Adashen Ƙauna 6: Kwalliyar Salla (Yarinya 'Yar Ɗagwas)



    Kamar yadda masana suke bayani, waƙa ko waƙe na bijiro wa marubuci ko mawaƙi a sakamakon dalilai masu yawa. Ko da sha’iri bai yi niyya ba, yayin da wani lamari na musamman ya yi tsinkaye zuwa cikin zuciyarsa, ƙwaƙwalwarsa ko birnin tunaninsa, ba zai san lokacin da fafutukar tunaninsa na zayyana siffa, yanayi, tsari ko surar abin zai kai shi ga rattabo luguden jeranton kalmomi ba. A irin wannan lokaci, yakan yi hakan cikin salo da siga na musamman. Maganganun kan ɗauki rauji da zubi da tsare su kuma ƙunshi salailai, wani lokaci ma har da ƙafiya. Da zarar haka ta faru, to waƙa ta haɗu. Me kuma zan ce…?



     Adashen Ƙauna 6: Kwalliyar Salla (Yarinya 'Yar Ɗagwas)

    Abu-Ubaida Sani


    1. Na gode Sarki guda,
    Da ya ban ɗiya ‘yar ɗagwas.

    2. Humaira ce A’isha,
    Ash’ab koko ‘yar ɗagwas.

    3. Humaira kin shero ni yau,
    Kwalliyarki ta yo ɗagwas.

    4. Kallonki na jirkice,
    Tamkar na faɗo a ƙas.

    5. Wankanki ya yo ƙaƙal,
    Suturarki ko sun yi fes.

    6. Da gaske kin cancare,
    Tabbas ko kin yo ɗagwas.

    7. Fiskarki ta yo bajau,
    Kwalliyarki ta yo ɗaɗas.

    8. Murmushin da kin kai ga ni,
    Haƙoranki sun yo fefes.

    9. Sun hau sahu ne kuwa,
    Na gan su sun jeru ras.

    10. Takunki ya tai da ni,
    Siffarsa ce ƙwas-da-ƙwas.

    11. Bar su o’i ‘yan hassada,
    Tafiyarsu tinƙis-tiƙis.

    12. Gashinka ya lailaye,
    Laushisa ya yo liƙis.

    13. Tsayinsa ya yo zuwat,
    Na su o’i tamkar talas.

    14. Ban gajiya da kallonki ni,
    Sai ma in kai kwana kas.

    15. Mata duk sun yo ado,
    Da ganin ki sun yo lakwas.

    16. Kin wuce su kin yo gaba,
    Kin bar su can baya ƙas.

    17. Kowa kwatancensa ke,
    Su ke ta yin ƙus-da-ƙus.

    18. Na ji suna roƙo ga ke,
    Domin su zo sui yi kwas.

    19. Maƙiyanki sun sha ƙasa,
    Dukkansu sun sha ƙwamas.

    20. Duk jikinsu ba walwala,
    Tamkar fa sun sha lalas.

    21. Mai gulmar ki lallai gani,
    Aish tabbas fa zai sha kiɓis.


    22. Zai sha afi yai jiɓi,
    Har sai jiki yai lilis.

    23. Sona da ni naki ne,
    Wata in ban da ke ta yi miss.

    24. Jiki har zuci duk naki ne,
    Ke ce na zaɓa kalas.

    25. Kin mallaken A’isha,
    Bara dai ya zamto halas.

    26. Zance na so sai da ke,
    Ga watarki ba shi murus.

    27. Abu ga Ubaidanki ne,
    Bihamdillah ƙurun ƙus.

    Pages