Citation: Sani, A-U. & Suleiman, M. (2022). Tsattsafin Haliya: Wani Ɗigo Cikin Tafashen Aminu Ladan Abubakar (ALA). In South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature, Vol. 4, Issue 2, Pp 77-77. ISSN 2664-8067 (Print) & ISSN 2706-5782 (Online). DOI: www.doi.org/10.36346/sarjall.2022.v04i02.005.
Tsattsafin
Haliya: Wani Ɗigo Cikin Tafashen Aminu Ladan Abubakar (ALA)
Abu-Ubaida Sani1
Musa Suleiman2
1Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Nigeria
2Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto,
Nigeria
Tsakure
Manufar wannan bincike ita ce zaƙulowa tare da faɗaɗa nazari a kan salon tsattsafi a cikin waƙa. Binciken ya mayar da hankali kan salon
tsattsafin haliya. An ɗora nazarin bisa ra’ayin Yahya na “Salon Tsattsafi.” An
keɓance nazarin kan zaɓaɓɓun waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) guda bakwai (7)
waɗanda suke mazaunin samfurin binciken. An ɗauki waɗannan waƙoƙi a matsayin
tushen bayani na farko. Tushen bayani na biyu da binciken ya yi aiki da shi,
shi ne rubuce-rubucen masana da suka gabaci wannan. Binciken ya tabbatar da
cewa, lallai mawaƙi na tsattsafin haliya ko haliyoyi a cikin waƙa. Haka kuma,
yana iya tsattsafin haliya guda a cikin waƙoƙi daban-daban da ya shirya yayin
da yake cikin yanayi iri guda. A bisa haka, binciken na ganin za a iya amfani
da wannan salon nazari a matsayin matakin bincike kan halaye da ɗabi’u.
Fitilun Kalmomin: Tsattsafi, Haliya, Waƙa, Salo
Gabatarwa
Salo a fagen adabi ba al’amari ne da ya shafi waƙa kawai ba. Wani makeken kandami ne wanda da wuya a iya kai
ga ƙarshensa. A fage na nazarin salo kullum ido na kaiwa ga wasu sababbin salailai da ba a nazarce su ba a
baya (Yahya, 2013). Salon tsattsafi
ya fito ne daga nazarin Yahya (2013).[1] Aikin nasa ne ya
zama tubalin gina wannan bincike.
Takardar ta mayar
da hankali wajen faɗaɗa nazari kan
salon tsattafin haliya a cikin wasu waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa).
Ta haka ne za a iya kallon matakan da ya bi domin barbaɗa haliyoyin zuciyarsa a
cikin wasu waƙoƙinsa. Kai tsaye, binciken ya mayar da hankali kan muhimman
abubuwa da suka haɗa da:
a. fito da yadda
Aminu ALA ya yi tsattsafin haliya a cikin wasu waƙoƙinsa,
b. gano nau’ikan
tsattsafin haliya da ya yi amfani da su a cikin wasu waƙoƙinsa,
Dabarun Gudanar Da
Bincike
Wannan takarda ta
tattara bayanan da aka nazarta kai tsaye daga tushen farko (primary source).
Wannan tushe ya kasance zaɓaɓɓun waƙoƙin ALA da ke cikin samfurin binciken. An
saurari waƙoƙin sannan aka rubuta su kamar yadda aka ji mawaƙin na rerawa. A ɓangare
guda kuwa, bayanan da aka samu daga rubuce-rubucen masana sun yi ƙarin haske da
jagoranci ga wannan bincike.
An ɗora wannan
bincike kan ra’ayin Yahya, (2013) na Salon Tsattsafi. A bisa wannan
fahimta, a cikin waƙoƙin ALA ana iya samun tsattsafin tunani da ra’ayoyinsa,
ciki har da na haliya. Idan kuwa haka ne, za a iya tsintar ɗangwaye a cikin
baituka da ba sa jere da juna waɗanda ke ɗauke da tsattsafin haliyar da ake
magana kanta. Tattara tsattsafin haliyar mawaƙi wuri guda na iya samar da
madubin da za a iya kallon hoton zuciyarsa, ra’ayoyinsa, halayensa da ɗabi’unsa,
da ma al’adarsa a kammale.
Malam Aminu Ladan
Abubakar (ALAN Waƙa) ya yi waƙoƙi da dama waɗanda suka shafi fannoni
daban-daban na rayuwar al’umma. Wannan bincike ya taƙaita ga bakwai (7)
daga cikin waƙoƙin a matsayin samfarun binciken. Kadadar binciken ta taƙaita
kan wannan samfuri. Waƙoƙin da ke cikin samfurin binciken su ne:
i. Waƙar Zuciya
ii. Waƙar Ɗan Birni
iii. Waƙar Wayyo Kaico
iv. Waƙar Garin Gumel
v. Waƙar Marainiya
vi. Waƙar Komai Ya Yi Kyau
vii. Waƙar Miftahul-Futahati
Waiwayen Tarihin Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa)
Tarihin ALA ba ɓoyayye
ba ne a ƙasar Hausa. Wannan ya samo asali daga ficen da ya yi bayan watsuwar
waƙoƙinsa da suka karaɗe ƙasar Hausa. Akwai rubuce-rubuce da dama da aka gudanar
a matakan ilimi daban-daban game da shi da kuma waƙoƙinsa. Daga cikinsu akwai
Faragai, (2008) da Imran, (2008) da Malami, (2010) da Hamza, (2011)A
da Hamza, (2011)B da Lawan, (2011) da Umar, (2011) da Mohammed,
(2014) da Lawal, (2015) da Ahmad, (2017) da Sulaiman, (2017) da Yakasai &
Sani, (2021). A bisa wannan, kawo tarihinsa tiryan-tiryan zai zama maimaici ne
kawai kan abin da aka riga aka kundace a rubuce-rubuce da suka gabaci wannan.
Sakamakon haka, wannan takarda za ta mayar da hankali kan kawo waɗansu muhimman
al’amura da suka shafi rayuwarsa kawai.
Malam Aminu Ladan Abubakar da kansa ya yi
tsokaci game da haihuwarsa a inda yake cewa:
Shekararrun haihuwata,
Ƙirgar
shari’ar Nabina.
Hijira ta alif dubu ɗai,
Da ɗari uku da ɗugunna.
Ma’anar manufar ɗugunna,
Casa’in da uku
nufina.
A Municipal Kanawa,
Yakasai ta garina.
Nan ne aka haihuwata,
Labarin assalina.
(ALA: Waƙar Shahara Ta 1, 19-23)[2]
Dangane da
karatunsa na boko da na Islamiya kuwa, yana cewa:
Nai ilmin Islama,
Matayassara
gwargwadona.
Nai ilmi zamanina,
Boko
dan zamanina.
Gwargwado dai diploma,
Nai
domin kare kaina.
Nai kan Art and design,
Ƙirƙirar zane fununa.
(ALA: Waƙar Shahara Ta Ɗaya, 24- 27)
Wani babban
tagomashi da ALA ya samu a rayuwarsa shi ne sarautun gargajiya daban-daban.
Wannan ya ƙara masa fice tare da ɗaukaka sama da mawaƙan Hausa da dama.
Sarautun da yake riƙe da su sun haɗa da:
a. Sarkin Waƙar Dutse (Sahibul-Hikima), a
masarautar Dutse da ke jahar Jigawa
b. Ɗan Amanar Bichi, a masarautar Bichi da
ke jahar Kano
c. Dujimin Ƙaraye, a masarautar Ƙaraye da
ke jahar Kano
d. Ɗanburan Gobir, a masarautar
Gobir/Sabon birni da ke jahar Sakkwato
e. Sarkin Ɗiyan Gobir, a masarautar Maraɗi
da ke Jamhuriyar Nijar
f. Fasihin Hausawan
Duniya[3]
Salon Tsattsafi
Kamar yadda Yahya,
(2013) ya bayyana, salon tsattsafi
salo ne da ke nufin kawo ƙunshiyar
tunani ko cusa wata haliya a wurare daban-daban cikin waƙa. Ya kuma shafi amfani da wani salo akai-akai (wato a yayyafa ko barbaɗa shi) cikin waƙa
ko kuma mafi yawan waƙoƙin marubuci idan gaba ɗayansu ne ake nazari. Tsattsafi a waƙa haka yake kamar ƙyallin taurari cikin sararin samaniya
ko ɗiyan rana
(kawalwalniya) cikin yashi ko kuma ƙyallin kwalli
wanda ya barbaɗa a kan daɓe.
A bisa wannan, za a yi cewa salon tsattsafi salo ne
da mawaƙi ko marubuci ke yin
yayyafi ko barbaɗen haliyoyin zuciyarsa ko harshensa ko al'adunsa a cikin waƙa
ko rubutunsa. Ta la’akari da
wannan ma’anar, za a fahimci
cewa salon tsattsafi yana da rassa da dama waɗanda suka haɗa da:
a. tsattsafin haliya,
b. tsattsafin harshe,
c. tsattsafin al’ada, da dai sauransu (Yahya, 2013).
Haka kuma, ana iya karkasa
waɗannan salailai da aka lissafo a sama zuwa ƙananan rukunoni. A taƙaice za su
iya kasancewa kamar haka:
A. Tsattsafin Haliya: A nan ana iya samun (i) tsattsafin
raha da (ii) tsattsafin ɓacin rai da (iii) tsattsafin fushi da (iv) tsattsafin murna da (v) tsattsafin bege da (vi) tsattsafin tausayi, da makamantansu.
B. Tsattsafin Harshe: A nan ana iya samun (i) tsattsafin
Ingilishi da (ii) tsattsafin Fillanci da (iii) tsattsafin Larabci da (iv) tsattsafin Kanuri da (v) tsattsafi Yarbanci da (vi) tsattsafin Inyamiranci, da
sauran makamantan harsuna.
C. Tsattsafin Al’ada: A ƙarƙashin wannan rukuni, ana iya samun ƙananan
rukunoni da suka haɗa da (i) tsattsafi fada da (ii) tsattsafin
noma da (iii) tsattsafin
dambe da (iv) tsattsafin
wasanni da (v) tsattsafin
sutura da (vi) tsattsafin
abinci da (vii) tsattsafin biki,
da sauransu.
Tsattsafi Haliya a Cikin Waƙoƙin ALA
Yanayin da zuciya take ciki, ko kamar yadda Hausawa kan ce: “Labarin zuciya...” shi ne ake kira haliya. Haliyoyin zuciya kuwa suna da yawa. Daga ciki akwai fara’a, ɓacin rai, fushi, baƙin ciki, murna, nadama, da-na-sani,
bege, ƙauna, ƙiyayya, da dai sauransu. A bisa haka, idan aka ce salon tsattsafin haliya
ana nufin barbaɗa ɗaya ko fiye daga cikin waɗannan haliyoyi
cikin waƙa. A misali, ana iya samun ‘salon tsattsafin raha’ ko ‘salon tsattsafin bege’
ko ‘salon tsattsafin soyayya’ ko wani makamancin wannan.
A mafi yawan
lokuta, salon
tsattsafin haliya ya dogara ne kan alaƙar zuciya da
kalmomin waƙa. Zuciyar mawaƙi ko ta manazarci ita ce za ta ji ko ta
ɗanɗani ko ta gani tare da jinjina kalma ko kalmomi masu ƙunshiyar haliya. A wani lokaci kuma mawaƙi kan yi amfani da salailai domin ya
cusa haliyar cikin waƙoƙinsa. Misali,
yana iya amfani da kalmomi masu kaifin ma’ana domin yin hakan. Bisa ga haka, za a iya cewa salon tsattsafi salo ne da
waƙa kan bayyana wani abu da yake cikin zuciyarsu, wanda yakan iya kasancewa
farin cikin ne ko ɓacin rai ko murna ko wanin hakan.
Idan aka kalli waƙar zuciya ta Aminu Ladan Abubakar, za
a tarar inda ya bayyana haliyar zuciya a cikin baiti na (1) zuwa
na (3). A cikin waɗannan
baituka, ya bayyana haliyoyin da
zuciyarsa take ƙullawa. Yana cewa:
1. In na shirya zan je Brigade sai ta mai da ni
Tarauni,
In
na durƙusa nai zaune
yanzu ka ga ta tada ni.
2. In na yunƙura na miƙe take ka ga ta zaune ni,
Nai
gabas ana madalla baya za ta zo maida ni.
3. Na yunƙura hannun dama sai dawayar ni hauni,
Bari
zuciya bar ja na kar ki mai da ni majanuni.
(Aminu
Ala: Waƙar Zuciya, 1-3)
Idan aka kalli waɗannan baituka za a ga cewa ALA ya
bayyana irin haliyoyin da zuciyarsa ke ƙulla masa, wanda idan ya yi niyyar shuka abin
alkhairi sai ta so ta cusa masa akasin haka.
Tsattsafin Raha
Salo ne da mawaƙi ke nuna farin cikinsa da nishaɗi a cikin waƙoƙinsa. A nan mawaƙi yakan bayyana haliyoyin raha ta amfani da kalmomin da ke nuna raha. Akan yi hakan ta
hanyar yin tsattsafinsu
a cikin baitukan waƙa. ALA ya yi amfani da
wannan salo a cikin waƙarsa ta “Ɗan Birni” a
baiti na 7 zuwa na 9. A ciki ya yi tsattsafin raha inda yake cewa:
7. Ni ma da
lafiya naka waƙa,
Har nay yi ‘yar rawa
nai tsalle.
8. Kuma ku rausaya fa ku risa,
In
kun ga sarari kui tsalle.
9. Mata a rausaya fa a risa,
In
an ga sarari ai tsalle.
(ALA: Waƙar Ɗan Birni, 7- 9).
Idan aka dubi waɗannan baituka za a ga mawaƙin ya rubuta waƙar a lokacin da yake
cikin nishaɗi da fara'a. Za a iya lura da
hakan musamman idan aka mayar da
hankali kan ire-iren kalmomin da ya yi amfani da su. Kalmomin sun haɗa
da rawa, tsalle, rausaya, risa... dukkanninsu kalmomi ne da ke nuna raha da nishaniɗi a zuciyar mawaƙi.
Tsattsafin Ɓacin Rai
Salo ne da mawaƙi ke amfani da shi domin nuna irin
haliyar da zuciyarsa ta shiga a yayin da yake cikin ɓacin rai. Wannan ne ya sa idan mawaƙi ya yi waƙa a irin wannan yanayi, ya zama dole sai ya yi tsattsafi na haliyoyin ɓacin rai a cikin baitukan waƙarsa. ALA ya nuna irin wannan haliyoyi a
cikin waƙarsa ta ‘’Wayyo Kaico’’ a baiti na 6. Ya nuna ɓacin ransa ta hanyar yin zambo a cikin baitin waƙar. Yake cewa:
6. Wai gyartai ka
bai wa ƙirar mota,
Mai ƙira ka ba shi saƙar mata,
Ya zama ‘yar burum-burum ɗan wauta,
An yi fagabniya ya mai tatata, wayyo kaico!
(ALA: Waƙar Wayyo Kaico, 6).
A nan mawaƙin ya nuna ɓacin ransa ta hanyar yin zambo, da kuma amfani da
kalmomi irinsu wayyo kaico. Ya nuna takaicinsa game da yadda aka kasa ajiye komai a hulallin da ya
dace.
Ba a iya wannan waƙar kaɗai ya nuna haliyar ɓacin rai ba. Idan aka dubi waƙar “Garin Gumel” a baiti na 13, za a ga yadda ya nuna mutuƙar ɓacin ransa. Yana cewa:
13. Bana an yi
gumi nai sharkaf ya jiƙa ni,
Na taho nai murna gun sarkinmu sani,
Mahara mafasa ƙwauri kawai suka hana ni,
Sai na dawo gida ɓacin rai ya ƙume ni.
(ALA: Waƙar Garin Gumel, 13).
A nan ma an ga yadda ya nuna cewa ya taho domin ya yi murna ga sarki amma mahara mafasa ƙwauri (‘yan daba) suka hana shi. Haka ya dawo gida cikin ɓacin rai. Ya yi amfani da kalmomi irinsu; wayyo, kaico, ɓacin rai, da ƙumewa domin nuna
haliyarsa.
Tsattsafin Tausayi
Salo ne da mawaƙi ke amfani da shi domin ya nuna haliyar
tausayi, wanda
zuciyarsa ta tsinci kanta a ciki. Irin wannan haliyoyi su ne makaman da za su
nuna wa mai sauraro ko mai nazari irin tausayawar da mawaƙi ya yi da kuma yanayin da zuciyarsa ta
shiga ciki. ALA ya yi
amfani da irin wannan salon a cikin waƙarsa ta “Marainiya.” A cikin waƙar yana cewa:
Abin ban tausai gidan marayun yara,
Abin ai kaico
hawaye sui ta darara,
Abin su marayu dagwai-dagwai ‘yan yara,
Wasu haɗarin mota a kai suka zam maraya,
Wasu ko tsinto ake a cikin shara,
Wasu masu taɓin hankali ka haifa yara,
Sababi na haɗakarsu ba shi ƙirgo yara,
Wasu ‘yan jarira a kan gadonsu na yara,
Wasu na tatata da rarrafe ‘yan yara,
Wasu na makarantar karatun ta mora,
Wasu an kakkai su sakandare da kara,
Ba uwa babu uba haɗin gamayyar yara,
Gida ɗaya amma kamarsu bamban yara,
Wani na zaluntar na ƙas da shi dan ƙwara,
Wani jarumta wani shagwaɓa ‘yan yara,
Wani ba ƙoshin lafiya
cikin ‘yan yara,
Wasu ko ƙoshin lafiya kamar tantabara,
Abinci idan za a ba su tamkar fara,
Jerin gwano suke kamar masu bara,
Gidansu matsattse sai ka ce tantabara,
Gidansu guda ɗaya jal ku je kui duba.
(ALA: Waƙar Marainiya)
Mawaƙin ya nuna
tsantsar tausayinsa ga yaran da ya tarar a gidan marayu saboda irin halin da ya
tsince su a ciki. Ya gan su ‘yan dagwai-dagwai ba uwa ba uba. Wasu na tafiya, wasu a kan gadonsu na
yara, wani na tatata, wani jarunta, wani shagwaɓa. Haka kuma, idan
za a ba su abinci tamkar fara. Wannan ne ya sa bai ankara ba sai ya ga hawaye yana zubo masa saboda
tsananin tausayi da ya kama shi.
Tsattsafin Fushi
A nan, mawaƙi na amfani da haliyoyin fushi ko wasu
mizanai da ke iya nuna fushi a yayin gudanar da waƙa. Aminu Ladan Abubakar ya yi amfani da irin wannan salon a cikin waƙarsa ta “Garin
Gumel” a baiti na (1) da na (2), inda yake cewa:
1. Bana na ga
daren kure na ba da baya,
Sukuwa da
makahon doki na ƙidaya,
A bikin sallar
gani na hangi shirinya,
Bana ga abin
al’ajabi ya suƙe ni.
2. Taro irin na
gani tushensa maulidi ne,
Taro irin na
gani tushensa al’ada ne,
Taro irin na
gani tushensa zumunci ne,
Mahara mafasa ƙwauri kawai suka hana ni.
(ALA: Waƙar Garin Gumel)
Idan a ka kalli waɗannan baitukan, za a ga cewa mawaƙin ya nuna fushinsa ta hanyar amfani da
mizanin fushi domin ya nuna irin fusatar da ya yi. Ire-iren waɗannan kalmomi da ya yi amfani da su sun
haɗa da;
daren-kure, sukewa,
makahon doki, hanawa, da sauransu. Ya yi hakan ba don
komai ba sai saboda ya je ne garin Gumel domin ya taya sarkin Gumel murnar
sallar Gani, amma ‘yan daba da mahara suka kawo farmaki suka tarwatsa taron
nasa. Wannan ne abin da ya yi mutuƙar ɓata wa Aminu ALA rai har ya bayyana
fusatarsa a cikin wannan waƙa.
Tsattsafin Murna
Shi ma yana ɗaya daga cikin rassan tsattsafin
haliyya, inda akan samu
mawaƙi ɗauke da murna da farin ciki, wanda hakan ne zai sa ya gudanar da waƙarsa
a cikin wannan yanayi na annashuwa. To a nan dole za a samu ya yi yayyafi
ko barbaɗa tsattsafin
haliya na murna da farin ciki ta hanyar amfani da wasu mizanai da za su nuna
irin yanayin sakewa da yake ciki.
Aminu Ladan Abubakar ya yi amfani da irin wannan salo a
cikin waƙarsa ta “Komai Ya Yi Kyau,” wadda ya yi wa mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero. A baiti na 8 da
na 10 yana cewa:
8. Lale-lale duk jama’ar Kano suna ma lale da alfahharo,
Yaran sauka
‘yan tahafizu na oyoyo ga ɗan Bayero,
Gatan kumbo ka
dawo gare mu sai madalla
mui ayyiraro,
Matan birni
sai guɗa suke suna
yin nishi suna ta
asayyaro,
Tamkar baba in na rufe idona na buɗe Ado Bayero.”
Ba a iya nan ya tsaya ba. Ya ƙara bayyana farin cikinsa a cikin baiti na goma
(10) inda yake
cewa:
10. Birni ƙauye sai guɗa ake ana ga Ado sak ɗan Bayero,
Har kaikawon nan fa da kas sani ga fararen
kaya jikan Bayero,
Na tsinkaya na aza mai Kano ne ashe mai Bichi ne ɗan Bayero,
Sai na ga ƙwalla na ta ciko ido tunani na can baya
ya warwaro,
Kan takawa marigayi mai Kano madubin mulki ba siddadaro”.
(ALA: Waƙar Komai Ya Yi Kyau, 8-10)
A cikin waɗannan baitukan ALA ya nuna mutuƙar murnarsa, inda
ya yi amfani da kalmomi irinsu: lale-lale da ayyiraro da assayyaro. Haka kuma, ya nuna yadda mutanen
birni da na ƙauye suke murna da dawowar Aminu Ado Bayero, da yadda ‘yan sauka
suke murna. Wannan ne har ya sa shi tunowa da sarki Kano marigayi Ado Bayero.
Tsattsafin Bege
Bege na ɗaya daga cikin rassan tsattsafin haliya. Akan samu mawaƙi na begen abin da yake so yake kuma ƙauna. A nan mawaƙi kan yi amfani da haliyoyin ƙauna domin ya bayyana irin son abin da
yake bege. Aminu Ladan Abubakar ya yi amfani da irin wannan salo a
cikin waƙarsa ta “Miftahul-Futuhati ta 1.” Za a ga hakan a
baituka na 36 zuwa na 45. A ciki ya kira Ma’aiki (S.A.W) da “linzamin rayawata.” Hakan ya
nuna mana cewa shi ne ke juya duk wasu
al’amura na rayuwarsa. Da jin ire-iren waɗannan kalamai na ALA za a iya fahimtar so
da ƙauna ce ta sa
shi ya yi haka. Yana cewa:
36. Na yunƙura in yi yabon masoyi,
Annabi
ne babban masoyi.
37. Mai darajar
da ta zarce shayi,
Mai hali na yabo da koyi.
38. Mai nasaba ciki babu shayi,
Rabbu hane ni ni da in yi sanyi.
39. Kan lamarin da na tsara zan yi,
In
yabi Annabi babu shayi.
40. Babu kure ciki ba bulayi,
Sai
madarar ƙaunar masoyi.
41. In faɗi tarihin masoyi,
Kuj ji busharorin masoyi.
42. Babu kasala babu sanyi,
Ba nukusani babu shayi.
43. Ku ji abin da yahudu kan yi,
Daga
busharorin masoyi.
44. Duk a cikin waƙar da zan yi,
Nutso
a cikin bahari fa zan yi.
45. Hujjoji na zuwan masoyi,
Har
ahlil kitabi sun yi.
(ALA: Waƙar Miftahul-Futuhati ta 1, 32-45)
A nan, mawaƙin ya nuna irin ƙauna da tsantsar soyayyar Ma'aiki da suka saka shi begensa. Ma’aunan haliyyar
bege da ya yi amfani da su sun haɗa da;
masoyi, zarce, babu kamar shi, ba nukusa ni, madarar ƙauna, babu kasala, da sauransu.
Sakamakon Bincike
Lallai akan samu
tsattsafin haliya a cikin waƙoƙi. An ga misalan kalamai da ke mazaunin mizanan
haliyar tausayi a cikin Waƙar Marainiya. An kuma ga na fushi a cikin Waƙar
Garin Gumel, duk na Aminu Ladan Abubakar. A taƙaice ke nan, haliyoyi da
mawaƙi ke iya tsattsafawa cikin waƙa suna da yawa. Za a iya kallon hakan cikin
waƙoƙin ALA inda aka samu tsattsafin haliyoyi da suka haɗa da na fushi da bege
da raha da sauransu.
A ɓangare guda
kuwa, binciken ya fahimci cewa ana iya nazartar tsattsafin haliya ta fuskoki
guda biyu. Fuska ta farko ita ce ganowa da ƙwanƙwance haliya ko haliyoyi
daban-daban cikin waƙa guda. Ke nan wannan na nuna cewa, ana iya samun haliyoyi
sama da guda a cikin waƙa ɗaya. An ga irin haka a cikin Waƙar Komai Ya Yi
Kyau. A cikin waƙar, an ga yadda tsattsafin tausayi ko jimami ya keta cikin
na murna. An kawo hakan cikin baiti na 10 yayin da jimamin rashin sarki ya kai
ga mawaƙin zubar da ƙwalla alhali yana tsakiyar murna.
A ɗaya fuskar
kuwa, ana iya nazartar tsattsafin haliya guda cikin waƙoƙi daban-daban. Ana iya
ɗaukar ɗaukacin waƙoƙin mawaƙi ko waɗansu daga cikinsu domin nazartar wata
haliya ko waɗansu haliyoyi. A irin wannan yanayi, za a riƙa bin waƙoƙin ɗaya
bayan ɗaya domin zaƙulo wuraren da haliyar ko haliyoyin da ake nazari suka
bayyana domin ƙwanƙwance su.
Naɗewa
Ko bayan
kasancewar adabi wani madubin hango rayuwar al’umma, nazarin tsattsafin haliya madubi
ne ko hoto da za a iya kallon mawaƙi a cikinsa kai tsaye. Salon nazari ne da ka iya taimakawa wajen gano abin da
ke ƙunshe cikin zuciyar mawaƙi yayin da yake barbaɗa wannan ƙunshi cikin
baitukan waƙa ko waƙoƙinsa. Har ila yau, hanya ce da ka iya taimakawa wajen
gano asalin yanayin mawaƙi ta fuskar sauƙin kai ko zafin kai, jarumta ko
ragwanci, soyayya ko ƙiyayya, lalama ko saurin fushi, da dai sauransu. Salo ne
da ke buƙatar ƙarin nazari domin ƙwanƙancewa sala-sala ta yadda za a ci
cikakkiyar gajiyar hikimomi da ke ƙunshe ciki.
Manazarta
Adewale, E. O.(1984). An Introduction to Social Anthropology.
Ibadan: Agbo Areo Publishers.
Ahmad, S. B.
(2017). Tasirin Waƙa A Cikin
Al’ummar Hausawa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). Takardar da aka gabatar a wajen taron Masoya
Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa a ɗakin taro na Makrantar Ado Gwaram da ke kan titin
Gidan Namun Daji, Kano.
Aliyu, S. B. (1986). “Alhaji Isah
Mai Kukuma Mina Da Waƙoƙinsa.” Kundin digiri na
farko jami’ar Sakkwato.
Bunza, A.M.
(2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Center Limited.
Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon
Feɗe Waƙa. Kano: Amana publishers.
Faragai, N. A.
(2008). Nazarin Salo Da Sarrafa Harshe A Waƙoƙin Aminu Ladan
Abubakar (ALA). Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano
Gobir, Y. A. da Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin
Hausa Na Gargajiya. Amal Printing and Publishing, Nigeria.
Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i Da
Tarke A Adabi Da Al’adu Na Hausa. Kano: Century Research and Publishing
Gwammaja, K. D. (2018). Jagoran Nazarin Karin Magana. Kano: Kdg publishing limited.
Hamza, M. K.
(2011)A. “Nazarin
Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminuddeed Ladan Abubakar (ALA). Kundin digiri
na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato.
Hamza, M. K.
(2011)B. Salo da
Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar. Kundin digiri na farko
wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato
Imran, A. L.
(2008). Jigo da Salo a Waƙoƙin Aminu ALA. Kundin digiri na farko wanda aka
gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya
Lawal, M.
(2015). “Yabon Sarakuna A Waƙoƙin ALA: Nazari Daga Waƙar Bakan Dabo Da Waƙar Farar Aniya Farar Atafa.” Kundin digiri na biyu
da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Jahar
Kaduna.
Lawan, M. B.
(2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar ALAn Waƙa, Littafi na Ɗaya. Kano: Iya Ruwa Publishers.
Magaji, B. (2009). “Nazarin Aron Kalmomi a Waƙoƙin Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa.” Kundin digiri na farko. Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Malami, U.
(2010). “Jami’a Gidan Ban Kashi: Nazarin Matsayi Da Kimar Jami’a Ga Cigaba da
Bunƙasa Al’ummar Hausawa.” Kundin digiri na farko
wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
Mohammed, Y.
(2014). “Kwatanta Salon Wasu Waƙoƙin Aminu ALA Da Na Fati Nijar.” Kundin digiri na
biyu wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero,
Kano.
Muhammad, D. (1980). “Waƙa
Bahaushiya” Cikin studies in Hausa Language, Literature and culture. Kano: Bayero University.
Muhammad, D. (1980). Zumunta
Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Hausa da Makaɗa. Cikin Harsunan Nijeriya na 4. Kano: Bayero University.
Omar, S. (2013). Fasahar Mazan Jiya
Nazarin A kan Rayuwa Da Waƙoƙin Malam Malam Mu’azu Hadeja. Kaduna: Garkuwa
Media Service Limited.
Sulaiman, I. M.
(2017). Salon Hoton Zuci: Nazari A Waƙar Ta’aziyar
Yahaya Mahmud Da Ta Ado Bayero na Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). Takardar da aka gabatar a wajen taron Masoya
Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa a ɗakin taro na Makrantar Ado Gwaram da ke kan titin
Gidan Namun Daji, Kano.
Umar, R. A.
(2011). “Matsayin Uwa a Bahaushiyar Al’ada: Nazarin Waƙar ‘Ummina’ ta Aminu Ladan Abubakar.” Kundin
digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato.
Yahya, A. B. (2004). “Tsattsafin Raha Cikin Waƙoƙin Alƙali Haliru Wurno”. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Yahya, A.B. (1997). Jigon Nazarin
Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
Yahya, A.B. (1999). Salo Asirin
Waƙa. Kaduna: Fisbas Media
Services.
Yahya, A.B. (2013). “TSATTSAFI: Wani Ɗigo Cikin Nazarin Salon Waƙoƙin
Hausa.” Takardar da aka gabatar a
taron ƙara wa juna sani. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriaya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato.
Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021).
Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Nigeria: Amal Printing Press. ISBN: 978-978-57624-9-0.
[1] A duba takardarsa mai
taken “TSATTSAFI: Wani Ɗigo Cikin Gulbin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa.”
[2] A baitocin da ke sama,
za a ga cewa ALA ya bayyana ranar haihuwarsa da wurin da aka haife shi.
[3] An yi masa wannan naɗi ne a
taron ranar Hausa ta duniya a jahar Gwambe.
author/Sani, A-U. & Suleiman, M.
journal/South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature
pdf-https://www.researchgate.net/publication/360182365_Tsattsafin_Haliya_-_Wani_Digo_Cikin_Tafashen_Aminu_Ladan_Abubakar_ALA
paper-https://www.researchgate.net/publication/360182365_Tsattsafin_Haliya_-_Wani_Digo_Cikin_Tafashen_Aminu_Ladan_Abubakar_ALA