Bahaushe na cewa: “Idan ka ji wane ba banza ba!” Duk da cewa ‘yan waɗandan baitoci sun kasance ɗaukani ne kawai game da rayuwar ALA, hakan bai hana su zama wani madubi ba wanda daga cikinsa ana iya hango hoton rayuwarsa a dunƙule. Basirar da Ubangiji ya huwace masa kuwa, tuni ya duƙufa wurin sarrafa ta. Ruwan alƙalaminsa bai daina zuba ba, haka ma ƙararrawar bakinsa ba ta daina kaɗawa ba. A bisa haka ne wannan takarda ke ba da shawarar cewa, a samu wani yunƙuri na musamman domin gudanar da nazarce-nazarce (bayan waɗanda ake yi a makarantu) dangane da waƙoƙin ALA. Hakan zai ba da damar cin gajiyar hikimomin da ke ƙunshe cikinsu, da kuma adana waƙoƙin domin ‘yan gobe.
Allah wanda shi ke raba dace,
A yau niyyata na tsaftace,
A nan wurinka naf fake neman dace.
Mai sama ilimi
baiwarka ce,
Mutum yakan yi
hankali ko haukace,
Mai duka ji ma
niyyarka ce,
Muddin ka so to
sai a kurumce.
Ilahu mai gani duk
kai ka amince,
Idan ko ka ga dama
sai ya makance,
Ilahu ko ɗanɗano sai ka amince,
Idan a yau ka so
komai ya sallace.
Na aminta arziki bayarwarka
ce,
Na sani kai kake
sa a talauce,
Nittsuwa da
fikkira baiwarka ce,
Nufinka ne ɗan Adam yag
gal-galce.
Ubangiji sallu ala
wanda yai fice,
Uban Alƙasim da kaa
amince,
Umumi[1]
ahlih was sahabi jimlace,
Ubangiji da duk
mabbiyansu jimlace.
Labari gare ni
wanda na tantance,
Labadiya[2]
a dena a zo a ji zance,
Lallebiyo[3]
tsayar taho a urince[4]
Lafshaka[5]
ku samu ku bi shi nitsance.
Alƙalam na ɗauka niyya na
tsaftace,
A yau tarihi ne
zan yi jerance,
A kan rayuwar
fasihi da yai fice,
A gaskiya, ilmi da
ma a mutunce.
Da farko Talata
ran biyu ga wata ce,
Da ɗai goma ga watan nineteen ce,
Daɗo seventy-three haɗa su jimlace,
Da ɗai haihuwar Ala
kun ji kammalce.
A Yakasai
haihuwarsa ta kasance,
A Kanon Dabo
babban birni fitacce,
Allo a rubuta tsaf
a hardace,
A ƙarƙashin Malam Tudu
yai fice.
Nan Tudu na
Murtala Primary ce,
Nineteen eighty-six ya kasance,
Nineteen ninety-two ya kammalce,
Nan Kano Dakata Secondary ce.
A nineteen eighty-six
ya zarce,
A Dakata ninety-two ya kammalce,
A two thousand three zo ka ji zance,
A School of Technology ya kasance.
Birnin Kanon Dabo
can ya kasance,
Bakin twenty-seven ya kammalce,
Ɓangaren design nan ya gwanance,
Bayan ɗimbin
karance-karance.
Ubangiji yai masa
baiwa ta fice,
Ubangiji ya azurta
shi da dace,
Ussi[6]ko
domin shi ya kasance,
Ubangiji ya kama
dare da maraice.
Batu na aure kuwa
tuni ya cikkace,
Baiwar ‘ya’ya
garai ya azurce,
Banuna wal banatun
akwai su jimlace,
Bagire na ilmi
sunka kasance.
Ala a waƙa tuni ya yi fice,
A nahiya ta Hausa
ba a kwatance,
A jamo’o’in ƙasa ana ta
bincike,
Ayyukansa libraries sun kundance.
Karamci, mutunci,
zuci tsaftace,
Kamili, fasihi,
gwani da yai fice,
Karsashi, kamala
ga manyance,
Kana da kyan hali
kawai a taƙaice.
Ai masu gulma
kanka sun kunyance,
A yau masu
hassadarka sun layince,
Af! Masu ƙin ka duk sun lamunce,
A ƙarshe masu ƙorafi sun amince.
Rabbi duniya Ala
ya buga dace,
Rabbana a lahira
ka sanya ya dace,
Rattabin
Abu-Ubaida ɗan Sani ce,
Ramzi MATISHA take
a ƙidance.
[1] Wannan kalmar tana da ma’anar: “Gaba
ɗaya”, ko “haɗuwar ra’ayi.”
[2] Wannan Kalmar tana da ma’anar
yawon banza.
[3] Wannan kalmar tana da ma’anar wata
wasa da yara suke yi a ruwa. A wasu wurare akan kira wasan da laɓi ko lebi ko a-kori-kada kokuma labis.
[4] Wannan kalmar tana da ma’anar
azalzala ko ƙagauta.
[5] Wannan kalmar tana da ma’anar:
“inuwa mai sanyi.”
[6] Kalma ce wadda take daidai da
kalmar “dalili.”
author/Sani, A-U.
journal/Peompdf-https://youtu.be/bHVaNFCfQuI
paper-https://youtu.be/bHVaNFCfQuI