author/Sani, A-U.; Hamma, A.; Aliyu, I. & Abubakar, K.A.
journal/Scholars International Journal of Linguistics and Literature
pdf-https://drive.google.com/file/d/1iBnuYfuKRxW5tPCeH6j18V2rITuuo7tN/view?usp=sharing
paper-https://drive.google.com/file/d/1iBnuYfuKRxW5tPCeH6j18V2rITuuo7tN/view?usp=sharing
Citation: Sani, A-U.; Hamma, A.; Aliyu, I. & Aliyu, K. A. (2022). Mawaƙa A Idon Hausawa: Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa Ta Fati Da Kasim. Sch Int J Linguist Lit, 5(7): 209-216. DOI: www.doi.org/:10.36348/sijll.2022.v05i07.002.
Mawaƙa A Idon Hausawa: Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa Ta Fati Da Kasim
Abu-Ubaida SANI1
Aliyu Hamma2
Ibrahim Aliyu3
Kachalla Aliyu
Abubakar4
1Department of
Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Nigeria
2, 3, & 4 Department of Hausa Studies, College of Education,
Waka-Biu, Borno State, Nigeria
Tsakure
Hausawa na
ɗaya daga cikin al’ummu da Allah ya azurta da ɗimbin
mawaƙa. Tun inda aka fito, Bahaushe na amfani da
waƙa a kusan dukkan ɓangarori
ko al’amuran rayuwarsa. Wannan ya haɗa da sana’o’i (noma da saƙa da dukanci da farauta da sarkanci da ƙira da makamantansu), da kuma zamantakewa da
bukukuwa da gyaran muhalli da ma sauran sha’anonin da rayuwar Bahaushe ke ƙunshe da su. Sai dai kamar yadda akan ce;
“Idan kiɗa ya canza, rawa ma sai ta canza,” haka ma
siga da salon waƙoƙin Hausa na canzawa tare da canjin zamani. A
yau zamani ya kai, an samu mawaƙa da dama da ke
amfani da kayan kiɗa na zamani yayin rera waƙoƙinsu. Sai
dai wani abu shi ne, mawaƙan ƙasar Hausa na fuskantar tsangwama. Sau da
dama matsayinsu ga idon jama’a ba ya wuce maroƙa ko
limamen shashanci. Wannan ne ya sanya mawaƙa da dama
ke rera waƙoƙi da ke
nuna ƙorafinsu ga hakan. Wannan takarda ta nazarci ɗaya
da cikin waɗannan waƙoƙi mai suna Waƙar Ranar Mawaƙa
wanda Fati da Kasim suka rera. Sakamakon nazarin na nuna cewa; mawaƙa na fuskantar tsangwama a ƙasar Hausa. Sannan al’umma ba ta tallafa wa
waɗannan mawaƙa ta
fuskar shawarwari da sauran abubuwa da suka dace. Daga ƙarshe an ba da shawarwari da suka haɗa
da, a riƙa jawo mawaƙa jiki
tare da ƙarfafa musu guiwa da nusar da su kan samar da
waƙoƙi masu
amfani ga al’umma ta fuskar ilimi da zamantakewa.
Fitilun
Kalmomi: Waƙa; Mawaƙa;
Ƙorafi; Tsangwama
1.0 Gabatarwa
Kamar
dai yadda waƙa
ta kasance hanyar isar da saƙwanni
da kuma bayyana muradin zuci, mawaƙa
kan yi amfani da waƙa
domin ƙorafi
game da wani abu da ke ci musu tuwo a ƙwarya.
Ɗaya
daga cikin ƙorafe-ƙorafen
da mawaƙa
suka fi yi, shi ne tsegumi da kallon banza da aka faye yi musu; wani lokaci har
da musgunawa daga hukuma. Sukan nuna rashin jin daɗin
hakan cikin hikima da fasaha a waƙoƙi daban-daan da suke rerawa.
A
ɗaya ɓangaren
kuma, a shekarun baya-bayan nan ne (wajajen 2013) mawaƙan Hausa suka ƙirƙiri wata ƙungiya mai suna Ranar Mawaƙan Hausa Foundation (RMHF), ƙarƙashin jagorancin Aminu Ladan
Abubakar (ALAn Waƙa).
Ƙarƙashin wannan ƙungiya, akan gudanar da
taron mawaƙa
a ƙarshen
kowace shekara. Akan ɗauki
kwanaki ana gudanar da taron. Wato
dai, har sai an shiga sabuwar shekara. Taron na samun halartar mawaƙa daban-daban, da masana waƙa (malamai) har ma da
shuwagabanni da sarakunan gargajiya. A bisa wannan ne, Fati da Kasim suka
shirya waƙar
da ke nuna koke ko ƙorafi
game da mawaƙa
a idon Bahaushe a yau. Sun yi amfani da wannan taron mawaƙa da ake gudanarwa, inda
suka kira shi Ranar Ɗaya Ga Watan Ɗaya.
Za ta yiwu sun yi hakan ne kasancewar, wannan taro na samun halartar mafi yawan
fitattun mawaƙa
daga kowane ɓangare na ƙasar Hausa.
2.0 Waƙa A Ƙasar Hausa
Waƙa ba sabuwar aba ba ce da
ake da buƙatar
dogon bayani game da ma’anarta. Masana da manazarta da dama sun bayyana ma’anar
waƙa a
rubuce-rubuce da suka gabatar a matakan ilimi daban-daban. Masana da marubuta da
suka yi tsokaci kan ma’anar waƙa
sun haɗa da: Gusau, (1993)
da Ƙaura,
(1994) da Yahya, (1996) da Bunza, (1988) da Habibu, (2001) da Zurmi, (2006) da Maikwari, (2020) da
makamantansu.
Waƙa wani furuci ne (lafazi ko saƙo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaitattun kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi. (Ɗangambo, a cikin Habibu, 2001).
Shi
kuma Alƙali
Haliru Wurno a waƙe
ne ya bayyana nasa ra’ayi kan ma’anar waƙa kamar yadda Abdullahi,
(2017) ya rawaito cewa:
Waƙa
ɗumi ne
hira ko labari,
Zargi yabo zagi da
kiznin sharri,
Koko kwaɗai ga
mutum ya ba ka ka amsa.
Labar ɗumi na
wanda kay yi ga tsari,
Wani dunƙulalle
kay yi jeri-jeri,
A cikin nashaɗi ko ganin
ka ƙosa.
Waƙe
bayani na kaɗanna da
tari,
Wani bi ka sa gishiri
ka yo mishi ƙari,
Haɗari na waƙe
mai faɗin damassa.
Waƙa
da waƙe Hausa sun ɗauke su,
Sunansu waƙa
ko’ina an san su,
Ka biɗo bayani
babu sai dai kansa.
Waƙa
fasaha ne da yac cuɗe ka,
Kuma ba karatuna ba
in an ba ka,
Ilimi dubu sai ka biɗo wani
nasa.
A cikin ɗumi waƙe
kamar rana ne,
Kuko ya zam hadarin
ruwan bazara ne,
Shi taho da sanyinai
na ma’aunin nesa.
(Alkali Haliru Wurno ma’anar waƙa)
Sai
dai waƙa
a ƙasar
Hausa ba nau’i ɗaya
ba ce kawai. Ɗangambo,
(2007) ya ƙarfafa
cewa: “Ya kamata mu tuna cewa akwai waƙoƙi iri biyu: rubutacciyar waƙa da waƙar baka, wato waƙar makaɗa.”
Gusau, (2003) cewa ya yi: “Waƙar
baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa
bisa ƙa’idojin
tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amo kari da kiɗa
da amshi.”
Abu
ne mai wuya a iya ƙayyade
asalin lokacin da Bahaushe ya fara waƙa.
Wannan kuwa na faruwa ne dalilin kasancewar a farkon rayuwar Bahaushe ba shi da
ilimin karatu da rubutu. Ya samu wannan ilimi ne bayan cuɗanyarsa
da al’ummar Larabawa da kuma karɓar
addinin Musulunci da ya yi. Bayan ya koyi karatu da rubutu ta hanyar amfani da
baƙaƙen Larabci domin rubuta
Hausa (ajami), sai kuma ya fara rubuta waƙoƙi. Wannan na nuna cewa, tun
kafin zuwan Musulunci da kuma hanyar rubutu Bahaushe na rera waƙoƙi da baka. Game da zuwan Musulunci
ƙasar
Hausa kuwa, an samu bambancin ra’ayi tsakanin masana da marubuta. Habibu, (2001) ya nuna cewa waɗansu na ganin cewa addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun ƙarni na goma sha biyu. Wasu
ma sun ce tun ƙarni
na bakwai. Birnin-Tudu,
(2002) ya bayyana cewa tabbacin Musulunci
ya shigo ƙasar
Hausa tun zamanin sarkin Kano Ali Yaji. Wato shekarar 1349 zuwa 1385.
Wani
babban lamari ya ɓullo
duniyar waƙa
yayin da Bahaushe ya samu ilimi da damar fara amfani da kayan kiɗa
na zamani domin rera waƙoƙinsa. Amfani da fiyano da
sutudiyo ya canji kalangu da ganga da dundufa da makamantansu na dangin kayan
kiɗan gargajiya da Bahaushe ya
saba amfani da su. Wannan sabon lamari ya samar da muhawara tsakanin masana waƙoƙin Hausa. Wasu dai suna da
ra’ayin cewa, duk waƙar
da aka sa mata kiɗa,
to ta tashi daga rubutacciya. Saboda haka za a kira ta ne waƙar baka kai tsaye. Wasu kuma
suna kallon cewa, sabon salo da waƙoƙin suka zo da shi, sun fi ƙarfin a kira su waƙar baka kawai. Idan aka yi
haka, haƙiƙa ba a yi wa waƙar baka ta asali adalci ba.
Domin ita ba sai an rubuta ba ake rerawa. Ma’ana ana rattabo ta ne kawai kai
tsaye.
Wani
bambanci da ke tsakanin waƙoƙin da ake samarwa a sutudiyo
da na baka shi ne, a waƙoƙin baka ba a samun amsa-amo da daidaiton baituka
kamar yadda yake samu a waƙoƙin zamani na sutudiyo. A
wannan ɓangare (ƙafiya da daidaiton baituka)
waƙoƙin zamanin sun fi kama da
rubutattun waƙoƙi. A taƙaice dai, waƙoƙin sai suka kasance tamkar
jemage; ba su ga tsuntsu ba su ga dabba. Wato dai siffofinsu ba su tsaya ga waƙoƙin baka ko rubutattu ba kaɗai.
Za ta iya yuwawa, wannan ne dalilin da ya sa kafar intanet na Hausa mai suna
amsoshi (www.amsoshi.com) ya kira irin waɗannan
waƙoƙi da Waƙoƙin
Zamani. Domin kuwa, duk inda aka zaga aka zago,
dole ne a yarda waƙoƙin sun samu ne a zamanance.
Sannan zamani yana tasiri ga waƙoƙin da su kansu mawaƙan.
3.0 Amfanin Waƙa
Haƙiƙa waƙoƙi suna taka muhimmiyar rawa
wurin faɗakarwa tare da
wa’azantarwa ga al’umma bayan ɗumbin
nishaɗantarwa da akan samu
daga gare su. A fahimtar Zurmi, (2006), ba za a taɓa
mantawa da gudummuwar rubutattun waƙoƙi ba a lokacin jihadin
jaddada addinin Musulunci ƙarƙashin jagoranci Shehu Usmanu
Ɗanfodiyo.
A zamanin yau kuwa, ɓangarorin
rayuwa da dama sukan rasa armashi idan babu waƙa. Bello, (2017) ya zayyano
wasu daga cikin fannonin rayuwa da waƙa
ke taka rawar gani gare su. Sun haɗa
da: siyasa, da ilimi da tarihi da makamantansu. A taƙaice, amfanin waƙa sun haɗa
da:
i.
Waƙa babbar hanya ce ta jawo
ra’ayin al’umma a lokutan siyasa domin zaɓen
wani ɗan takara. Mawaƙa na da babban gurbi wurin
tallata ‘yan takara ta hanyar kurara su da fito da ayyukansu na alkairi fili
tare da kushe abokan takararsu.
ii.
Waƙa babbar hanya ce ta tallata
haja ga ‘yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban. Masu shaguna da kamfanoni da
ma sauran
nau’ukan kasuwanci iri-iri kan nemi mawaƙa su tallata hajarsu.
iii.
Waƙa hanya ce ta ilimantarewa
da faɗakarwa. Jama’a sukan
samu ilmummuka daban-daban tare da wayewar kai daga waƙoƙin da suke saurara. Wannan
ya haɗa da bayanai game da
cututtuka, da yanayin siyasar ƙasa, da tarihi da makamantansu.
iv.
Waƙa hanya ce ta samun abin
masarufi da dogaro da kai ga mawaƙa
da dama.
v.
Waƙa na samar da nishaɗi
da annashuwa.
vi.
Kafa ce ta adana tarihi da
al’adu. Akwai waƙoƙi da suke ɗauke
da tarihin muhimman mutane cikin al’umma ko wasu muhimman lamura da suka faru.
Ire-iren waɗannan
waƙoƙi za su kasance tamkar taska
na adana waɗanan muhimman tarihai
har zuwa lokaci mai tsawo nan gaba.
vii.
Waƙa na tallafa wa waɗansu
ɓangarorin adabin Bahaushe na
baka da rubutattu. Misali, tazuniya a
gargajiyance da finafinai a zamanance duk sukan yi armashi ta dalilin waƙoƙi da ake sanyawa ciki.
viii.
Waƙa hanya ce ta tallatawa tare
da yaɗa harshe zuwa ga wasu
al’ummu da duniya baki ɗaya.
ix.
Waƙa ta kasance babbar hanya da
al’umma za su iya bayyana kukansu ga gwamnati ko wata majiya a matsayin ƙungiya ko ɗaiɗaikun
jama’a.
4.0 Mawaƙa A Idon Al’umma
Duk
da ɗunbin amfanin waƙa, mawaƙa na fuskantar matsin lamba
tare da tsangwama ta fuskoki daban-daban. A mafi yawan lokuta akan ɗauki
mawaƙa
a matsayin watsattsun mutane waɗanda
ba sa riƙo
da addini. Wani lokaci akan ɗauke
su a matsayin mabarata kawai sannan marasa mutuncin kai ko wata ƙima ta a-zo-a-gani. Wannan
nazari ya yi hasashen wasu dalilai da za su iya kasancewa sanadiyar wannan
kallon hadarin kaji da ake yi wa mawaƙa.
Dalilan sun haɗa
da:
i.
Kasancewar wasu ɓata
gari a cikin mawaƙa
da ke ayyukan da suka ci karo da al’ada da kuma addinin Hausawa. Wannan ya haɗa
da shigar da ta saɓa wa
al’ada yayin gudanar da waƙoƙi da tarukan mawaƙa, da kuma waƙoƙin batsa da makamantansu.
ii.
Mawaƙa da suka mayar da waƙa hanyar maula: Wannan ma
zai iya kasancewar dalilin faɗuwar
daraja da ƙimar
mawaƙa
a idon al’umma. Hakan na faruwa ne kasancewar addini da al’adar Bahaushe bai
aminta da lalaci da mutuwar zuciya
ba.
iii.
Siffa da salon Turawa: Waƙoƙin sutudiyo dai sun samu ne
a zamanance, bayan cuɗanyar
Hausawa da baƙin
al’ummu musamman Turawa. Ƙyamar
da Bahaushe ke yi wa al’adun Turawa zai iya kasancewa dalilin da ya sa ya ƙyamaci waƙoƙin zamani. Wato dai an ci
biri har an sha romonsa.
iv.
Shagala: Addinin Bahaushe
bai yarda da shagala ba. Wannan zai iya zama dalilin tsangwama ga mawaƙa. Musamman yayin da aka ɗauki
waƙa a
matsayin hanyar shagala ga al’umma.
Haƙiƙa ire-iren waɗannan
dalilai na da nasaba ga irin kallon da ake yi wa mawaƙa a ƙasar Hausa a yau. Irin
wannan tsangwama ta sanya mawaƙa
da dama sun yi raddi ko martani a cikin waƙoƙinsu. A cikin ire-iren waɗannan
waƙoƙi na raddi sukan nuna baƙin ciki da takaicin salon kallon banza da tsangwama
da ake musu. A wasu lokutan har sukan yi baƙar addu’a ga mutanen da ke
neman ɓatanci gare su. A waƙar Ala da abokan ɗaninsa
ta Hasbunallahu, za a iya kallon inda
mawaƙan
suka nemi tsari daga masu yin ɓatanci
ga san’arsu ta waƙa
kamar haka:
Ya mai tsare halitta mun zo ka taimake mu,
Ka ba mu kariya kar wani ɗa ya
addabe mu,
Allahu kai katanga ta tsari ga magautanmu,
Masu bibiyar ɓatanci ga
sana’unmu,
Mun zamma sai ka ce jemagu da iyalanmu,
Mun zamma mujiya a cikin jinsin yarenmu,
Suna ta cin amanar bayinka cikin hammu,
Sun shigga innuwar al’adu addininmu,
Allahu don isarka da mu kai kaƙ
ƙage mu,
Ka ba mu kariya don ƙaunar Abu
Batulu.
Haƙiƙa a baitukan da ke sama,
mawaƙan
sun nana cewa, masu neman ɓatanci
ga sana’arsu ta waƙa
suna jingina abin ne ga al’ada da kuma addini. Wato dai suna nuna cewa, waƙa ta ci karo da addini da
kuma al’adar Bahaushe. A cikin wannan waƙar kuma, sun yi baƙar addu’a ga ire-iren waɗannan
mutane (masu neman ɓatanci
ga waƙa
da mawaƙa),
inda suke cewa:
Muna da maƙƙiya wanda
ka yarda mun ka gan su,
Akwai na ɓoye wanda
kawai Rabbi kai ka san su,
Rugurguje shirinsu ka mai da
shi bissa kansu,
Da sun kira ka Allah don miƙa
buƙatunsu,
Ka juyar da buƙatunsu ya
Zuljalalu.
Cutar Gloria har cholera gami da tension,
Cutar hawan jini har Typhoid in addition,
Cuta ta kuturta da makanta a conclusion,
Cuta ta ƙanjamau
mai hana ɗan Adam
emotion,
Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.
Cuta ta Asthma da Koshorko ka sa gare su,
Cutar Pneumonia da ƙarzuwa
cikin jikinsu,
Ciwo na karkare da kurkunu ka sa gare su,
Cutar Malaria Fever sa ka kassara su.
Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.
Cuta ta Anthrax Allah sa a
jikkunansu,
Cuta ta Glaucoma a sa a maganansu,
Cuta ta Trachoma maƙala wa
ijjiyarsu,
Ka mai da su kurame ka ɗoɗe
maganansu,
Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.
5.0 Game Da Waƙar Ranar Mawaƙa
Waƙar Ranar Mawaƙa
waƙa ce
da aka yi ta bisa salon ɗani.
Salon ɗani dai yanayi ne da
wani mawaƙi
ke yin ɗani (wato tayawa ko
tsokaci ko tsoma baki) a cikin waƙar
wani mawaƙi
daban. Wannan takarda ba ta mayar da hankali kan wani abu daban ba, face wadda
waƙar
ta zo da ita. Kenan dai, komai dangane da waƙar ko mawaƙan zai fito ne daga bakin su
mawaƙan.
Takardar ta fahimci cewa, mawaƙa
biyu ne suka yi waƙar. Asalin mai waƙar sunanta Fati kamar yadda
aka ambata a cikin ɗiyan
farko a baiti na bakwai (7) na waƙar.
Misali:
Fati
waƙa fa
kwalba ce …
Sai
kuma wanda ya yi ɗani
a waƙar
da ke da suna Kamis, kamar yadda ya zo a ɗan
fari da ke baiti na huɗu
cikin waƙar.
Misali:
Amma Kamis fa duk da haka …
Waƙar tana da baituka goma sha
shida (16). Dukkansu sun kasance masu ƙwar
huɗu in ban da baiti na sha
shida da ya kasance mai ɗiya
goma sha huɗu (14). Baitukan na
da ƙananan
amsa amo mai canzawa daga baiti zuwa baiti. Sannan waƙar tana da babban amsa amo
na: ‘ma’ wanda ke zuwa ƙarshen
kowane baiti.
A
farkon waƙar
an kawo shimfiɗa cikin salon
siffantawa game da ranar mawaƙa,
kamar haka:
Ranar ɗaya ga
watan ɗaya,
Ga mu bai ɗaya,
A wuri ɗaya,
Shigarmu ɗaya,
Manufarmu ɗaya,
A ƙasarmu
ɗaya Najeriya.
Sannan
waƙar
tana ɗauke da amshi mai ɗiya
biyu. Shi ma wannan amshi yana bayani ne game da ranar mawaƙa. Wato ranar ɗaya
ga watan ɗaya. Amshin ya
kasance kamar haka:
Ranar ɗaya ga
watan ɗaya ita ce
ranar mawaƙa,
Ranar baje kolin fikira da nishaɗantar
da al’umma.
An
buɗe waƙar da addu’a tare da salati
ga manzo a baiti na ɗaya
da kuma na biyu:
Ya Rabbi Ubangijin
kowa,
Daga mai rai har zuwa
gawa,
Rabbana ka tsare mu
gantsarwa,
Mui waƙar
babu ɓamɓarma,
Rabbana tsira
amincinka,
Ka daɗa wa Makiyu
zaɓinka,
Ka cika shi kakaf da
yardarka,
Don ya tsamo ‘yan cikin ɓurma.
Baya
ga haka, mawaƙan
sun yi amfani da salailai daban-daban domin isar da saƙon waƙar. Waɗannan
salailai sun haɗa da
salon kamance da na abuntawa da sauransu. Sarɓi,
(2007) ya bayyana ma’anar salo da cewa: “A fagen nazarin waƙa salo hanya ce da marubuta
waƙoƙi ke bi wajen isar da saƙonsu ga jama’a.
6.0 Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa
Turken
waƙar
ranar mawaƙa
ita ce ƙorafi.
Turke da jigo kalmomi ne masu ma’ana ɗaya
wanda ake amfani da su wurare daban-daban. Wato kamar dai yadda ake amfani da
jigo a rubutattun waƙoƙi, haka ake amfani da turke
a waƙoƙin baka. Abdullahi, (2017)
ya rawaito ma’anar turke daga Ɗangambo
(2007): “Jigo shi ne saƙo,
manufa, ko abin da waƙa
ta ƙunsa
wato abin da take magana a kai.” Wannan ya yi daidai da ma’anar da Yahya (1997)
ya bayar cewa: “Jigo na nufin saƙo
ko manufa ko bayani ko ruhin da waƙa
ta kunsa wanda kuma shi ne abin da waƙa
ke son isarwa ga mai sauran ko karatu ko nazarinta.” ‘Yar’aduwa (2010: 149) ya ce: “Jigo kalma ce
da masana adabin Hausa suka amince su riƙa yin amfani da ita wajen
ambaton saƙon
da zube ko wasan kwaikwayo ko waƙe
suke ɗauke da shi.”
Kamar
yadda aka bayyana a sama, jigo da turke na nufin manufar waƙa. Gusau, (1993: 28) ya
bayyana ma’anar turke da cewa: “Turke shi ne abin da waƙa take magana a kansa wanda
ya ratsa ta tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta.” Baituka da dama
cikin waƙar
Ranar Mawaƙa na ɗauke
da ƙorafi
game da irin kallon hadarin kaji da al’umma ke yi wa mawaƙa. Bayan baituka biyu na buɗewa,
mawaƙiyar
ta nuna matsayinsu da amfanin ranar mawaƙa inda take cewa:
Yau ce ranar mawaƙa,
Rana ta ruwan hazaƙa,
Bishiyar fikira muke
tsinka,
Muke shayar da
al’umma.
Ta
yi amfani da salon abuntawar abuntawa, inda ta ta kwatanta baitukan hazaƙa da ake yi da ruwa a ɗiya
na biyu. Ta yi haka dan ta nuna ɗimbin
waƙoƙin fikira da hazaƙa da ake gabatarwa a ranar
mawaƙa.
A ɗiya na uku kuma sai ta yi
amfani da salon abuntawa inda ta kwatanta waƙoƙin fikira da fasaha da mawaƙa ke gabatarwa da tsinkar
bishiyar fikira. Daga nan kuma sai mawaƙiyar ta kawo ƙorafi a baiti na huɗu,
inda take cewa:
Amma Kamis fa duk da
haka,
Ana zagin mu ba
shakka,
Har a sa mu sahu na
‘yan shirka,
A
cire mu sahu na Islama.
A
nan mawaƙiyar
na ƙorafin
cewa, duk da irin gudunmuwa da suke bayarwa wurin yaɗawa
da tallata al’adun Bahaushe, al’umma suna tsangwama gare su. Har ma ana
siffanta su da masu yin shirka. A baiti na biyar ma, mawaƙiyar ta yi ƙorafi na cewa:
Sai a ce kar ka auri
mai waƙa,
Mace ko namijinsu su
duka,
Maroƙa
ne baƙar harka,
Ba
a bambance mu gun ƙyama.
A
nan tana ƙorafi
da yadda al’umma ta ɗauki
mawaƙa
maza da mata a matsayin abin ƙyama,
sannan
maroƙa
masu baƙar
harka. Ta yi amfani da salon kamancen daidaito wurin nuna ƙyamar da ake yi wa mawaƙa maza da mata. Kamar dai
yadda take cewa ba a bambance mu gun ƙyama (bambance mawaƙa maza da mata). Daga nan
sai mai ɗani ya karɓa,
inda shi ma ke ƙorafi
a baiti na shida da cewa:
Fati wai don muna waƙar,
Aka sa mu cikin sahun
shirkar,
Iko daga Rabbana Ƙadir,
Waƙa
ta zam abin ƙyama.
A
nan ya nuna takaicin yadda aka sanya mawaƙa a sahun shirka kawai a
dalilin suna waƙa.
Ya yi amfani da da salon kambama a wannan gaɓa.
Domin kuwa laifin da ake tsangwamar waƙa
da shi bai kai matsayin shirka ba. Amma a nan sai ya kambama abin ta hanyar
kwatanta tsangwamar da tuhuma
game da shirka. A ɗiya
na uku da na huɗu
kuma, sai ya bayyana cewa, waƙa
iko ne kuma Ubangiji, amma jama’a sun kasa ganewa, a maimakon haka, sai suke
tsangwamar masu wannan baiwa ta waƙa.
A baituka na gaba kuwa, mawaƙan
sun yi amfani da salon kamantawa wurin bayyana matsayin waƙa. A baituka na takwas sun
kamanta waƙa
da kwalabe da aka jera, sannan aka sanya musu abubuwa daban-daban:
Idan ga kwalabe an
jera,
Na giya da turare da
madara,
Zuma da ruwa fa har
minira,
A
dukansu a kwalba al’umma.
A
wannan baiti ya yi amfani da salon duguwar siffantawa; inda ya siffanta
nau’ukan waƙa
(ta fuskar jigo) da kwalabe. Kwalaben kuwa sun haɗa
da na giya da na turare da na madara da na zuma na da ruwan minira (lemon
kwalba). A baiti na tara (9), sun bayyana falsafar da ke cikin wannan
siffantawa kamar haka:
Kwalba mai giya
haramun ce,
Amma mai ruwa halali
ce,
Mai zuma kuma magani
dace,
Ga
zaƙi ga waraka kuma ma.
Wannan
baiti na tara (9) na nuni da cewa, waƙa
ba abar ƙyama
ba ce har sai idan jigonta ya kasance abin ƙyama. Mawaƙan sun nuna cewa, jigo da
salon waƙar
da aka yi, shi zai nuna matakin da ya kamata a ajiye ta. Sannan cikin hikima
suka nuna cewa, tun da ya kasance a mawaƙa akwai masu waƙoƙi na gari da ke amfanarwa (misali, faɗakarwa
da ilimantarwa), a ɗaya ɓangaren
kuma akwai waƙoƙin shashanci; ya kamata ne
jama’a su riƙe
waƙoƙin ƙwarai masu nagarta, su fita
batun waƙoƙin shashanci – kamar dai
yadda idan aka jera kwalabai, za a bar na giya a ɗauki
na ruwa da zuma da makamantansu.
A
baituka biyu da suka biyo baya (baiti na 11, da na 12), mawaƙan sun sake fito da maganar
da ke sama fili, suna nuni da cewa; waƙa
na iya kai mutum wuta ko aljanna. Wuta ko aljanna ga mawaƙi kuwa ya danganta da yanayin
waƙarsa.
Suka ce:
Waƙa
na kai mutum fa wuta,
Idan a cikinta yai
wauta,
Tana kuma kai shi
aljannata,
Idan a cikinta yai
salama.
Ko me ka faɗi cikin waƙa,
Da shi za ai
hukuncinka,
In alkairi ka sassaƙa,
In
sharri ne da shi shi ma.
Wato
dai mawaƙan
na ƙara
jaddada cewa, bai kamata a riƙa
yi musu kuɗin goro ba ta hanyar
yi musu kallon banza baki ɗaya.
Domin kuwa, ko da an samu masu waƙoƙin wauta, cikin mawaƙan akwai masu waƙoƙin salama da za ta iya kai
mutum aljanna. A baiti na goma sha biyu (12), sun faɗa
ƙarara
cewa, duk abin da mai waƙa
ke faɗi cikin waƙarsa, da shi ne za a masa
hukunci.
A
baiti na goma sha uku (13) kuwa, sun nuna cewa, waƙa fa ba aikin jahilci ba ce.
Aiki ne na ilimi wanda ko ciki masu ilimi ma, sai ɗaiɗaikun
mutane ke iya waƙa.
Suka ce:
Waƙa
aiki na ilmi ne,
Jahili bai yin ta kun
gane,
Ko mai ilimi sai yai
aune,
Ya
cika ta da tsantsar hikima.
Wannan
magana tasu ta yi daidai da ra’ayin masana waƙa da dama. Masana waƙa suna da ra’ayin cewa, waƙa baiwa ce da Ubangiji ke
sanya wa ɗan Adam. A taƙaice dai ba kowa ke da
baiwar waƙa
ba. Wanda ba shi da baiwar waƙa
kuwa, ko da an yi yunƙurin
koya masa, ba zai iya koya ba.
A
baitukan gaba kuwa (baiti na 14 da na 15), mawaƙan sun kawo wasu muhimman
amfanin waƙa
guda biyu. Suka ce:
Waƙa
na kau da yin yaƙi,
Tana sa wa cikin sauƙi,
Samun ‘yanci fa ba yaƙi,
Tana ɗaga
yarenku sama.
Duk yaren da babu mai
waƙa,
Akwai wahala ya ɗaukaka,
A ƙasa
yaren da ke waƙa,
Sai
ya fi na sauran hawa sama.
A
nan sun ja hankalin jama’a zuwa ga rawar da waƙa ke takawa wurin samar da
zaman lafiya. Za a iya yarda da maganarsu yayin da aka yi dubi da ɗinbin
waƙoƙin da mawaƙa daban-daban suka rera
domin jan hankali da faɗakarwa
zuwa ga zaman lafiya da haɗin
kai da guje wa tashin hankali. Ɗaya
daga cikin ire-iren
waɗannan waƙoƙi ita ce waƙar Abubakar Ladan Zariya mai
suna; ‘Waƙar Haɗin Kan Afirka.’
A
gaba kuwa sai suka nuna cewa, waƙa
wata babbar garaɓasa
ce a cikin yare, da ke taimakawa wajen bunƙasa yaren. Sun nuna cewa,
yaren da ba su da mawaƙa,
ko ba a waƙa
cikinsa, ba zai kai sauran yaruka da suke da mawaƙa ɗaukaka
ba. Za a iya hasashen gaskiyar wannan zance kasancewar waƙa hanya ce ta adana harshe
da yaɗa shi tare da kundace
al’adunsa da dai sauran muhimman abubuwa da suka shafe shi. Waƙa hanya ce da ke sa a riƙa jin amon masu wannan
harshe cikin al’ummun kusa da na nesa.
Mawaƙan sun rufe waƙar da wani dogon baiti mai ɗiya
goma sha huɗu (14). A cikin
wannan baiti suna nuna rukunnen al’umma da ke da daraja cikin duniya da suka yi
waƙa.
Sun haɗa da shuwagabannin ƙasa, kamar yadda suka kawo a
wasu ɗiya na baitin:
Shugabannin ƙasa
suna waƙa,
Muhammad Wardi yai waƙa,
Jibson
Gwarma yana waƙa…
Sun
kuma nuna cewa, manyan malamai ma kuma sahabbai suna waƙa. Cikin waɗannan
sahabbai mawaƙa,
har da wanda ya yi dace da aljanna a dalilin waƙa. Inda daga ƙarshen baitin, suka yi
addu’ar Allah ya haɗa su
da irin wannan dace (ta aljanna). Sun bayyana hakan cikin wasu ɗiya
na baitin kamar haka:
Manyan malamai suna
waƙa,
Sahabbai ma suna waƙa,
Abubakari mai waƙa,
Umar shi ma yana waƙa,
Usuman shi ma yana waƙa,
Imamu Ali yana waƙa,
Annabi ya sa a mai waƙa,
Da mai waƙar
yai waƙa,
Allah ya ji daɗin
haka,
Yai mai kyauta da
aljanna,
Allahu ka sa da mu mu
ma.
7.0 Sakamakon Nazari
A
ƙarshen
wannan nazari, an fahimci manyan abubuwa guda uku, kamar haka:
Mawaƙa a ƙasar Hausa na fuskantar
tsangwama da matsin lamba. Sau da dama akan musu kuɗin
goro kan cewa dukkansu ɓatattu
ne da suka yi tarayya cikin shashanci. Ya kamata al’umma da ma gwamnati ta fahimci
cewa, mawaƙa
ba su taru sun zama ɗaya
ba. Ko da an samu masu waƙoƙin shashanci, akwai waɗansu
mawaƙan
masu ɗimbin yawa da ke waƙoƙi masu ɗauke
da ilimantarwa da faɗakarwa
kan ɓangarorin rayuwa
daban-daban.
Ba
a tallafa wa
masu basirar waƙa
ta fuskar ƙarfafa
sumu guiwa ko ba su agaji na shawarwari da kayan aiki da makamantansu. A
maimakon haka, sai ma akan yi ƙoƙarin mayar da su saniyar
ware. Domin samun cigaba mai amfani, ya
kamata gwamnati da sauran al’umma su riƙa jawo mawaƙa kusa tare da ba su
shawarwari da buƙatar
su (mawaƙan)
rera waƙoƙi kan wasu lamura masu buƙatar a ja hankalin jama’a
gare su (kamar sabbin cututtuka ko wata sara mara kyau da dai sauransu). Za a
ci gajiyar hakan, kasancewar mawaƙan
na da baiwar tura saƙwanni
zuwa ga ɗumbin al’umma cikin ƙanƙani lokaci.
Waƙa na da tasiri matuƙa tare da ɗimbin
amfani wurin isar da saƙwanni
da suka shafi faɗakarwa
da ilimantarwa da nishaɗantarwa
da dai makamantansu. Kasancewar
waƙa
mai ɗimbin amfani, wanda
ko bayan nishaɗantarwa da faɗakarwa
da ilimantarwa,
akan yi nazarinta a makaranti da ke matakan ilimi mabanbanta; ya kamata a samu haɗin
kai da aiki tare tsakanin gwamnati da makaranti da ma sauran al’umma baki ɗaya game da lamarin waƙa, duk don cin
gajiyar alfanunta tare da ƙoƙarin kawar da shagala da ke ciki.
8.0 Kammalawa
Haƙiƙa waƙa hanjin jimina ce, akwai na
ci akwai na zubarwa.
Tasirin waƙa ga al’umma na da
dogon tarihi. Al’ummu da dama na ba wa mawaƙa daraja da ƙima ta musamman. Ko
a cikin Hausawa, ba a ko’ina ba ne, sannan ba koyaushe ba ne ake nuna tsangwama
ga mawaƙa. Duk da haka, mawaƙa a ƙasar Hausa na fuskantar
tsangwama da takunkumin al’ada. Wannan kuwa na
da nasaba da halaye da ɗabi’u da salailai da suka samu a zamanance, waɗanda suka ci karo
da al’ada da addinin Bahaushe na Musulunci. Ƙungiyoyin mawaƙa da hukumomi na da
rawar da za su iya takawa wajen ganin mawaƙa ba su wuce gona da iri ba.
Manazarta
Abdullahi, S. M. (2017). “Kuɗi A Idan
Mawaƙan Hausa Na Baka Da Rubutattu, Waƙar
Kuɗi Ta
Alhaji Audu Wazirin Ɗanduna Da Ta Alhaji
Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja” Kundin digiri na farko da aka gabatar a
Sashen Harunan Nijeriya, Jami’ar Usamnu Ɗanfodiyo
Sakkwato
Bello, S. A. (2017). “Tasirin Waƙa
A Cikin Al’ummar Hausawa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙƙin
Aminu Ladan Abubakar.” Takardar da aka gabatar a taron masoya Aminu Ladan Alan
Waƙa, a makarnatar Ado Gwaram, Kano
Birnin-Tudu, S. Y. (2002). “Jigo da Salon
Rubutattun Waƙoƙin Fura’u
na Ƙarni na Ashirin.” Kundin babban digiri na uku
(Ph. D.) wanda aka gabatar a Sashen Harrunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
Bunza, A. M. (1988). “Nason Kirari Cikin
Rubutattun Waƙoƙin Hausa
na Ƙarni na 20.” Maƙalar da
aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Ɗangambo,
A. (1980). “Hausa Wa’azi Verse
Fron CA 1800 to CA 1970: A Critical Study of Form, Content, Language and Style.
A Ph. D. thesis submitted to the University of SOAS, London.
Dangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Fede Waƙa. Zaria: Amana
publishers LTD.
Gusau, S. M. (2003). Jagora Nazarin Waƙar Baka. Kano:
Benchmark.
Habibu, L. (2001). “Bunƙasar
Rubutattun Waƙoƙin Hausa a
Ƙarni na Ashirin (20).” Kundin digiri na farko
wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato.
Ƙaura, H.
I. (1994). “Ƙawancen Salo a Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin
Wa’azi da Madahu da Kuma Siyasa.” Kundin kammala digiri na biyu (M.A.) wanda a
aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
Maikwari, H. U. (2020). “Wasu Al’adun Hausawa
Cikin Rubutattun Waƙoƙin
Hausa.” Kundin digiri na biyu wanda aka
gabatar a matakin jarabawa ta cikin gida a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Usaman, B.B. (2018). Ruwa-Biyu: Sabon
Zubin Waƙoƙin Ƙarni
Na Ashirin Da Ɗaya. An tsakuro daga: https://www.amsoshi.com/2018/03/ruwa-biyu-sabon-zubin-wakokin-karni-na.html.
Yahya, A. B. (1987). “The Verse Category of Madahu With Special
Reference To Theme, Style and the Background of Islamic Soures and Beliefs.” A
Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo
University,
Sokoto.
Yahya, A. B. (1996). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna:
Fisbas Media Service.
‘Yar’aduwa, T. M. (2010). Jagoran Nazain Rubutaccen Adabin Hausa. Ibadan: HEBN publishers
PLC.
Zurmi, A. D. (2006). “Tsoratarwa a Cikin Waƙoƙin
Wa’azi na Nana Asma’u.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato.
Ratayen Waƙar Ranar
Mawaƙa Ta Fati Da Kasim
Ranar ɗaya ga watan ɗaya,
Ga mu bai ɗaya,
A wuri ɗaya,
Shigarmu ɗaya,
Manufarmu ɗaya,
A ƙasarmu ɗaya Najeriya,
Amshi
Ranar ɗaya
ga watan ɗaya ita ce ranar mawaƙa,
Ranar baje kolin
fikira da nishaɗantar da al’umma.
1. Ya Rabbi Ubangijin
kowa,
Daga mai rai har zuwa
gawa,
Rabbana ka tsare mu
gantsarwa,
Mui waƙar babu ɓamɓarma,
2. Rabbana tsira
amincinka,
Ka daɗa
wa makiyu zaɓinka,
Ka cika shi kakaf da
yardarka,
Don ya tsamo ‘yan
cikin ɓurma.
3. Yau ce ranar mawaƙa,
Rana ta ruwan hazaƙa,
Bishiyar fikira muke
tsinka,
Muke shayar da
al’umma.
4. Amma Kamis fa duk
da haka,
Ana zagin mu ba
shakka,
Har a sa mu sahu na
‘yan shirka,
A cire mu sahu na
Islama.
5. Sai a ce kar ka
auri mai waƙa,
Mace ko namijinsu su
duka,
Maroƙa ne baƙar harka,
Ba a bambance mu gun ƙyama.
6. Fati wai don muna
waƙar,
Aka sa mu cikin sahun
shirkar,
Iko daga Rabbana Ƙadir,
Waƙa ta zam abin ƙyama.
7. Fati waƙa fa kwalba ce,
Ita mai ɗaukar
kalamai ce,
In ta ɗau
mara kyau ta lalace,
Kuma mai yi za ya sha
fama.
8. Idan ga kwalabe an
jera,
Na giya da turare da
madara,
Zuma da ruwa fa har
minira,
A dukansu a kwalba
al’umma.
9. Kwalba mai giya
haramun ce,
Amma mai ruwa halali
ce,
Mai zuma kuma magani
dace,
Ga zaƙi ga waraka kuma ma.
10. Wannan ne
hukuncin waƙa,
In ka ɗau
zance ka sassaƙa,
In mai kyau ne ya
cece ka,
In yai muni akwai
rigima.
11. Waƙa na kai mutum fa wuta,
Idan a cikinta yai
wauta,
Tana kuma kai shi
aljannata,
Idan a cikinta yai
salama.
12. Ko me ka faɗi
cikin waƙa,
Da shi za ai
hukuncinka,
In alkairi ka sassaƙa,
In sharri ne da shi
shi ma.
13. Waƙa aiki na ilmi ne,
Jahili bai yin ta kun
gane,
Ko mai ilimi sai yai
aune,
Ya cika ta da
tsantsar hikima.
14. Waƙa na kau da yin yaƙi,
Tana sa wa cikin sauƙi,
Samun ‘yanci fa ba yaƙi,
Tana ɗaga
yarenku sama.
15. Duk yaren da babu
mai waƙa,
Akwai wahala ya ɗaukaka,
A ƙasa yaren da ke waƙa,
Sai ya fi na sauran
hawa sama.
16. Shugabannin ƙasa suna waƙa,
Muhammad Wardi yai waƙa,
Jibson Gwarma yana waƙa,
Manyan malamai suna
waƙa,
Sahabbai ma suna waƙa,
Abubakari mai waƙa,
Umar shi ma yana waƙa,
Usuman shi ma yana waƙa,
Imamu Ali yana waƙa,
Annabi ya sa a mai waƙa,
Da mai waƙar yai waƙa,
Allah ya ji dadin
haka,
Yai mai kyauta da
aljanna,
Allahu ka sa da mu mu ma.