Bahaushe na cewa: “Idan ka ji wane ba banza ba!” Duk da cewa ‘yan waɗannan baitoci sun kasance ɗaukani ne kawai game da rayuwar ALA, hakan bai hana su zama wani madubi ba wanda daga cikinsa ana iya hango hoton rayuwarsa a dunƙule. Basirar da Ubangiji ya huwace masa kuwa, tuni ya duƙufa wurin sarrafa ta. Ruwan alƙalaminsa bai daina zuba ba, haka ma ƙararrawar bakinsa ba ta daina kaɗawa ba. A bisa haka ne wannan takarda ke ba da shawarar cewa, a samu wani yunƙuri na musamman domin gudanar da nazarce-nazarce (bayan waɗanda ake yi a makarantu) dangane da waƙoƙin ALA. Hakan zai ba da damar cin gajiyar hikimomin da ke ƙunshe cikinsu, da kuma adana waƙoƙin domin ‘yan gobe.
author/Sani, A-U.
journal/Peompdf-https://youtu.be/bHVaNFCfQuI
paper-https://youtu.be/bHVaNFCfQuI