Waƙar da aka shirya
domin shiga gasar waƙa ta Hausa Music Institute wanda za a gabatar
yayin bukin ƙungiyar Dangin Juna Masoya Ala Foundation a
Katsina, ranar Lahadi 23-6-2019.
Shaye-Shaye:
Mafari, Illoli da Mafita a Taƙaice
Ta
Abu-Ubaida
SANI
1. Alhamdullilla kai kaɗai ke ba da sa’a,
A kullum na ja
zaren bai ce a’a,
Allah yi salati ga
mai jan jama’a,
Ahlihi, sahabu duk
da ke masa ɗa’a.
2. Duniya mai yayi mai al’adu,
Dubi masu kyau,
dubi ko na Yahudu,
Duk ciki
shaye-shaye ni ke wa gudu,
Dunkurki ka aikin
ga sai mai fasadu.
3. Nau’o’in shaye-shaye sun fi ƙidana,
Na san na ƙwaya manya da ƙanƙana,
Na ga na busawa
idan aka ƙona,
Na ji ana shan sirob,
babbar magana!
4. Ranar da anka riƙa har allura,
Rayi bai nutsuwa sai an ɗura,
Raba ni kai! Har shaƙa ake na lura,
Raɓe-raɓe can kango domin
lalura.
5. Shi shaye-shaye a zam gane shi,
Shina nufin duk
abin da in an sha shi-
Shike sanya maye
jiki ya yi yaushi,
Shiru-shiru ko
surutun ban haushi.
6. Mafarin shaye-shaye akwai haɗama,
Masu son aiki tuli
wai su gama,
Mahaya na biyu,
manema rigima,
Matasa da kan fita
“taho mu gama.”
7. Sai kuma yara da ba a kula su sosai,
Saimomi anka mai
da su kamar masai,
Sai fa wanda shi
abokai suka kwasai,
Sai majinyaci da
ke son jin sa wasai.
8. Matsalolin shaye-shaye suna da dama,
Mai yi a ƙarshe sai ya yi
nadama,
Mashayi da lafiyarsa zai yi ta fama,
Mutane
ba su ganin mashayi da ƙima.
9. Ba ya iya ajiyar kuɗi ko kadara ba,
Ba zai haifi
‘ya’ya masu lafiya ba,
Ba zai ko samu yardar Ubangiji ba,
Ba
dole ne ya zulle homar hukuma ba.
10. Ya ne za a tsai da safarar ƙwaya,
Yaɗuwa da shan su yara da manya,
Yara sai mu tashi mui tarbiyya,
Yawo, abokai, mu rinƙa tankiya.
11. Wanda duk ka so ga ice yai tanƙwarawa,
Walla tun yana ɗanye yake farawa,
Walwalar ɗiya duk zamo
dubawa,
Wurin
biɗar illimi su zam
dogewa.
12. Mu lura sai hukuma ta zan ta damu,
Mutum da anka kama ya san ya kamu,
Mu jama’a dukanmu sai mun fa gamu,
Mu
ɗauki jinka gyaran
halayenmu.
13. Ya Allah mun tuba ka ba mu lafiya,
Ya Ubangiji ba mu arziki da kariya,
Ya Mai Iko, hana mana ƙwaya da giya,
Yara
da manya mu guje su bai ɗaya.
14. Naku ne Abu-Ubaida mai ƙin ɓarna,
Na rubuta MATISHA ƙidan ramzina,
Na ƙidaya baitukan sha
huɗu dai na,
Na bar ku lafiya sai wata rana.