Citation: Sani, A-U. (2021). Fasihahhiya: Gudummuwar Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy a Fagen Kimiyyar Harshe. In Yakasai. S.A. et al (eds), A Great Scholar And Linguists: A Festchrift in Honour of Professor Ibrahim Ahmad Mukoshy, Pp, 537-543. Kaduna: Amal. ISBN 978-978-59094-3-2.
Fasihahhiya: Gudummuwar Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy a Fagen Kimiyyar Harshe
Na
Abu-Ubaida
Sani
Department
of Educational Foundations
Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto
Phone
No: 08133529736
Email:
abuubaidasani5@gmail.com
J
- Jalla
maƙagin kowa,
Allahu mai rayawa,
Gare ka nai roƙowa,
Na ilmi har ma baiwa,
Kullum ba ka gajiyawa.
I
- Ilahu
yau ma ga ni,
Sai dai a yau ta sauya zani,
Domin kusan karambani-
Na ne kawai ya saka ni,
Wannan aiki nai farawa.
N
- Na
soma aiki mai tsauri,
Batu a kan mashahuri,
Da ke buƙatar tsari,
Da zurfafawar nazari,
Ƙimarsa
na ruÉ—arwa.
J
- Jalla
ba za ni iya ba,
Tab! Ba na ma fara ba,
Da son ka Sarki Rabba,
Zan yi shi ba tababa,
Abin yana rikitarwa.
I
- Idan
rana ta fitowa,
Tafi fa bai karewa,
Muruci in ya fitowa,
Ga dutsi yai shiryawa,
Ka fi su sai hangowa.
N
- Na
so a ce ku biyo ni,
Mu taka dukkan tsani,
Tare da ku kuma ga ni,
Domin ku fahimci bayani,
Kansa gwani É—an
baiwa.
A
- A
farko dai sunansa,
Ibrahim Ahmad sunansa,
Mukoshy inkiya nasa,
Maiwurno ne tushensa,
Sakkwato can gun baiwa.
G
- Gimshi
wajen ilimi ne,
Idan batun haifa ne,
ÆŠai
ga wata na É—aya ne,
Na shekarar nayintin ne,
Sai foti wan É—orawa.
A
- Akwai
É—iya
shida gunsa,
Jamilu babban É—ansa,
Ahmad Rufa’i ka bin sa,
Sai FaÉ—ima
ban Musa,
Mamman da Maimuna nawa.
F
- FirÉ—i!
Batun karatunsa,
Maiwurno yai farkonsa,
Da ke Sudan can nesa,
Nayintin foti sabin sa,
Sai fifti wan ƙarewa.
A
- Al’mahad
Al-ilmin nan,
Da ke a Omdurman É—in
nan,
Intermediate
School É—in
nan,
Nayintin fifti tu É—in
nan,
Fifti sabin ya yi kammalawa.
R
- Rankayawa
yai sakandari,
A Khartoum can yai nazari,
Captic
College wurin nazari,
Nayintin fifti ed fari,
A sisti ed yai ƙarewa.
F
- Farko
nayintin sisti tiri,
Ibadan ya fara yin digiri,
Yunibasiti nan yai nazari,
A sisti fo cikon ƙuduri,
Ashekar yai ƙarewa.
E
- Elum
boko bai masa ba,
Domin bai tsaya haka ba,
Sai da ya ƙara ciwo gaba,
Karatu tuni ya zam babba,
Tabbas ko ya yi ƙwarewa.
S - School
of Oriental ya je,
London can ƙasar waje,
Jami’ar Wisconsin ya je,
Da ke a USA ta waje,
Duk ilm yai ƙarowa.
A
- Akwai
yunibasitin nan,
Sudan a Khartoum É—in
nan,
Tuni ya je har wannan,
Domin biÉ—ar
ilmin nan,
Babba abin gaisarwa.
I
- Idan
ko kwalifikeshin ne,
Tuli garai kowanne,
Abin a-zo-a-yaba ne,
Arabik wannan Ibadan ne,
Yunibasiti yai amsowa.
B
- B.A.
a harshe da al’ada,
Wisconsin can ya ida,
M.A. a Linguistics wanda-
Wisconsin shi ma ya ida,
Abin gwanin ban sha’awa.
R
- Rawar
ganin da ya taka,
Yunibasiti da ya sauƙa,
Can Khartoum ba shakka,
Hakan a Linguistics ya saka,
Ph. D. yai
samowa.
A
- In
batun harshe kuwa,
Yana fahimtar da yawa,
Sa Larabci farawa,
Da Ingilishi daÉ—awa,
Fillanci ya yi ƙwarewa.
H
- Har
French yai ganewa,
Hausa ko sai ƙyalewa,
Domin ko ya yi ƙwarewa,
Ya yi fice da zarcewa,
Fitilarsa na haskawa.
I
- Idan
batun littafai ne,
Ya yi tuli kowanne,
Abin a-zo-a-gani ne,
Suna ilmantarwa ne,
‘FulÉ“e’
kui dubawa.
M
- Mutuncin
Shehu ya duba,
Ya zayyano ba wai ba,
Siffofin
Shehu je duba,
Transciency
Nomadism duba,
Mobile
Education Kammalawa.
A - A
Fulfulde-English Dictionary,
Wannan an masa tsari,
Tindinore
Demuwa ya yi ƙari,
KaÉ—an
ke nan cikin tari,
Yawansu ya fi ƙirgawa.
H
- Haka
yai littafai da yawa,
Sun fi gaban ƙirgawa,
Sannan editan masu yawa,
Gime
Fulfulde farawa,
Sannan da wasu da yawa.
M
- Matsayi
ya fa rirriƙe,
Mai ji zai yo kasaƙe,
Nauyin kansa ya sauƙe,
Cikin adalci ya riƙe,
Kowa yana ta yabawa.
A
- A
É“angaren
koyarwa,
Ya je makaranti da yawa,
Kamar a Sokoto farawa,
Nizamiyya yai koyarwa,
Kowa yana ta yabawa.
D
- DaÉ—i an
ji a Ibadan,
Aikin da yai gadan-gadan,
Sun so riƙe shi har abadan,
A yunibasiti na Ibadan,
Kowa yana ta yabawa.
M
- Mukoshy
har a London ma,
Ya nuna É—abi’un
girma,
A jami’ar S.O. gama,
Ya yo aiki babu zama,
Sabo da zimmar koyarwa.
U
- UDUS
garai ai gida ne,
A ABU sananne ne,
BUK ma
sananne ne,
Unimaid ba
baya ba ne,
Har Khartoum ya yi koyarwa.
K
- Kowa
yana son barka,
Da fatar ƙara ɗaukaka,
Al’umma duk na son ka,
Saboda kyawun halinka,
Da ƙoƙarin ilmantarwa.
O
- Organized mai
recognition,
Ga Allah shi yai submission,
Gaskiya yai adhesion,
Outstanding
in nation,
Farfesa ka sam dacewa.
S
- Sannan
yana da karamci,
Ga shi da kirki da mutunci,
FaÉ—in
gaskiya duk É—aci,
Amana ba ha’inci,
Rayuwar abin burgewa.
H
- Har
kullum kai dace,
Wannan gare ka du’a’i ce,
Aljanna ga kai ta kasance,
Makoma wurin hutawa.
Y
- Yawan
baitukan talatin ne,
Sai shida ‘yan Æ™ari ne,
Na ƙanƙanin
É—alibi
ne,
Abu-Ubaida sunan ne,
Hamdan nai ƙarewa.