Tsokaci: Wai “kowa da abin da ya dame
shi!” inji maƙwabcin mai akuya yayin da ya sayi kura. ‘Yan’adam na abota/ƙawance
ko soyayya. Yawanci ana gina wulɗayyar da wasu tubalai na musamman. Daga
cikinsu akwai sha’awa da dukiya da ilimi da mutunci da fice ko ɗaukaka da hali ko
ɗabi’a. Waɗannan kuwa su ke zaman ginshiƙan da ke tallafe da shigifar hulɗayyar.
Yayin da aka samu gazawar ginshiƙan, sai dai a ce “Allah ya kiyaye!” Zuciyata
ma na da irin nata muradi. Tana da wani abu na musamman da ke burge ta. Yayin da
mace ta mallaki wannan abu, lallai ta zama “macen da take burge ni!”
WACCE TAKE BURGE NI
Ba sai tana da
siffa na burge ‘yan maza ba,
Ban damu ‘yar
firat ce koko duma-duma ba,
Ba sai tsawonta
daidai abin ake yabo ba,
Ban
damu ko fara ce koko baƙa wulik ba.
Ban damu ko da
siffa na kanta ya yake ba,
Ban damu sai da
gashi ko da ko talkobo ba,
Ban damu ko
goshinta ya shigga off site ba,
Ban damu ko
ƙeyarta ta wucce boundry ba,
Ban
damu ko fuska tana da kyan gani ba.
Ban duba
kunnuwanta in sun kyawun gani ba,
Ban duba ko
idonta fari koko da ja ba,
Ba wai tsawo na
hanci koko in ya daɓe ba,
Ba wai siffa ta
baki da anka yo mata ba,
Ba
ko tsarin haƙora da ac cikin baki ba.
Ban damu in a
miƙe ko danƙare wuya ba,
Ban damu
kafaɗunta salonsu ya yake ba,
Ban damu
hannuwanta nau’insu ko siffa ba,
Ban damu ko da
cindo ƙida na yatsukan ba,
Ban
damu in faratanta na da kyan gani ba.
Ban damu ko
kamannun cikinta ya yake ba,
Ban damu
kunkuminta ko yai zubin diri ba,
Ban damu in
ƙafafunta sun yi kyan gani ba,
Ban ce ko babu
kyawu ko ba ni so na kyau ba,
Amma
a zuciyata ba shi yake mulki ba.
Ba sai tana da
nera tuli a bankuna ba,
Ba sai tana
albashi abin a zo gani ba,
Bai sai tana
sana’a na burge al’uma ba,
Ba sai a
kasuwanci jarinta ya ɗaga ba,
Kuɗi
da arzikinta ba su nake gani ba.
Ba wacce
kaddarori a nan ta yo fice ba,
Ba sai tana da
mota koko gidan shiga ba,
Ba sai tana da
fili da ko dabbobin kiyo ba,
Ban musa kyansa
sam-sam biɗa da yin na kai ba,
Sai
dai a zuciyata ba shi nake gani ba.
Ba sai gidan
sarauta da ke da ɗaukaka ba,
Ba sai gidan
tajirci da sunka yo fice ba,
Ba ‘yar gidan
siyasa da ke a gwamnati ba,
Ba wai gidan
malunta tushe na illimi ba,
Ban
damu da giddansun ba itta zan yi duba.
Duk waɗanda ba
su ko ni nake hari ba,
Macen da ni nake
so ba zan ƙi ambata ba,
MAI HALIN ƘWARAI
wacee ba ta zamba,
Ba wacce
gaskiyarta sai dai a yo sha’an ba,
Ba
wadda ke da halin gani na duniya ba.
Ba wacce ba ta
kunyar ta yo abin faɗi ba,
Ba wacce ba
kawaici gare ta ko kaɗan ba,
Ba wacce ba ta
tsoron ta yo abin gayi ba,
Ba macce mai
gadara mai nuna tutiya ba,
Ba
wacce ke ganin ta fi ai mata hani ba.
Ba wacce ke da
ƙyashi ko nuna hassada ba,
Ba wacce ke da
gulma ko son a yo mata ba,
Ba wacce ke da
ƙeta ga ɗan da ba nata ba,
Ba wacce ba ta
buri na taimakon umma ba,
Ba
wacce rayuwarta bai zam abin gwadi ba.
Ba wacce
tarbiyarta bai wucce fafaki ba,
Ba wacce ko
iyaye ke yin Allah wadai ba,
Ba wacce sai an
ce yi, koko a ce bari ba,
Ba wacce in an
yi hani take maiman kure ba,
Ban
son macen da ba ta san shiru da maggana ba.
Ba mai yawan
surutun da babu kan gado ba,
Ba wacce bat ta
san lokacin a yo kaza ba,
Ba wacce ke da
ganda ba koko son jiki ba,
Ba wacce bat ta
damu ta yo ƙwazon fice ba,
Ba
mai yawan ƙawaye na ɓata lokaci ba.
Ba mai biye
ƙawaye wajen sharholiya ba,
Ba mai ɗaukar
zuga gun waɗansu ‘yan’adam ba,
Ba mai ganin
waɗai ba da so na kwaikwayo ba,
Ba wacce ke da
son wai a san tana da shi ba,
Ba
wacce ke gani don ta zo ta kwaikwaya ba.
Ba wacce ba ta
nazari da yin tuntuntuni ba,
Ba wacce ba ta
tsarin salo na rayuwa ba,
Ba wacce duk
tunaninta bai wuce na yau ba,
Ba wacce ba
azanci a kanta ko kaɗan ba.
Ba
bogaza ba sannan ba mubazzara ba.
Ba wacce ke da
son kai da so na zuciya ba,
Ba wacce ke da
son rai da so na rayuwa ba,
Ba wacce ke da
buri na hole duniya ba,
Ba wacce ke da
cacar kuɗi da dukiya ba,
Ba
wacce tattali bai gane ta ko hanya ba.
Ba wacce ke faɗa
kan ƙarya da so na rai ba,
Ba wacce ke
biris da shure gaskiya ba,
Abin da duk
daidai ne bai saɓa ƙa’ida ba,
Idan yawa gare
shi yawan bai yo yawa ba,
Idan
kaɗan ake so, bai zamto ɗan ɗiris ba.
Ba wai ina zuba
ne kawai a don waƙa ba,
Ban yo zancen
daɗai don in tara baituka ba,
Tabbas ar
ra’ayina ban ƙara gisshiri ba,
Ban so abin wuya
ba da ke wuyar samu,
Hali
kaɗai nake so, ba zan ƙi ai daɗi ba.
Ina ta kan batu
af! Ban sanya basmala ba,
Astagfirullah
Allah ka sa ban sau hanya ba,
Ka gyara
zuciyata ka sa ba zan taɓe ba,
Da ni da duk
salihhai ba mu so so na kai ba,
Shigar
da mu aljanna Ilahu, Jalla, Rabba!
Daɗo dubban
salati da bai wu aƙ ƙida ba,
Ga Manzo
Al-aminu da bak ka yo ya shi ba,
Da alaye sahabu
dukansu ban rabe ba,
Ka sa a ran
ƙiyama da su ba ma rabe ba,
Tamat!
Abu-Ubaida ban girmi kuskure ba.