Abstract
The paper is an analysis of a poem titled “Waƙar Alhakin Mumini
Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” (The Rights of a Believer Upon a Believer and
the Upbringing of Children) written by Isan Kware Ɗan Shehu. Attempt
was made to bring out the major and minor themes of the poem as they relate to
the social life of the Hausas. The various stylistic devices that he used in
the poem were identified to be symbolism, metaphors and alliteration among
others. Ɗangambo’s 2007 model of analyzing poetry was used. It was found that, he
used a simple language and showed expertise in his choice of words to pinpoint
socio-religious issues directed at the Hausafolk. The paper finally suggested
that experts need to analyze more of such works as an effort of inculcating
good moral values to the general society.
Keywords: Rights; Social
Interaction; Child Orientation; Isan Kware
Gargaɗi ga Kyautata Zamantakewa: Faɗakarwa Daga Alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu
Dr. Bello Bala Usman1 and Abu-Ubaida Sani2
1. Department of Nigerial Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria
2. Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria
Tsakure
Wannan takarda nazari ce na “Waƙar Alhakin Mumini Bisa
Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware Ɗan Shehu. A cikin takardar, an yi ƙoƙarin
fito da babban jigon waƙar da kuma ƙananan jigogi tare da warware su domin gane
haƙiƙanin saƙon da waƙar ke ƙoƙarin isarwa. Bayan nan an yi ƙoƙarin fito da
ire-iren salailan da mawaƙin ya yi amfani da su a matsayin dabarar isar da saƙo.
Sun haɗa da salon alamci da siffantawa da sauransu. An ɗora wannan nazari ne a
kan hanyar nazarin waƙa na zamani wanda ya ke ƙarƙashin mazhabar Ɗangambo,
(2007: 10). Daga ƙarshe kuwa an kawo sakamakon nazarin haɗe da shawarwari. Takardar
ta fahimci cewa, sha’irin ya yi amfani da harshe mai sauƙi da kuma zaɓaɓɓun
kalmomi domin isar da saƙonninsa. An ba da shawarar cewa, manazarta su ƙara ƙaimi
wurin nazartar ire-iren waɗannan waƙoƙi domin fito da saƙonninsu fili, tare
kuma da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin karantar da waƙoƙin a
makaranti, wanda hakan na iya tasiri matuƙa a ɓangaren gyaran tarbiyya.
Muhimman Kalmomi: Alhaki; Zamantakewa;
Tarbiyyar Yara; Isan Kware
Taƙaitattun Kalmomi
WAMBMTY: Waƙar
Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara
Bt.: Baiti
Ɗg: Ɗango
Ƙ: Ƙarni
1.1
Gabatarwa
Wannan
aiki ya shafi nazarin waƙa ne. Waƙar kuwa rubutacciya ce wadda ta kasance cikin
jerin waƙoƙin ƙarni na goma sha tara. Masana da dama sun bayyana ma’anar waƙa a
rubuce-rubucen da suka gudanar a matakan ilimi daban-daban.[1] Daga cikinsu akwai Ɗangambo,
(2007: 5) da Sarɓi, (2007: 1) da Yahya, (2016: 26) da sauransu. Rubutacciyar waƙa
dai tsararren zance ne da ke tattare da hikima da fasaha da zalaƙa wanda ake
rubutawa cikin salo da zubi da tsari na musamman. Wannan ya ƙunshi abubuwan da suka
haɗa da jeranta tunani da amfani da amsa-amo da kari da salailai daban-daban.
Waƙa
aba ce mai matuƙar amfani a tarihin ɗan’adam musamman saboda tasirinta ga zukata da kuma saurin isar da saƙo.
Tarihi ba zai taɓa mantawa da rawar da rubutattun waƙoƙi suka taka ba a ƙarni
na goma sha tara (Ƙ19) musamman lokacin jahadi ƙarƙashin jagorancin Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo. Hassan, (2019: 1) ya bayyana cewa, masana da dama sun
tabbatar da ingancin waƙa wajen isar da saƙo. Waɗannan masana sun haɗa da:
Abdulƙadir, (1974: 7) da Abdulƙadir, (1979: 10) da Dumfawa, (1990: 26) da Omar, 2013: ix) da Yahya, (2016: 2) da Idris, (2016: 1)
da Bunza, (2016: 29).
An
raba wannan takarda zuwa manyan rukunoni guda biyar (5). Na farko shi ne
gabatarwa inda aka yi tsokaci kan mawaƙin (Isan Kware) da kuma waƙar da ake
magana a kanta “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara.” Ɓangare na
biyu kuwa ya mayar da hankali ne kan jigo, inda aka kawo babba da ƙananan
jigogi sannan aka warware su. A rukuni na uku kuwa, an yi duba ne zuwa ga zubi
da tsarin waƙar. Ɓangare na huɗu ya mayar da hankali ne kan salo, inda aka fito
da misalan salailan da waƙar ta ƙunsa. Ɓangaren aikin na ƙarshe (5) yana ɗauke
da sakamakon nazari da sharhin da kuma kammalawa.
1.2 Manufar Nazari
Manufar
wannan takarda shi ne nazarta da kuma yin sharhi kan “Waƙar Alhakin Mumini Bisa
Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware. Takardar za ta mayar da hankali kan:
i.
Nazartar babba da ƙananan jigogin waƙar
domin fito da manufar marubucin fili.
ii.
Nazartar ire-iren salailai da mawaƙin ya
yi amfani da su domin isar da saƙonsa.
iii.
Nazartar irin harshen da mawaƙin ya yi
amfani da shi na dangane da zaɓen kalmomi da tasirin al’ada ko addini cikin
zaren tunaninsa.
1.2 Isan Kware
Ali
(Mrs), (2019) ta yi ƙoƙarin kawo Tarihin Malam Isan Kware (Autan Shehu) cikin
jaridar Leradership. An haife shi a
garin Gwandu a shekara ta 1816. Sunan mahafiyarsa Mariya. Ya kasance ɗan Auta a
wurin mahaifinsa wato Shehu Usmanu Danfodiyo. Nana Asma’u ‘Yar Shehu ita ce ta
rene shi, sannan a wurinta ne ya
hardace Alƙur’ani tun yana ɗan shekara goma a duniya. Daga nan ne kuma ya ci
gaba da karance-karancen littattafai da waƙoƙi.
Dangane
da zuwansa Kware kuwa, ya je ne lokacin da yayansa Sarkin Musulmi Muhammadu
Bello ya naɗa shi Sarkin Yamma. Wannan ya faru bayan da an ƙwace garin daga
hannun Abdussalami a shekarar 1836. Ya gudanar da mulki har na kimanin shekaru
talatin da biyar (35). Duk da cewa akwai ruwayoyi mabambanta game da haƙiƙanin
lokacin da ya rasu, Wazirin Sakkwato Alhaji Junaidu ya yi hasashen Malam Isa ya
rasu ne a wajajen shekara ta 1872. Waƙoƙin da Isan Kware ya rubuta kafin
rasuwarsa sun haɗa da:
a. Waƙar
Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara
b. Waƙar
Tuna Mutuwa
c. Waƙar
Halin Duniya
1.3 Game da “Waƙar Alhakin Mumini
Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara”
Wanda
ya rubuta wannan waƙa shi ne Isan Kware (Autan Shehu) duk da bai rubuta sunansa
cikin waƙar ba.[2]
Waƙar ‘yar tagwai ce, sannan tana da
adadin baitoci 54. Ya rubuta wannan waƙa a shekarar hijira ta 1288 wadda ta yi daidai da shekarar 1858 a shekarar
Girigori.
Ya bayyana hakan a baiti na 52 cikin waƙar inda yake cewa:
52.
Ramzi
na hijira tai Fiyayye kun jiya,
SHURAFA’UHU
haƙƙan ina bege nasa.
(Isan
Kware, WAMBMTY: 52)
Ga yadda lissafin
ya kasance:
SH – 1,000
R – 200
F – 80
H – 8
1,000
+ 200 + 80 + 8
= 1288
2.1 Jigo
Sarɓi,
(2007: 70) ya ba da ma’anar jigo da cewa: “Jigo a fagen adabi na nufin manufar
marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa,
jigo shi ne irin saƙon da marubuci ke son sadarwa ga jama’a.” Babban jigon “Waƙar
Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware shi ne gargaɗi da faɗakarwa.
Akwai
ƙananan jigogi da dama waɗanda suka taru suka ba da wannan babban jigo. Dukkannin
ƙananan jigogin na da nasaba da wannan babban jigo. Sun haɗa da:
i.
Haƙƙoƙin mumini bisa mumini
ii.
Haƙƙoƙin iyaye kan ‘ya’yansu
iii.
Haƙƙoƙin ‘ya’ya kan iyayensu
iv.
Haƙƙoƙin mata kan mazajensu
v.
Haƙƙoƙin bawa bisa ubangidansa
2.2 Jigo a Taƙaice
Sha’irin
ya yi amfani da salo mai armashi wurin jeranta saƙonnin da ke ƙunshe cikin waƙar
ba tare da an samu kwan-gaba-gwan-baya ba. Ya rattabo su cikin waƙar bi-da-bi
kamar haka:
a. Baituka
na 1 da 2 sun kasance mabuɗi ga waƙar.
b. Daga
baiti na 3 zuwa baiti na 9 an bayyana haƙƙoƙin mumini bisa mumini da suka fito
cikin hadisan Manzon Allah (SAW).
c. Daga
baiti na 10 zuwa na 14 an bayyana haƙƙoƙin maƙwabci kan maƙwabcinsa.
d. Daga
baiti na 15 zuwa na 23 an bayyana haƙƙoƙin aboki kan abokinsa.
e. A
baiti na 21 da na 23, an yi magana ne kan haƙƙin iyaye.[3]
f.
Daga baiti na 24 zuwa na 40, an bayyana haƙƙoƙin
‘ya’ya kan iyayensu.
g. Daga
baiti na 41 zuwa na 44 kuwa, an yi magana ne game da haƙƙoƙin mata kan
mazajensu.
h. A
baituka na 45 da 46 kuwa kawo haƙƙoƙin maza kan matayensu.
i.
Baituka na 47 zuwa na 50 na ɗauke da bayani
kan haƙƙoƙin bawa bisa ubangidansa.
j.
Baituka na 51 zuwa na 54 kuwa na ɗauke da rufewa.
2.3 Warwarar Jigo
Kamar
yadda aka bayyana a sama, babban manufar wannan waƙa shi ne gargaɗi
da faɗakarwa.
Wannan
ya ƙunshi jan hankali da faɗakarwa tare da tunasarwa dangane da yadda hulɗa
tsakanin jama’a ta dace ta kasance. Hakan kuwa ya haɗa da ba wa kowa haƙƙinsa
yadda ya kamata, musamman kamar yadda addini ya tanadar. A ƙoƙarin marubucin na
cim ma muradinsa (bayyana haƙƙoƙin mumini bisa mumini), ya samar da ƙananan
jigogi kamar dai yadda aka ambace su a sama. Tun daga baiti na uku Isan Kware
ya bayyana manufarsa ta rubuta wannan waƙa inda yake cewa:
3. Daɗa za ni
bayyana alhakin kau mumini,
Bisa mumini, gai sai wurin gamuwa tasa.
Yayin
da aka yi la’akari da baitin da ke sama, za a tarar da cewa mawaƙin ya bayyana
manufar waƙar tasa kai tsaye wato “bayyana alhakin … mumini bisa mumini” (Isan
Kware, WAMBMTY: Bt.: 3, Ɗg.: 1). A haƙiƙanin gaskiya, wannan ya ƙunshi dukkanin
jigogin waƙar tun daga babba har ƙananan jigogin. Dalili kuwa shi ne, duk wani
abin da ya shafi alhakin wani ko wasu rukunin jama’a bisa wasu mutane na daban,
to ya shafi zamantakewa
ne. A ɗangon waƙar na biyu ya fara lissafo ire-iren waɗannan haƙƙoƙi. Na farko
da ya kawo shi ne gaishe da mutum yayin da aka haɗu da shi.
Daga
wannan gaɓa (Bt. 3) har zuwa baiti na 8, mawaƙin ya bayyana haƙƙoƙin mumini
bisa mumini yayin zamantakewa waɗanda suka fito a cikin hadisai daban-daban.
Shi da kansa ya faɗa a baiti na 9 cewa, haƙƙoƙin da ya zayyano a waɗannan
baituka (na 3 zuwa na 8), Annabi ne ya faɗe su, wato kenan sun fito cikin
hadisai. Ya faɗi hakan inda yake cewa:
9. Daɗai ka ji an
yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
Ka tsare su Annabi
yaf faɗe su da kai nasa.
(Isan
Kware, WAMBMTY: 9)
Su
kuwa baitukan da ya bayyana waɗannan haƙƙoƙi da asalinsu ya samo daga hadisai,
sun kasance kamar haka:
4. Ka riƙai riƙon
girma ka yo fara’a da shi,
In
yak kirai ka ka zo ka karɓi kira nasa.
5. In yai
atisshewa ka zam yin godiya,
Ka
yi addu’ar rahama garai ka mayas masa.
6. Lotton da yai
ciyyo ka gai sai anka ce,
Lotton da yam mutu
duk ka zo ka biso nasa.
7. Koyaushe yai
zance ka karɓam mai walau,
Ko
ba shi nan ka tsare tutut mus’ha tasa.
8. So mai ga zucci
abin da kas so, ƙi masa,
Ga
abin da kaƙ ƙi ga zucciyakka ga rai nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 4-8)
A
baiti na 4 kamar yadda yake a sama, ya fito da biyu daga cikin haƙƙoƙin. Na
farko shi ne fara’a, na biyu kuwa amsa kira (wato dai amsa gayyata yayin da aka
yi gayyatar).[4]
A baiti na 5 kuwa, ya bayyana wani haƙƙin na daban wato amsa wa wanda ya yi
hacitawa tare da yi masa addu’a.[5] A baiti na 6 ya kawo cewa,
haƙƙin mumini ne kan mumini ya gaishe shi yayin da ba shi da lafiya.[6] Bayan haka, haƙƙinsa ne ya
je bisonsa (jana’iza) yayin da ya rasu.[7] A baiti na 8 kuwa, ya
bayyana wani haƙƙin na mumini bisa mumini wato ya so wa ɗan’uwansa abin da yake
so wa kansa, sannan ya ƙi ma ɗan’uwansa abin da yake ƙi ma kansa.[8]
Bayan
waɗannan, Isan Kware ya ci gaba da lissafo haƙƙoƙi daban-daban na mumini bisa
mumini yayin zamantakewarsu. Misali a baiti na 10 ya bayyana cewa, haƙƙi ne na
maƙwabci ya taimaka wa maƙwabcinsa ko da kuwa bai tambaya ba. Ya ce:
10. Hakana maƙwabci
an yi foro taimaka,
Ko
bai biɗa ba ka ba shi kyakkyauta masa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 10)
A
cikin baiti na 11 kuwa, ya kawo cewa lallai haƙƙi ne a gai da marar lafiya.
Wannan ciwo na iya kasancewa na jiki ko na zuciya.[9] Haka kuma a taya shi murna
yayin da wani abin farin ciki ya same shi. Ga abin da yake cewa:
Ga farin ciki ka
yi mai ka ba shi rabo nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 11)
A cikin baituka na 12 da 13 ya yi magana ne
game da cimaka wato abinci. Ga abin da yake cewa:
In ba ka ba shi rabo ka ɓoye ido nasa.
13. Ka hana ma
yara fita da shi shi gani zama,
Ba ka ba shi, ɓoye
mai da shi da ɗiya nasa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 12, 13)
Kamar
yadda yake a misalan baitukan da ke sama, haƙƙi ne kada mutum ya nuna wa maƙwabcinsa
wani abinci idan dai har ba zai ba shi ba. A baiti na 13 har yake cewa a hana
yara ma fita da shi duk dai domin kada maƙwabcin ko kuma ‘ya’yansa su gani.
A
ƙoƙarin Isan Kware na bayyana haƙƙin mumini bisa mumini cikin zamantakewa, ya
kawo maganar aboki. Ya bayyana cewa, tun a matakin farko ya kamata wanda ya
tashi neman aboki ya nemi abokin ƙwarai “mai mutumci.” Sannan kuma ya tsare
abotar tasu da gaskiya da riƙon amana, wanda ya haɗa da taya shi lamuran da
suka sha kansa. Ya bayyana hakan a baituka na 15 da 16 kamar haka:
15. Ga wajen
abutta yaf fi ƙarfi an faɗai,
Biɗi mai mutumci
yo tsaron sahuba tasa.
16. Ka riƙai da
amfani walau bai tambaya,
Ka tsare laluratai
ka zam tanyo nasa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 15, 16)
Marubucin
ya ƙara bayyana wasu haƙƙoƙin da suka haɗa da taya shi ayyukansa da na iyalansa
domin rufa masa asiri (Bt. 17), da kuma yabon sa bisa duk wani abin ƙwarai da
ya aikata (Bt. 18), sannan a riƙa yi masa uzuri a kuma ba shi haƙƙoƙinsa gaba ɗaya
(Bt. 20).
A
ci gaba da magana dangane da hulɗa da jama’a, Isan Kware ya kawo haƙƙoƙin
‘ya’ya kan iyayensu. Ya nuna cewa, matakin farko shi ne tabbatarwa da an zaɓa
musu uwaye da masu reno na ƙwarai domin yaran su taso da tarbiyya mai nagarta.
Sannan a tabbatar da an ba su ilimi mai inganci. Ya kuma ƙara da cewa, har suna
ma a zaɓa masa irin na addini. Ya bayyana hakan cikin baituka na 24 da 25 da
kuma 26 inda yake cewa:
24. Haƙƙi na ɗa ga
wajan uwaye kun jiya,
Zaɓam ma ɗa asuli
ga adddini nasa.
25. A yi mai
karatu nai a ba shi shi sha kuma,
Mai ba shi mamma
daɗa da mai yaye nasa.
26. Duka masu
addini a zaɓam mai daɗa,
Sunansa ras suna a
yanka mai bisa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 24, 25, 16)
Isan
Kware ya ci gaba da bayyana haƙƙoƙin ‘ya’ya a kan iyayensu dangane da abin da
ya shafi tarbiyyantar da su. Wannan ya haɗa da yin bisimilla kafin fara cin
abinci da kuma cin abincin da hannun dama (Bt. 27). Wani abu kuma shi ne hana
yara hulɗa da abokai da ba su da nagartar tarbiyya (Bt. 28). Sauran ɓangarorin
tarbiyya da mawaƙin ya taɓo sun haɗa da cin abin daɗi koyaushe (sagarta yaro) da sanya tufa na ƙawa da nusar
da shi game da ibada da biyayya ga na gaba da sanin ya-kamata. Ya kuma yi nuni
da a tausaya wa ‘ya’ya tare da yin amfani da dabaru wurin yi musu hani ga aikata ba daidai ba.
Daga
baiti na ishirin 41 zuwa na 44 na ɗauke da bayani kan haƙƙoƙin mace kan
mijinta. Sun haɗa da ciyarwa da shayarwa da samar da muhalli. A cikin haƙƙoƙin
ya kawo har da sadaki da kuma ilimantarwa da daidaita kwana.[10] A ɓangare guda kuwa, mawaƙin
ya lissafo wasu haƙƙoƙin maza a kan matansu da suka haɗa da yi masa biyayya da
riƙe amanarsa da kuma yi masa ado (Bt. 45 da 46).
Daga
baiti na 47, Isan Kwari ya tsunduma cikin zayyano wasu haƙƙoƙin bayi kan iyayen
gidansu. Sun haɗa da ciyar da su da tufatar
da su da musu rangwame (kada a musu tsanani) da kuma guje wa dukansu. Dangane
da haka ne ma ya nuna a baiti na 50 cewa, dukansu saɓo ne a wurin Ubangiji,
inda yake cewa:
50. Kada kai fushi
ka bugai ka saɓi Ubangiji,
Shi ad da shi nan
anka ba ka riƙo nasa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 50)
Yayin
da aka yi la’akari da saƙonnin da ke ƙunshe cikin baitukan wannan waƙa, lallai
za a tarar da cewa tana magana ne game da hulɗa da jama’a. Wannan kuwa ya shafi
musamman haƙƙoƙin da suka wajaba mutum ya lura da su yayin zamantakewa. Kamar
dai yadda aka gani cikin baitukan waƙar, haƙƙoƙin sun haɗa da na tsakanin
abokai da maƙwabta da ‘ya’ya da iyayensu da mata da miji da kuma bawa da uban
gidansa.
3.0 Zubi da Tsari
Zubi
da tsari a rubutacciyar waƙa na nufin hanyoyin da mawaƙi ke bi domin tsara
rubutun waƙarsa. Yayin da take magana dangane da zubi da tsari a waƙoƙin Mu’azu
Haɗeja, Omar, (Mrs) (2013: 39) cewa ta yi: “… hanyoyin da yake bi wajen tsara
da zuba tunaninsa.” Wanan ɓangare na aikin zai duba yadda zubi da tsarin waƙar
ta Isan Kware ta kasance.
3.1 Tsarin Baituka
“Waƙar
Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware na da adadin
baituka 54. Baya ga haka ta kasance mai zubin ƙwar biyu (wato ‘yar tagwai). Tun daga baitin waƙar na farko har na
ƙarshe (54), ba a samu taƙadarin baiti ba ta ɓangaren sauya adadin ɗangwaye.
Ma’ana kenan, duka baitukan na ɗauke da ɗangwaye biyu-biyu ne.
3.2 Mabuɗi da Marufi
Mabuɗi
da marufin waƙa sun shafi irin kalamai ko bayanan da aka yi amfani da su a
farko da kuma ƙarshen waƙa. A ra’ayin Usman, (2008: 164): “Abin da ake nufi da
mabuɗi a sharhin waƙa shi ne irin yadda marubuci ya buɗe waƙarsa wato abin da
ya fara da shi wanda ke nuna cewa farkon waƙar ke nan.” A shafi na 173 kuwa, ya
bayyana ma’anar marufi
(salon rufewa) da cewa: “A fagen rubutacciyar waƙa marufi yana nufin yada ake
rufe waƙar ko kuma abin da ke nuna alamun ƙarshen waƙa.” A wannan gaɓa, aikin
zai nazarci “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” domin duba
yadda abin ya kasance.
3.2.1 Mabuɗi
Mabuɗin
waƙa na iya kasancewa addu’a ko yabon Manzo
ko neman ƙarin ilimi da sa’a ko bayyana jigon waƙa ko dai wani abu mai kama da
wannan. Akan samu kuma waƙoƙin da suka zo da haɗakan biyu ko sama da haka na
daga cikin abubuwan da aka lissafa. A wasu lokutan kuwa, ana iya samun waƙar da
aka fara ta kai tsaye ba tare da ɗaya daga cikin waɗannan ba. A waƙar “Alhakin Mumini
Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware, an fara da yabon Ubangiji da kuma
salati ga Manzo (SAW) tare da alayensa da kuma sahabbansa a matsayin mabuɗin waƙar.
Ga yadda abin ya kasance:
1.
A
mu gode Sarki Wahidun Rahama tasa,
Ita
ta ishe mu zumai mu zam gode masa.
2.
A
mu zam salati ga Annabinmu da sallama,
Allai
Sahabbai nai da masu biya tasa.
(Isan
Kware, WAMBMTY: 1; 2)
Idan
aka yi la’akari da baitukan da ke sama, baiti na farko yana ɗauke ne da godiya
ga Ubangiji dangane da rahamarsa. Mawaƙin ya ma ƙara da kira ga al’umma da su
gode masa a ɗango na biyu (zumui
mu zan gode masa, Bt. 1, Ɗg. 2). Baiti na biyu kuwa na ɗauke da salati ne ga Manzo
da alaye da kuma sahabbansa. Haƙiƙa ba abin mamaki ba ne da aka samu waƙar ɗauke
da wannan nau’in salon buɗewa kasancewarta waƙa ce da aka rubuta ta a ƙarni na
goma sha tara. Da ma dai dukkanin waƙoƙin ƙarni na goma sha tara ba su da wani
jigo wanda ba shi da dangantaka da addinin Musulunci.
3.2.2 Marufi
Mawaƙi
na iya rufe waƙa ta hanyar godiya ga Ubangiji, ko salati ga Manzo, ko bayyana
adadin baitukan waƙar, ko bayyana shekarar da aka wallafa ta, ko kuma ya yi
amfani da biyu ko sama da haka daga cikin abubuwan da aka ambata (har ma da
makamantansu da ba a
ambata ba). Isan Kware ya rufe waƙar a cikin baituka huɗu (na 51 da 52 da 53 da
kuma 54) kamar haka:
51.
Daɗa
na cika Allah shi ba mu farin ciki,
Don Annabinmu
zumui mu zam gode masa.
52.
Ramzi
na hijira tai Fiyayye kun jiya,
SHURAFA’UHU haƙƙan
ina bege nasa.
53.
Allah
shi dawwama assalatu da sallama,
Bisa Sayyadinmu da
Sahabu har Allai nasa.
54.
Na
gode Allah wanda yat tanye ni don,
Ƙari shikai haƙƙan
ga masu yabo nasa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 51, 52, 53, 54)
Yayin
da aka lura da waɗannan baitukan kammalawa, za a tarar da cewa suna ƙunshe da
abubuwan da suka haɗa da:
i.
Roƙon Allah ya faranta musu zukata (Bt. 51)
ii.
Bayyana ramzi ko shekarar da aka wallafa waƙar (Bt.
52)
iii.
Salati ga Manzo da alaye da sahabbai (Bt.
53)
iv.
Godiya ga Ubangiji da ya taimake shi ya samu ikon yin waƙar da fatar samun
falalar yin godiya wato ƙarin wasu alherai (Bt. 54)
3.3 Amsa-Amo
“A
cikin rubutacciyar waƙa, amsa-amo sauti ne da layuka ko baitukan waƙa ke ƙarewa
da shi” (Sarɓi, 2007: 90). A cikin “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da
Tarbiyyar Yara,” Isan Kware ya yi amfani da gaɓar kalma “sa” a matsayin babban
amsa-amo. Ya fi yin amfani da kalmar “nasa” a matsayin kalmar ƙarshe na ɗangon ƙarshe
da ke kowane baiti. Duk da haka, babban amsa-amon bai kasance kalma ba domin
kuwa akwai baituka da suka ƙare da wasu kalmomin na daban, misali kalmar “masa”
a baituka na 1 da 5 da 10 da 14 da 18 da sauransu. Haka ma an yi amfani da
kalmar “tasa” kamar a baituka na 2 da 3 da sauransu. A taƙaice kenan, babban
amsa amon da aka yi amfani da shi cikin waƙar shi ne gaɓar kalma na “sa” duk
kuwa da cewa kalmar “nasa” ta fi yawa a ƙarshen baitukan. Wato a ɗaukacin waƙar ya yi amfani da doguwar ‘yar
mallaka (nasa, tasa da masa) a matsayin uwar goyon amsa-amo babba. Dangane
da ƙaramin amsa-amon waƙar kuwa, kasancewar
waƙar a zubin ‘yar tagwai ya sa ba a samu daidaiton harafi a ƙarshen layukan
farko na baitocin waƙar ba.
3.4 Gangara da Saɓi-Zarce
Wannan
wani al’amari ne da ke faruwa cikin waƙoƙi wanda yakan kasance a cikin baiti
(tsakanin ɗango da ɗango) ko kuma tsakanin baiti da baiti. Usman, (2008: 208-209) ya yi bayanin ganganra
da cewa: “A gangara ana fara zance ne ko wata manufa amma sai a ja ta zuwa ga ɗangon
da ke biye kafin a ƙarasa.” Yayin da yake bayani game da saɓi-zarce kuwa, sai
ya ce: “Saɓi-zarce kuwa gangara ce mai zurfi wadda ake fara zance a baiti amma
sai a baiti na gaba ne za a ƙarasa maganar” (shafi: 210).
3.4.1 Gangara
A
cikin “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara,” akwai wurare
daban-daban da marubucin ya yi amfani da gangara. Ga misalansu kamar haka:
1.
A
mu gode Sarki Wahidun Rahama tasa,
Ita
ta ishe mu zumai mu zam gode masa.
(Isan
Kware, WAMBMTY: 1)
A
wannan baiti na farko, za a ga yadda mawaƙin ya fara da godiyar Ubangiji (Sarki
Wahidun), inda har ya ba da ɗaya daga cikin dalilan da za a gode masa, wato
rahamarsa da ta ishe ‘yan’adam (kamar yadda mawaƙin ya ambata “… rahamar tasa
ita ta ishe mu…” Bt. 1, Ɗg. 2). Ya faro maganar rahamar ne a ɗangon farko na waƙar,
amma bai cika zancen ba sai a ɗango na biyu inda yake nuna rahamar ce ta ishe
mutane, wanda ya kamata a masa godiya bisa wannan. Isan Kware ya sake amfani da
gangara a baiti ba 3 inda yake cewa:
3. Daɗa za ni
bayyana alhakin kau mumini,
Bisa
mumini, gai sai wurin gamuwa tasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 3)
A wannan baiti da ke sama, mawaƙin ya fara
zance a ɗangon farko inda yake ƙoƙarin bayyana manufar waƙar. Ya nuna cewa ƙudurinsa
shi ne “… bayyana alhakin kau mumini… Bt. 3, Ɗg. 1.” Bai ƙarasa wannan zance
ba. A ɗango na biyu ne ya kammala shi inda yake cewa “… bisa mumini… Bt. 3, Ɗg.
2.” Yayin da aka karanta baitocin biyu ne za a fahimci manufar mawaƙin wato
“bayyana alhakin … mumini bisa mumini.” A baiti na 8 ma an samu irin wannan
inda mawaƙin ke cewa:
8. So mai ga zucci
abin da kas so, ƙi masa,
Ga
abin da kaƙ ƙi ga zucciyakka ga rai nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 8)
Abin
da Isan Kware ke son bayyanawa shi ne, mutum ya so wa ɗan’uwansa abin da yake
so wa kansa, sannan ya ƙi masa abin da yake ƙi ma kansa. Ya fara wannan batu a ɗango
na farko, amma zancen bai kammala ba sai a na biyu. Sauran misalan baitukan da
mawaƙin ya yi amfani da gangara sun haɗa da na 2 da 7 da 12 da 13 da 19 da 21
da 24 da 34 da 35 da 36 da 40 da 46 da 48.
A baiti na 14 a lura da yadda ya raba kalmar gidanai
(gidansa) zuwa gida biyu; wato ya saka farkon kalmar a ɗango na farko, amma sai
ya ɗauko ƙarshen kalmar zuwa ɗango na biyu, inda yake cewa:
14. Foron
da anka yi kar ka dubi cikin gida,
Nai
ka ji kar ka matsai ka yalwanta masa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 14)
Yana bayanin cewa, an yi horon duk mumini kada ya yi
leƙon gidan maƙwabcinsa, domin kada ya haifar da yanayin da zai kawo matsatsi
tsakaninsu har ya ji an sauya ido a harkokinsa.
3.4.2 Zaɓi-Zarce
A misalin zaɓi-zarce a lura da yadda ya ja ma’anar zance
da yake yi daga layin ƙarshe na baiti na 23, inda yake cewa:
23.
A
hana shi kwanan ana kwantawa tutut,
Bisa shimfiɗa hakana ayukkan kai nasa.
24.
Sannan
a sa shi daɗa ga addini shi bi,
Foron uwaye nai da mallammai nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 23-24)
A nufinsa yana nuni da cewa sai ‘yayan da suka bai wa
iyaye haƙƙin da Allah ya ɗora a kansu ne za su shiga aljanna. Wato duk wanda ya
saɓa wa iyaye kuma bai yi musu biyayya ba ko bai darajanta su ba, to
sakamakonsa wauta ne. Sannan iyaye ko sun ƙi ‘ya’ya idan sun yi musu biyayya to
wannan ba zai shafi ‘ya’yan da komai ba, balle ma ya ka kamata iyayen su
gafarta ma ‘ya’yan da suka ba da haƙƙin Allah.
3.5 Kari
Kari na nufin bahari ko daujiyar muryar da mawallafi ya
gina sautin waƙarsa a kai. A wannan fuskar, waƙar tana bisa zubin karin Kamil
ne inda ƙafa ta takwas ta maimaita kanta sau uku (8 + 8 + 8) tare da zihafin
Ilmari wanda ke mayar da ita ta shida a wasu wurare. Ga misalin yadda abin
yake:
v v –
v – / – –
v – / v
v – v –
A mu gode
Sarki Wahidun Rahama
tasa
v
v – v –
/ v v
– v –/–
– v –
Ita ta
ishe mu zumui
mu zan gode masa
4.0 Salo
Salo
hikima ce ko dabara ta
isar da saƙo cikin siga mai jan hankali da ƙayatarwa. Yahya, (2016: 29) ya ba
da ma’anar salo da cewa:
Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a
cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin ya isar da saƙon da yake son ya isar. Ita
wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga
mai saurare ko karatun waƙa.
Akwai
salailai daban-daban da mawaƙa
ke amfani da su cikin waƙoƙinsu. Wannan ɓangare na aikin zai nazarci “Waƙar
Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware domin fito da
ire-iren salailai da ke ciki.
4.1 Siffantawa
Sarɓi,
(2007: 172) ya bayyana ma’anar siffantawa da cewa: “Kwatantawa ce da ta shafi
daidaita tsakanin abubuwa biyu kai tsaye. Dabara ce ta jawo hankali ta hanyar ɗaukar
wani abu a ce shi ne wani abu daban.” A yayin siffantawa, ba a amfani da
kalmomi irin su “kamar” ko “sama da” ko “irin” da makamantarsu (wato saɓanin yadda lamarin yake a kamantawa). Mawaƙin
ya yi amfani da salon siffantawa a baiti na 11. A cikin baitin ya siffanta
‘taya maƙwabci murna yayin da abin farinci ya same shi’ da “rabo” (rabo nasa):
11. Gai sai da
ciyyo dud da ciyyon zucciya,
Ga
farin ciki ka yi mai ka ba shi rabo nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 11)
4.2 Alamtarwa
“Alamtarwa
wata hanya ce wadda ake bayyana wani abu ta ba shi wata alama da ta yi kama da
shi ta fuskar siffa ko yanayi ko ɗabi’a ko hali ko asali ko jarumtaka ko ƙasaita
da sauransu” (Gusau, 2011: 37). Lura da wannan ma’ana, alamtarwa na nufin
dabara ko hikimar yin amfani da kama ko siffar da wani abu ke da shi domin a
bayyana wani abu na daban a kaikaice. Isan Kware ya yi amfani da alamtarwa a baiti na 8. Ya yi hakan ne
yayin da yake nuna cewa, haƙƙi ne mumini ya so wa mumini dan’uwansa abin da ya
so wa kansa. Haka ma ya ƙi masa abin da ya ƙi ma kansa. A cikin baitin sai mawaƙin
ya yi amfani da “rai” a matsayin mutumin sukutum. Kenan dai, “rai” a cikin
baitin na wakiltar mutumin da ake batu kansa (mumini da ke da haƙƙi). Ga abin
da yake cewa:
8. So mai ga zucci
abin da kas so, ƙi masa,
Ga abin da kaƙ ƙi
ga zucciyakka ga rai nasa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 8)
Mawaƙin
ya sake amfani da salon Alamtarwa a baiti na 12. Ya nuna cewa, yayin da maƙwabci
ba zai ba da cimaka (abinci) ga maƙwabcinsa ba, to ya ɓoye masa (wato kada maƙwabcin
nasa ya gani). A maimakon Isan Kware ya ce a ɓoye masa kai tsaye, sai ya ce: “…
ka ɓoye ido nasa” (Bt. 12, Ɗg. 2). A nan ya yi amfani da “ido” domin su wakilci
shi mutumin da ake magana a kansa, wato maƙwabci.
12. In ka raba in
cimaka ta ka jiya,
In
ba ka ba shi rabo ka ɓoye ido nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 12)
4.3
Jaddadar Ƙarfafawa
Ɗangambo, (2007: 48) ya ba da ma’anar
wannan salo da cewa: “Dabara ce ta jawo hankali da ƙarfafa manufa. Akan
maimaita wasu kalmomi ko rukunin kalmomi, da sauransu, a yi musu wani irin jeri
mai ban sha’awa cike da hikima.” A baiti na 9, mawaƙin ya yi amfani da jaddadar
ƙarfafawa. Ya yi hakan ne yayin da yake ƙoƙarin nuna matsayin haƙƙoƙin mumini
bisa mumini da ya zayyano cikin baitocin waƙar (daga baiti na 3 zuwa na 8). Ga
abin da yake cewa:
9. Daɗai ka ji
an yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
Ka tsare su Annabi
yaf faɗe su da kai nasa.
A
ɗango na farko ya jaddada inda yake cewa: “… an yi ƙidansu su duka
ɗan’uwa” (Bt. 9, Ɗg. 1). A nan, ya jaddada kan dukkanin haƙƙoƙin da ya lissafo
domin dai ya ƙarfafa zancen. A ɗangon ƙarshe na baitin sai ya ƙara jaddadawa
inda yake faɗin: “Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da kai
nasa” (Bt, 9. Ɗg. 2). Bayan wannan, ya sake yin amfani da wannan salo a
baiti na 18. Ya ce:
18. Ka yabai tutut
ga abin da kas san ka sani,
Hakana
mutane nai ka zam ka faɗa masa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 15 da 16)
4.4 Jerin Sarƙen Daidaito/Bambanto
Wannan
salo yana kama da salon Jaddadawar Ƙarfafawa
domin kuwa dukansu biyu sun shafi jeranto kalmomi domin jaddada wani batu.
Yayin nuna bambancinsu, Ɗangambo, (2007: 49) ya ce: “Shi jerin sarƙe, bayan
jaddada, akan sami sarƙaƙƙiyar daidaito ko ta banbanto, wato akan sami makusanciyar
dangantaka tsakanin kalmomi iri daban-daban a baiti, wannan dangantakar tana
iya zama ta daidaito ko ta bambanto. Mawaƙin ya yi amfani da jerin sarƙen
daidaito a baiti na 33. A cikin wannan baiti ya kawo kalmomi biyu da ke da
dangantaka da juna ta fuskar daidaiton ma’ana wato “kwana” (bacci) da kuma
“kwantawa.” An dai sani cewa, a bisa al’ada akan yi bacci ne yayin da aka
kwanta. Ga abin da mawaƙin ke cewa:
33. A hana shi
kwanan ana kwantawa tutut,
Bisa shimfiɗa
hakana ayukkan kai nasa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 33)
4.5 Ƙarangiya
Gusau,
(2011: 39) ya bayyana ma’anar ƙarangiya da cewa: “Dabara ce ta luguden haruffa
ko kalmomi ko wasa da harshe cikin baƙaƙe da kalmomi a lokacin da ake ƙoƙarin
isar da wani saƙo.” Mawaƙin ya yi amfani da ƙarangiya a baiti na 29 inda ya
kawo jerin kalmomi masu ɗauke da harafin /ƙ/. Haƙiƙa furta kalmomin a jere
kamar yadda suka fito a baitin na samar da wani salo na gagara-bami. Ga abin da
yake cewa:
29. Kada ko shi
saba cin abin daɗi kaɗai,
Da tufan ƙawa
shi ƙawai ƙawa a gaya masa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 29)
4.6
Gamin Bauta
Gamin
bauta a nazarin waƙa na nufin yin amfani da kalmomi guda biyu wuri guda waɗanda
ke ɗauke da ma’anoni da suka yi hannun
riga da juna. Mawaƙin ya yi amfani da salon gamin bauta a baiti na 48. A cikin
baitin ya kawo kalmar “rage” da ke ɗaukar ma’anar sassautawa ko ɗebewa ko
ragewa da ya shafi adadi ko mizanin wani abu. Ya haɗa wannan kalma da kalmar
“tsanantawa” wadda ke ɗaukar ma’ana da kai tsaye ta yi hannun riga da kalmar ta
farko. Ga yadda abin ya kasance:
48. Mu rage
tsanantawa ga bauta kowane,
Yak
karɓi bautawa mu zam kyauta masa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 48)
4.7 Tasirin Al’adu
Ala’ada
na nufin abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya. Ta kuma
shafi rayuwar al’umma da harkokin da suke yi don zaman duniya (Ibrahim, 1982: ɗiii).
Yayin da aka nazarci waƙar “Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara,” za a
tarar da akwai tasirin addinin Musulunci kan mawaƙin. Baituka da dama suna ɗauke
da wannan tasiri na addini. Mafi yawa na abin da mawaƙin ke faɗa cikin waƙar
sun samu asali ne daga addini. Tun wurin buɗe waƙar ya fara da yabon Ubangiji
da kuma salati ga manzo da iyalan gidansa da kuma sahabbansa. A baiti na farko
ya kawo kalmomin “Sarki” da “Wahidun” da “Rahama” waɗanda ke nuni ga
tauhidinsa. Irin waɗannan kalmomin fannu da suka shafi addini sun mamaye waƙar
baki ɗaya.
A
ɓangare guda kuwa, an samu tasirin karin magana[11] a cikin waƙar ta Isan
Kware a baiti na 31. Akwai karin maganar Hausawa da ke cewa: “Hannun da ke
bayarwa shi ke a sama.” Mawaƙin kuwa sai ya ce:
31. Liddinsu anka
halatta sawa tai ku san,
Mai ba da kyauta
ya fi mai karɓa masa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 31)
4.8 Salon Samarwa da Korewa
Wannan
salo ne da ya shafi kawo bayanai da ke nuna yarda ko rashin yarda a cikin ɗangogin
baitukan waƙa. Ɗangambo, (2007: 53) ya yi ƙarin bayani dangane da wannan salo
da cewa: “Wannan ita ma dabara ce ta jan hankali wada mawallafa kan yi amfani
da ita don samun yarda daga makaranci ko mai sauraro. Cikin wanan dabara, sukan
kawo “yarda” ko “rashin yarda” wato “samarwa” da “korewa.” A wannan gaɓa za a
nazarci waƙar domin ganin ko marubucin ya yi amfani da irin wannan salo?
4.8.1
Samarwa da Korewa
Samarwa da korewa na nufin wurin da aka
samu mawaƙi ya kawo jimla ko furucin samarwa, sannan jimla ko furuci na korewa
ya biyo baya. Mawaƙin ya yi amfani da wannan salo cikin waƙarsa. Misali a baiti
na 14 yana cewa:
14. Foron da
anka yi + kar ka dubi cikin gida,
Nai ka ji kar ka
matsai ka yalwanta masa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 14)
4.8.2
Samarwa
da Samarwa
A
misalin baitin da ke ƙasa, mawaƙin ya yi amfani da haɗin samarwa da samarwa. Ga
yadda abin ya kasance:
11. Gai sai da
ciyyo + dud da ciyyon zucciya,
Ga
farin ciki ka yi mai ka ba shi rabo nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 11)
4.8.3
Korewa
da Samarwa
A
wannan wuri kuwa, mawaƙin ya kawo ɗango da ke ɗauke da korewa da samarwa. Ga
yadda abin ya kasance:
13. Ka hana ma
yara fita da shi shi gani zama,
Ba
ka ba shi,
+ ɓoye mai da shi da ɗiya nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 13)
4.8.4
Samarwa
A
baiti na 23 kuwa, za mu iya tsintar misalin ɗangon da ke ɗauke da samarwa
kawai. Ga yadda abin yake:
23. Ka shiga gidan
Aljanna ko sun tonyatai,
Shi
kam haƙiƙan sai su gafarta masa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 23)
4.8.5
Korewa
Ɗangon
waƙa na iya zuwa da furuci ko jumla mai ɗauke da korewa kawai. An samu irin
haka a baiti na 48 inda mawaƙin ke cewa:
48. Mu rage
tsanantawa ga bauta kowane,
Yak karɓi bautawa
mu zam kyauta masa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 48)
4.9
Zaɓen Kalmomi
Mawaƙin
ya yi amfani da karin harshen Sakkwatanci a baituka da yawa na cikin waƙar.
Kalmomin rukuni da ya yi amfani da su cikin waƙar sun haɗa da:
a. Zumai (Bt.1) = ‘yan uwa
b. Daɗa
(Bt. 3) = kuma
c. Lotto (Bt. 6) = lokaci
d. Tutut
(Bt. 7 da 33) = kullum
e. Biɗa
(Bt. 10) = nema
f.
Cimaka
(Bt. 12) abinci
g. Tonyatai
(Bt. 23)
h. Abutta (Bt. 15) = abokantaka
i.
Miyau (Bt. 35) = yawu
j.
Wargi (Bt. 35) = wasa
k. Amre
(Bt. 41) = aure
l.
Bananci (Bt. 43) = zamananci
m. Gyarta
(Bt. 45 da 46) = gyara
n. Tanye (Bt. 54) = taimake
Baya
ga wannan kuma, akwai kalmomin aro da Isan Kware ya yi amfani da su a cikin waƙar,
musamman daga harshen Larabci. Wasu daga cikinsu an yi musu kwaskwarima bayan
an are su. Wasu kuwa an yi amfani da su yadda suke a harshen na Larabci. Ga
misalan kalmomin aron da aka yi amfani da su:
a. Wahidun
da Rahama (Bt. 1)
b. Salati
da Alai da Sahabbai (Bt. 2)
c. Mumini
(Bt. 3)
d. Rahama
(Bt. 5)
e. Mutu
(maiti na 6)
f.
Mus’ha
(Bt. 7)
g. Biɗa
(Bt. 15)
h. Salihi
(Bt. 32)
4.10 Zubin
Jimloli
Akwai
baitukan daga cikin waƙar da ke ɗauke da ɗangwaye masu giɓin jimla. Za mu tarar
da wannan misali yayin da muka nazarci baiti na 47, inda yake cewa:
47. Bayi mu ba su
abin da muka ci dud su ci,
Da tufanmu alher(i)
na mu zam ko yi nasa.
(Isan Kware,
WAMBMTY: 48)
A
wannan misali da ke sama, mawaƙin ya yi amfani da kalmar alheri a ɗango
na biyu inda a maimakon sanya kalmar ta “alheri” sai ya yi amfani da “alher.” A
taƙaice dai ya bar giɓi a cikin jimlar.
5.1 Sakamakon Nazari
Wannan
nazari ya fahimci abubuwa kamar haka:
1. Wannan
waƙa ta Isan Kware mai suna “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar
Yara” tana ɗauke da muhimman jigogi masu magana kan “zamantakewa”. Mawaƙin ya yi matuƙar ƙoƙari
wurin bayyana haƙƙoƙin mutane a tsakanin junanansu ga matakan zamantakewa
daban-daban. Sun haɗa da haƙƙoƙin maƙwabtaka da haƙƙoƙin abota da haƙƙoƙin da
ke tsakanin iyaye da ‘ya’yansu da kuma ma’aurata
sannan da bawa da uban gidansa. Wasu daga cikin waɗannan haƙƙoƙi ya ɗauko su ne
daga hadisan manzon Allah (SAW) kamar yadda ya faɗa a baiti na 9 inda ya ce:
9. Daɗai ka ji an
yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da
kai nasa.
(Isan Kware, WAMBMTY: 9)
2. Isan
Kware ya yi amfani da salailai domin jawo hankali da kuma samun damar isar da
saƙon waƙarsa. Waɗannan salailai sun haɗa da salon Alamtarwa da siffantawa da
gamin bauta da jaddadawar ƙarfafawa da makamantansu.
3. Mawaƙin
ya yi amfani da harshe mai sauƙi wurin isar da saƙonsa duk da cewa waƙar ta ƙunshi
Sakkwatanci a wasu ɓangarorinta. Baya ga haka kuma, waƙar cike take da tsattsafin
tasirin addinin Musulunci da mawaƙin ke da shi.
5.2 Kammalawa
Haƙiƙa
“Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta amsa sunanta, domin
kuwa ta zayyano ire-iren haƙƙoƙin da suka rataya kan rukunnen mutane da ka iya tsintar
kansu cikin hulɗa da zamantakewa ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Lura da yadda waƙa ke
tasiri ga zukata da kuma sauri da sauƙin isar da saƙo, wannan aiki ya tanadi
shawarwari ta la’akari da sakamakon nazarin kamar haka: Manazarta su ƙara ƙaimi
wurin nazartar ire-iren waɗannan waƙoƙi domin fito da saƙonninsu fili, tare
kuma da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin karantar da waƙoƙin a
makarantu wanda hakan na iya tasiri matuƙa a ɓangaren gyaran tarbiyya. Wata
hanyar da ka iya taimakawa ita ce amfani da kafafen sadarwa da suka haɗa da
gidajen rediyo da talebijin da jaridu da kuma kafar intanet.
Rataye (Appendix)
Waƙar Alhakin
Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara ta Isan Kware Ɗan Shehu
(The Rights of a Believer Upon a Believer and the Upbringing of Children)
Ita ta ishe mu zumai mu zam gode masa.
2.
A
mu zam salati ga Annabinmu da sallama,
Allai Sahabbai nai da masu biya tasa.
3.
Daɗa
za ni bayyana alhakin kau mumini,
Bisa mumini, gai sai wurin gamuwa
tasa.
In yak kirai ka ka zo ka karɓi kira
nasa.
5.
In
yai atisshewa ka zam yin godiya,
Ka yi addu’ar rahama garai ka mayas
masa.
6.
Lotton
da yai ciyyo ka gai sai anka ce,
Lotton da yam mutu duk ka zo ka biso
nasa.
7.
Koyaushe
yai zance ka karɓam mai walau,
Ko ba shi nan ka tsare tutut mus’ha
tasa.
8.
So
mai ga zucci abin da kas so, ƙi masa,
Ga
abin da kaƙ ƙi ga zucciyakka ga rai nasa.
9.
Daɗai
ka ji an yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da kai
nasa.
10.
Hakana
maƙwabci an yi foro taimaka,
Ko bai biɗa ba ka ba shi kyakkyauta
masa.
11.
Gai
sai da ciyyo dud da ciyyon zucciya,
Ga farin ciki ka yi mai ka ba shi rabo
nasa.
12.
In
ka raba in cimaka ta ka jiya,
In ba ka ba shi rabo ka ɓoye ido nasa.
13.
Ka
hana ma yara fita da shi shi gani zama,
Ba
ka ba shi, ɓoye mai da shi da ɗiya nasa.
14.
Foron
da anka yi kar ka dubi cikin gida,
Nai
ka ji kar ka matsai ka yalwanta masa.
15.
Ga
wajen abutta yaf fi ƙarfi an faɗai,
Biɗi
mai mutumci yo tsaron sahuba tasa.
16.
Ka
riƙai da amfani walau bai tambaya,
Ka
tsare lalura tai ka zam tanyo nasa.
17.
Ka
yi mai ayukka nai sa’annan naka kau,
Hakana
iyali nai rufe aibi nasa.
Hakana mutane nai
ka zam ka faɗa masa.
19.
In
an yabe shi ka bar gwada mai al’amar,
Duka
mai wuya, laifi ka gafarta masa.
Balle zumu ka
tsaya ma alhukka nasa.
21.
In
ka raba fara da shi sanna uwa,
Sanna
uba shi ko ka ba shi rabo nasa.
22.
Sanna
abukkan haifuwa kuma ka jiya,
Sai
mai tsaron hakkin mahifayye nasa.
23.
Ka
shiga gidan Aljanna ko sun tonyatai,
Shi
kam haƙiƙan sai su gafarta masa.
24.
Haƙƙi
na ɗa ga wajan uwaye kun jiya,
Zaɓam
ma ɗa asuli ga adddini nasa.
25.
A
yi mai karatu nai a ba shi shi sha kuma,
Mai
ba shi mamma daɗa da mai yaye nasa.
26.
Duka
masu addini a zaɓam mai daɗa,
Sunansa
ras suna a yanka mai bisa.
27.
In
za shi ci sunnammu Bismillahi ai,
Shi
ci ko da hannun dama nan wajje nasa.
28.
A
tsare shi kar shi shigam ma yara mawargata,
Balle
fa masu ƙawa a zam ka hana masa.
29.
Kada
ko shi saba cin abin daɗi kaɗai,
Da
tufan ƙawa shi ƙawai ƙawa a gaya masa.
30.
Da
tufa na zinari azurfa alharin,
Mata
ka sa su cikin gida a tuna masa.
31.
Liddinsu
anka halatta sawa tai ku san,
Mai
ba da kyauta ya fi mai karɓa masa.
32.
Ga
wajen karatu nai kai shi ga salihi,
Salla
shi yo ta shi yo ibadadi nasa.
Bisa shimfiɗa
hakana ayukkan kai nasa.
34.
Sannan
a sa shi daɗa ga addini shi bi,
Foron
uwaye nai da mallammai nasa.
35.
A
hana shi wargi kau gaban manya da kau,
Tofin
miyau sai nesa duk a gwada masa.
36.
In
an bugai lotton karatu nai a ce,
Wayyo
na bayi na a kwankwamta masa.
37.
In
ya ƙiya sau ɗai a bar shi a hanƙure,
Lotton
da yaƙ ƙara a yo ruɗi nasa.
38.
Ɗau
anniya kai kun jiya foron uwa,
Tsoro
daɗa taka ba shi nan da uba nasa.
39.
Raba
yara in sun kai ga shekarru bakwai,
Kowa
rufa shi daban tufa ga wuri nasa.
40.
A
buge su nan lotton faɗin salla akul,
Sun
kai ga goma da ukku nan ga faɗi nasa.
41.
Koway
yi amren macce haƙƙan ci da shi,
Da
wurin shiga duka an aza su ga kai nasa.
42.
Bisa
ya cika mata alhakinta da shar’u duk,
Shi
as sadaki wanda anka azama masa.
43.
An
kai ta nan aka son walima tai shi yo,
Mata
nan bananci dud da ko murna tasa.
44.
Shi
sanad da mata nai sanin addin shi kau,
Daidaita
kwanakki shi gyarta gida nasa.
45.
Daidaita
kwana mustahabbi na, ta zam,
Jin
ko batu nai duk ta zam gyarta masa.
46.
Ta
tsare daɗa ajiyad da yay yi ta sa ƙawa,
Ga
jikinta dud da tufanta don girma nasa.
Da tufanmu alher
na mu zam ko yi nasa.
Yak karɓi bautawa
mu zam kyauta masa.
49.
Daɗa
wanda yaƙ ƙi mu bar bugu nai kun jiya,
Rabuwa
da shi das sannu ya fi bugu nasa.
50.
Kada
kai fushi ka bugai ka saɓi Ubangiji,
Shi
ad da shi nan anka ba ka riƙo nasa.
Don Annabinmu
zumui mu zam gode masa.
52. Ramzi na hijira
tai Fiyayye kun jiya,
SHURAFA’UHU haƙƙan
ina bege nasa.
53. Allah shi dawwama
assalatu da sallama,
Bisa Sayyadinmu da
Sahabu har Allai nasa.
54. Na gode Allah
wanda yat tanye ni don,
Ƙari shikai haƙƙan
ga masu yabo nasa.
[1]
Ana ba da ma’anar waƙa ne ta fuskoki guda uku wato: (i)
Ma’ana ta gaba ɗaya ko (ii) Ma’anar rubutacciyar waƙa ko kuma (iii) Ma’anar waƙar baka (Idris, 2019).
[3] Idan aka lura za a fahimci cewa,
baituka na 21 da 22 da kuma 23 na ɗauke da batun haƙƙin iyayen kan ‘ya’yansu da kuma haƙƙin aboki kan aboki.
[4] Manzon Allah (SAW) ya ambaci haka
cikin hadisin Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) mai lamba 2162 a cikin
Sahihul Muslim.
[5] Abin da addini ya koyar shi ne,
wanda ya yi hacitawa zai ce: “Alhamdulilla” (Godiya ta tabbata ga Allah). Amsa
masa haƙƙi ne inda
za a ce: “Yarhamakalla” (Allah ya maka rahama). Wannan batu ya zo a cikin
hadisin Abu Huraira (Allah ya yarda da shi). Hadisi ne mai lamba 5870 a cikin Sahihul
Bukari.
[6] Wannan batu na cikin Hadisin Abu
Huraira (Allah ya yarda da shi). Hadisi ne mai lamba 12 a cikin Sahihul Muslim.
[7] Abu Huraira (Allah ya yarda da
shi), shi ne ya rawaito wannan hadisi. Ya zo a cikin Sahihul Buhari mujalladi
na ɗaya, lamba na 81).
[8] Wannan hadisi ne sananne wanda aka
karɓo daga Baban Hamzata (Allah ya
yarda da shi). Hadisin na zo cikin Sahihul Buhari. Yana da lamba 13.
[9] Masana Hausa musamman al’ada sun
kasa cuta ta hanyar la’akari da abubuwa daban-daban. Daga cikin rabe-raben
akwai abin da ya shafi cutukan jiki (waɗanda suka kasance bayyanannu) da
kuma cutukan zuciya (waɗanda suka kasance ɓoyayyu) (Gobir, 2012: 165).
[10] Ana samun maganar daidaita kwana
ne yayin da namiji ya kasance ba mata guda yake aure ba. A irin wannan lokaci,
daidaita yawan kwanaki da yake yi a ɗakin kowacce, abu ne da addini ya
nuna a kula da shi. Wannan ne kuma mawaƙin
yake magana a kai.
[11] Gulbi, (2014: 8) ya bayyana
ma’anar karin magana da cewa: “Wani zance ne da akan shirya cikin hikima da naƙaltar harshe wanda kan zo da sigar
taƙaita zance.”