da ake samu cikin Hausar teloli
na iya kasancewa ƙirƙirarru,
ko kuma waɗanda ake
da su a Hausar asali amma sai aka ba su waɗansu ma’anoni na daban.
c.
Ana amfani da Hausar teloli wajen
fayyace sunayen abubuwa ko bayanin waɗansu al’amura da ke faruwa ko kuma domin sakaya zance.
A bagiren
al’ada, Hausar teloli na iya kasancewa wata hanya ta gulma da zunɗe da ƙulla munafurci da yaudara. Tana iya zama hanyar ƙulla damfara da
zamba ga abokin kasuwanci ko da kuwa a gaban idonsa ne. Duk waɗannan kuwa halaye da ɗabi’u ne da suka ci karo da koyarwar al’adun Hausawa
nagartattu.
5.0 Kammalawa
Sana'ar ɗinki sana'a ce mai daɗaɗɗen
tarihi a ƙasar Hausa, wadda takan samar da tufafi da danginsu ga al'ummar Hausawa. Ta tattara abubuwan nazari a fannin
ilimi, musamman idan muka yi la'akari da fannonin nazarin harshen da al'ada. Nazarin Hausar
kalmomi na iya taimaka wa fagen nazarin harshen Hausa da sababbin kalmomi tare
da bunƙasa
farfajiyar nazarin walwalar harshe, musamman abin da ya shafi Hausar rukuni ta
sana’a. Ta fuskar al’ada binciken zai kasance hannunka mai sanda game da gyaran
halaye da ɗabi’un
da suka shafi damfara da zamba da ƙarya da gulma da munfaruci da sauran munanan ɗabi’u da halaye makamantan waɗannan. Bayan haka, ankararwa ne ga sauran al’umma
domin fahimtar wainar da ake toyawa.
Manazarta
1.
Alhassan H. da wasu, (1984). Zaman Hausawa, na biyu. Nothern Nigeria Publishing Company.
2.
Bashir, A. (2012). The Morphosyntax of
Diminutive in Hausa. [Kundin
digiri na ɗaya da ba a wallafa ba]. Jami’ar
Bayero, Kano, Nijeriya.
3.
Bashir, A.
& Sambo, M.W. (2021). “Suffixation and Reduplication
in Zamfara Dialect of Hausa Language”. Interdisplinary Approach to the Study
of African Languages. Festschrift
in Honour of Francis Egbokhare. ISSN: 978 –
978 – 966 – 297 – 5. Pp236-243.
4.
Bunza A.M. (2004). Waƙƙƙen ƙa'idojin rubutun Hausa. Ibrash Islamic
Publication Center Ltd.
5.
Bunza, A. M. (2019). Ƙwarya a
farfajiyar adabi da al’adun
Bahaushe. East African Scholars Journal of Education, Humanities and
Literature, 2(12), 720-727.
6.
Bunza, A.M. (2017). Dabarun
bincike a nazarin harshe da adabi da al'adun Hausawa. Ahmadu
Bello University Press Limited.
7.
Garba, C.Y. (1991). Sana'o'in
gargajiya a ƙasar Hausa. Baraka Press and Publishers Limited.
8.
Muhammad, A. (2021). Sana'a sa'a: Yankan farce a
garin Gusau.
[Kundin digiri na farko da ba a wallafa ba]. Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara,
Nijeriya.
9.
Muhammad, M.S. (2020). Bahaushiyar al’ada. Bayero
University Press.
10.
Sani,
A-U. (2022). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin
digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato,
Nijeriya. www.doi.org/10.13140/RG.2.2.24862.61764.
11.
Sani, A-U., Buba, U. &
Mohammad, I. (2019). Wanda ya tuna bara...: Biɗa da Tanadi a tsakanin Hausawa matasa a yau. Global Academic Journal of
Humanities and Social Sciences, (1)2, pp. 44-50. https://www.gajrc.com/media/articles/GAJHSS_12_44-50_aLnXk46.pdf.
12.
Yahaya, S. U. (2021). Damben Hausawa a
zamanance [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato, Nijeriya.
[1]
Sani, Buba, & Mohammad, (2019 p.
44) sun bayyana cewa “Hasali ma, Hausawa sun shahara ta fuskar noma da
kasuwanci da fatauci da sauran sana’o’i daban-daban. Ficen da Hausawan suka yi
a ɓangaren sana’o’in
fatauci da kasuwanci ya taimaka matuƙa wajen bazuwarsu zuwa wurare daban-daban.
Hausawa sun kafu a ire-iren waɗannan wurare tare da cigaba da gudanar da
sana’o’insu.
[2]
A can da, sana'ar ɗinki sai
ɗan gado. A yanzu kuwa, ana koyo a cibiyoyin koyar da sana'o'i da shagunan ɗinki
daban-daban. Wannan dama ce ga kowa. Hakan ne kuma ya sa ake samun ƙaruwar gasa a cikin sana’ar.
[3]
Akwai ayyuka daban-daban da aka ɗora
su a kan Bahaushiyar hanyar gudanar da bincike. Daga cikinsu akwai Bunza,
(2019) da Sani, Buba, &
Mohammad, (2019) da Yahaya, (2020) da Sani, (2022).
[4]
Akwai shagunan teloli a dukkannin waɗannan
yankuna da aka ambata. A cikinsu, wurare biyu da suka yi fice a matsayin cibiya
ko matattarar maɗinka su ne Bakin Kasuwa Gusau da Sabongari.
[5]
Kalmar sana’a ba sabuwa ba ce ga
Bahaushe. Tana nufin hanyar amfani da fasaha da hikima da kuma kayan aiki domin
sarrafa wani abin amfani da za a iya sayarwa ko a musanya da wani abu mai
daraja. Domin samun ƙarin bayani game da sana’a da kasuwanci, ana iya duba Muhammad,
(2020).
[6] Mafi akasarin telolin Gusau ‘yan
ci-rani sun fi tafiya kudancin Nijeriya da kuma wajen ƙasa, kamar Libiya da
Nijer da Togo da sauransu.
[7]
Sana’ar ɗinki
na da matuƙar amfani a ƙasar Hausa. Daga cikin amfaninsa akwai (i) samar da tufafi
da danginsu ga al'umma da (i) samar da rufin asiri ga masu sana’ar da (iii) hana
zaman banza tsakanin al'umma da (iv) samar da kuɗin shiga ga hukuma da (v) kyautata
mu'amula tsakanin al'umma, da sauransu.