Zamantakewar Hausawa Jiya Da Yau
Na
Musa SHEHU
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato
0703 131 9454
Da
Abu-Ubaida
SANI
Department of Languages
and Cultures
Federal University
Gusau, Zamfara
Phone No: 08133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com
Tsakure
Hausawa kan ce wanda ya tuna bara bai ji daɗin bana ba. Haƙiƙa zamantakewar Hausawa a da ta kasance gwanin ban sha’awa. A da, Hausawa sun kasance suna zama ne na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Wannan ne ma ya sanya tsarin muhallin Bahaushe a da bai kasance ramin-kura ba, daga ke sai ‘ya’yanki. A maimakon haka, yakan zauna ne a gida na gandu. Hausawa kan ci abinci tare, su yi aiyuka da tarurruka a tare, da ma dukkan sauran al’amuran yau da kullum. Hakan ya sa duk wanda ya shiga matsala, abin yakan zo da sauƙi domin kuwa ‘yan uwa da abokai da sauran makusanta za su tsaya tsayin daka su ga an shawo kan matsalar. Abin sai dai a ce Allah san barka. Kash! Sannu a hankali an wayi gari wannan tsarin zamantakewa na dusashewa. Tausayin juna da taimakon juna da zumunci da zaman lafiya duk sun ja baya. Son kai da hasada da gaba sun fara maye gurbin zaman lumana da taimakekeniya da aka san Bahaushe da su a da. Wannan takarda tana ɗauke da bitar irin kyakkyawar tsarin zamantakewar Bahaushe ta asali da kuma yadda zamantakewar ke taɓarɓarewa a yau. Sannan daga ƙarshe takardar ta kawo hanyoyin da za su iya taimakawa wajen ɗinke waɗannan ɓaraka da ake samu.
1.0 Gabatarwa
Zamantakewa
a kowace irin al’umma gona ce mai faɗin gaske, sai dai a yau ana iya
cewa, haki na ƙoƙarin yi
mata barazana na hana yabanya walwala. Haƙiƙa
al’ummar Hausawa sun kasance masu kyakkyawar zamantakewa a tsakanin junansu.
Gaskiya da riƙon amana da shi suke kwana suke tashi. Haƙuri
da taimakon juna ya zama musu ruwan sha a ji sanyin rayuwa. Biyayya ga magabata
da tausaya wa talakawa ga shugabanni ya zama ruwan dare game duniya. Sai dai
kuma wannan kyakkyawar zama yana neman taɓarɓarewa a
wannan zamani. Saboda haka, manufar da wannan maƙala ita
ce, fito da tsarin zamantakewar Hausawa a jiya, da kuma yadda zamantakewar ke ƙoƙarin
sukurkucewa a yau. Taɓarɓarewar
zamantakewar na da nasaba da rashin gaskiya da riƙon amana
da kuma kwaikwayon baƙin al’adu musamman
daga finafinai (Al-kanawy, 2000; Ali, 2004; Kiyawa, 2013). A yau, taimakon juna
da biyayya ga magabata, da tausaya wa talakawa daga shugabanni, da haƙuri
da juna yana neman ya zama tarihi. Ga dai al’amurran nan suna ƙoƙarin
taɓarɓarewa a
rayuwar Hausawa a yau.
2.0 Yanayin Zamantakewar Hausawa a Jiya
Tarihi ya nuna al’umma takan kafu ne
a sakamakon wata yarjejeniya tsakanin wasu mutane waɗanda suka
taru suka amince da kare kansu daga wasu abubuwan ban tsoro, ko hare-haren
abokan gaba, ko namun daji, ko kuma su sauƙaƙa
wa kansu wasu wahalolin duniya (Mar, a cikin Gusau 1999). Irin wannan zama na
yarjejeniya yakan kawo sahihin haɗin kai da yarda da juna, sannan da
taimakon juna. A irin wannan yarjejeniyar zama aka sami wasu mutane daga ƙabilu
daban-daban suka haɗa ƙarfi suka
samar da al’ummar Hausawa, masu ma’amala da harshe ɗaya wato
harshen Hausa, tare da samun daidatuwa ta wajen fannin ɗabi’unsu
da al’adunsu da muhallinsu da sauran kayayyakin ayyukansu duk sun zama fanni ɗaya
(Gusau, 1999).
Hausawa tun farko mutane ne da suka
tashi da taimako da son juna, da ladabi da biyayya, da tsare gaskiya da riƙon
amana, da aikata ɗa’a da
tsare haƙƙin shugabanci da maƙwabtaka da
sadar da zumunci, da tausayi da sanin ya kamata, da sauran ayyukan alheri iri
daban-daban. Kuma su mutane ne masu matuƙar karimci
da saurin amincewa da wasu mutane, wato baƙi. Sannan
ga sakin fuska da shimfiɗar fuska wadda ake cewa ta fi
shimfiɗar
tabarma. Mutane ne masu kyakkyawan zamantakewa tsakaninsu da ma sauran baƙi
masu shigowa (Bunza, 2012; Maikadara, 2012). Duk da yake cewa, mun san akwai
wasu halaye da ɗabi’u
munana da ake aikatawa tun wancan lokaci na farkon rayuwar Hausawa, domin
Hausawa na cewa, mutum duka ɗan tara ne bai cika goma ba. A kan haka, za a iya kallon zamantakewar
Hausawa zuwa waɗannan
rukunnai:
2.1 Zamantakewa Tsakanin Maƙwabta
Gusau (1999) ya bayyana cewa, maƙwabtaka
ita ce zama wuri guda da mutum dangane da sana’a ko wurin zama. Ba shakka,
akwai kyakkyawan zama da ƙaunar juna
tsakanin maƙwabci da maƙwabci.
Idan wani abin farin ciki ya sami maƙwabci
kamar harkar aure ko suna, yakan shaida wa maƙwabcinsa
don a taru a yi murna. Haka zalika, idan abin baƙin ciki ne
ya samu akan haɗu a
jajanta wa juna. Sukan kuma taimaka wa junansu idan wata hidima ta samu domin a
rufa wa juna asiri. Maƙwabcin Bahaushe
tamkar ɗan’uwansa
ne, ya san samu ko rashin maƙwabcinsa.
Haka ma ya san farin ciki ko baƙin cikin
maƙwabcinsa. Bugu da ƙari,
zamantakewar ba ta tsaya a nan ba, galibi idan dare ya yi magidanta sun dawo
gida, maƙwabta sukan fito da abincin dare daga
gidajensu a zauna a ci tare ana tattauna lamurran da suka shafi rayuwar duniya.
Ziyarar mara lafiya, da zuwa jaje ga wanda wani abu na baƙin ciki ya
sama, da saƙonnin taya murna, duk Hausawa na gudanar
da su ga maƙwabtansu na jini da na zaman unguwa ko
gari ko sana’a, saboda ba da haƙuri da
nuna tausayawa da taya murna. Idan wani rikici ya ɓarke
tsakanin maƙwabta, akan haɗu a
tattauna a yi sulhu don samun masalaha.
Irin
wannan kyakkyawar zamantakewa da aka zayyana a sama ita ta sanya aka samu karin
maganganun Hausawa daɗanda ke nuni game da zamantakewa ta gari.
Sun haɗa da:
i.
Mahaƙurci
mawadaci
ii.
Haƙuri shi ne
ribar rayuwa
iii.
Idan da hali muni kyawo ne
iv.
Alheri danƙo ne ba ya
faɗuwa ƙasa
banza
v.
Maci amana yana tare da kunya
vi.
Ɗa na kowa
ne
vii.
Zaman duniya cuɗeni in cuɗe ka
viii.
Zaman duniya kamar rumbu ne miƙo
man in miƙo maka (Ɗanyaya,
2007; Koko, 2011, Malumfashi da Nahuɗe, 2014).
2.2 Zamantakewa Tsakanin ‘Yan’uwa
Zamantakewa
tsakanin ‘yan’uwa na jini kamar ta maƙwabci da
maƙwabci ce. Babu nuna bambanci tsakanin
‘yan’uba. Iyaye mata ko kishiyoyi ba sa nuna bambanci tsakanin ‘ya’yansu. A
wani lokaci ma yaro bai gane mahaifiyarsa sai idan ya girma. ‘Yan’uwa kan
yawaita sadar da zumunci tsakaninsu ta hanyar ziyartar juna daga lokaci zuwa
lokaci. Kamar maƙwabta, su ma ‘ya’uwa kan taru domin taya
juna murna ko farin ciki idan wani buki ya samu. ‘Yan’uwa kan yi iya ƙoƙarinsu
don ganin ɗan’uwa bai
ji kunya ba. Babu yaudara ko cin amana tsakanin ‘yan’uwa. Idan iyayen yara suka
rasu, ‘yan’uwa kan ɗauke su suna kulawa da su tamkar su suka
haife su ta yadda rayuwarsu za ta inganta ba tare da sun tagayyara ba. Idan
wata rashin lafiya ta sami ɗan’uwa, babu maganar ƙyama,
‘yan’uwansa na kusa da ma na nesa kowa yakan kawo tasa gudummuwa domin ganin
wannan ɗan’uwa ya
sami cikakkiyar lafiya (Gumel, 1999; Maikada, 2012).
2.3 Zamantakewa Tsakanin Masu Mulki da
Talakawa
Haƙiƙa
akwai kyakkyawar zamantakewa ta fahimtar juna a tsakanin masu mulki ko sarakuna
da talakawansu. Abin da aka sani tun can azal a rayuwar Hausawa, sarki ko
shugaba mutum ne wanda a koyaushe yake ƙoƙarin
tsare mutuncin sarautarsa ko shugabancinsa ta hanyar riƙe
talakawansa da kyawo, ya ɗora su kan tafarki madaidaici wanda
zai amfani rayuwarsu. Yakan sa ido ya ga cewa, zalunci da cin amana da rashin
gaskiya ko yaudara bai wanzu tsakanin talakawansa ba. Yakan kare mutuncinsu ga
dukkan wani abu da zai kawo tarnaƙi ga
rayuwarsu. Shugabanni kan sa ido ga baƙi masu
shigowa cikin gari don gudun saukar da ɓara-gurbi. Haka ma
a ɓangaren
talakawa, akwai ɗa’a da
ladabi da biyayya zuwa ga shugabanni. Sukan kuma taimake su wajen tabbatar da
zaman lafiya mai ɗorewa da
kawo arziki da wadata a cikin ƙasa. Haka
kuma sarakuna sukan nemi shawarar talakawansu a cikin al’amurra daban-daban
domin tabbatar da adalci ga jama’arsu.
2.4 Zamantakewa Tsakanin Malamai da Ɗalibai
Malamai dai a cikin kowace al’umma
su ne masu ilmantar da jama’a maza da mata, yara da manya sanin hanyoyin rayuwa
tagari, da koya musu halaye masu nagarta, da nuna musu munanan halaye don su
kauce wa faɗawa a
ciki. Sannan su ilmantar da mutane ilimin addini da na zamani wanda zai shiryar
da su zuwa ga rayuwar duniya da na gobe. Malami shi ne mai koya wa yara ƙima
da girmama iyayensu, da yadda za su yi musu ɗa’a da
biyayya, da kuma yadda za su yi kyakkyawar hulɗa da
sauran jama’a. Su kuwa ɗalibai suna matuƙar girmama
malamansu da yi musu ɗa’a da biyayya da kauce wa duk wani abu da
zai sosa rayuwarsu. Sukan kuma ƙudurta
kyakkyawar niyya game da malamansu. Ba su cin zarafin malamai ko yi da su,
balle ma a gabansu. Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take gudana tsakanin
malamai da ɗalibansu.
Bugu da ƙari, ko da ilimin zamani ya shigo ƙasar
Hausa aka fara samun malamai da ɗalibai ‘yan ƙasa,
wannan kyakkyawan tsarin zamantakewa tsakanin malaman zamani da ɗalibansu
bai sauya ba. Gumel, (1999) da Bunza, (2012) sun nuna cewa, a wancan lokaci,
malaman sukan ɗauki ɗaliban
kamar ‘ya’yansu na cikinsu. Haka su ma ɗaliban sukan yi wa
malaman ladabi tamakar iyayen da suka haife su. Akwai girmamawa da tsare haƙƙin
juna tsakaninsu.
2.5 Zamantakewa Tsakanin Mawadata da
Talakawa
Masu iya magana na cewa, kowa am
mutum mutane ash shi. Zamantakewa tsakanin mai shi da mara shi abu ne gwanin
ban sha’awa a ƙasar Hausa. Mawadata ba su walaƙanta
talakawa, hasali ma sukan jawo su ga jiki domin su ma su sami albarkar dukiyar.
A wasu lokuta, mawadata sukan rarraba wa talakawa jarin da za su gudanar da
kasuwanci domin kowanensu ya amfana. Idan wata lalura ta sami talaka wanda ya
shafi aure ko suna da makamantansu, talaka yakan kai kukarsa ga masu shi kuma a
share masa hawaye gwargwadon iko. Su kuwa talakawa sukan kasance masu ɗa’a da
biyayya da gaskiya da riƙon amanar
dukiyar da masu shi suka damƙa masu.
Idan wata hidima ta samu mai shi, za ka tarar talakawa sun taru a ƙofar
gidan mai shi don su taya shi murna idan abin farin ciki ne. Idan kuma akasin
farin ciki ne ya auku, nan ma talakawan sukan taru domin taya shi juyayi da
jajanta masa. Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take tsakanin masu arziki
da talakawa a ƙasar Hausa, sai dai ɗan abin da
ba a rasa ba na saɓani na yau da gobe. Da ma Hausawa na cewa,
mutum duka ɗan tara ne
bai cika goma ba.
2.6 Zamantakewa Tsakanin Ma’aurata
Haƙiƙa
akwai kyakkyawar yanayin zamantakewa tsakanin miji da matarsa a ƙasar
Hausa. Miji yakan yi iya ƙoƙarinsa
na ganin ya tsare haƙƙin matarsa da ke
bisa kansa. Yakan kula da ci da sha da lafiyar matarsa da sauran lalurorin yau
da kullum gwargwadon hali. Yakan kauce ma wasu munanan halaye na cin zarafi ga
matarsa ko waɗanda
al’ada ba ta amince da su ba. Bugu da ƙari, miji
kan sa hannu wajen tarbiyyantar da yaran da suka haifa don ganin sun rayu bisa
turba tagari da yanayin zamantakewar duniya. Ita ma matar takan yi ƙoƙarin
tsare haƙƙin mijinta da ya rataya a wuyanta (Bugaje,
2013). Takan kasance mai ɗa’a da biyayya ga miji da rashin ƙetare
iyakokinsa. Ita ce mai kula da harkokin gida na yau da gobe, da tsaftar yara da
ba su tarbiyya tagari. Mace kan yi haƙuri da
mijinta da tausaya masa game da harkokin rayuwa (CCF, 2009; Sani da Abdullahi,
2016). Idan wata matsala ta shiga a tsakaninsu, sukan taushe zuciyarsu ga hana
aikata ɗanyen
hukunci. Wannan ne ya sa yawaitar sakin aure bai samu gindin zama a tsakanin
Hausawa ba. Haƙuri kusan shi ne jigon zamantakewar mata
da miji, tare da bai wa juna shawara don samun mafita a rayuwa (Gada, 2014).
Sai dai akwai masana da manazarta da suke ganin cewa, tun asali da ma Bahaushe
mai yawan sakin aure ne.
2.7 Zamantakewa Tsakanin Iyaye da
‘Ya’yansu
A koyaushe
burin mahaifa ko uwaye bai wuce ganin ‘ya’yansu sun tashi cikin halaye masu
kyau da nagarta. Saboda haka suke koya musu ɗa’a da
ladabi da biyayya da bin kyakkyawar turba don su ribanci rayuwarsu, al’umma ma
ta amfana da su. Uwaye sukan sanya yaransu makaranta irin ta addinin musulunci
da ta zamani. Sukan nuna musu muhimmancin gaskiya da riƙon amana
domin aiki da su. Sa’annan kuma da illar ƙarya da
cin amana domin su kauce musu. Sukan kuma nuna musu amfanin zumunci da ‘yan
uwantaka ta hanyar yawaita aikensu a gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki. Akan
koya musu sanin darajar mutane da girmama su, ba wai sai iyayensu kawai ba.
Saboda haka ne ‘ya’ya sukan kasance masu biyayya da jinƙan
iyayensu tun suna yara har zuwa girmansu (Bunza, 2012).
A taƙaice, ana
iya kallon yanayin zamantakewar Hausawa a jiya da wasu kyawawan abubuwa da
al’ada da addini suka amince da su da kuma masu aikata su.
i.
Gaskiya da riƙon amana
ii.
Zumunci da ziyartar ‘yan’uwa
iii.
Tsare haƙƙin maƙwabtaka
iv.
Taimako da tausaya wa juna
v.
Ladabi da biyayya ga shugabanni
vi.
Girmama na gaba
vii.
Adalcin shugabanni ga talakawa
viii.
Tsare haƙƙin
talakawa ga masu mulki
ix.
Haƙuri da
yafe wa juna
Duk da
cewa har yau akan samu waɗannan al’adu masu kyau wurin
Hausawa, sai dai abin ba kamar yadda yake da ba.
3.0 Taɓarɓarewar Zamantakewar Hausawa a Yau
Sanin kowa
ne cewa, matsayin zamantakewar Hausawa ya kai inda ya kai a yau. Kyakkyawar
tsarin zamantakewa da aka sani ga Hausawa a da, a yanzu ya ɗauki sabon
salo na koma baya. Kusan kowane rukunin tsarin zamantakewar Hausawa da aka
ambata a baya, an sami taɓarwarewarsa a yau.
Kyakkyawar zamantakewa da ke
tsakanin maƙwabta a da, ya fara yin nisa a yau. Sau da
yawa za ka iske ba a ga-maciji tsakanin maƙwabci da
maƙwabci, kowa ya kama mai fisshe shi.
Maganar maƙwabta su haɗu kowa ya
fito da abinci a ci tare ya zama tarihi a yau, kowa ya yi gabansa. Sai maƙwabta
su share mako ɗaya ba su
yi ido huɗu da juna
ba balle a yi maganar gaisawa, sai dai idan an yi kiciɓis da juna
a bisa hanya. Hatta ‘ya’yan maƙwabtan da
suke haɗuwa
musamman da dare domin gudanar da wasanni, ya sha ruwa a yau, kowane maigida ya
ja babbar ƙofa ya rufe ‘ya’yansa a cikin gida. Maƙwabci
bai san halin da maƙwabcinsa yake ciki
ba, na farin ciki ko akasinsa, balle su taimaka wa juna da shawara wajen samun
maslaha a rayuwa. Sau da yawa za ka iske
maƙwabta na ta husuma a kan iyakokin gida ko
haraba har zuwa wajen masu shari’a. Ga dai al’amurra nan sun cakuɗe sai dai
Allah ya gyara.
Shi kuwa harkar zamantakewa tsakanin
‘yan’uwa a yau ya zama abin da ya zama. Babu zumunci da taimakon juna, balle riƙon
aman. Kowa ya kama gabansa, kansa kawai ya sani sai ‘ya’yansa. A yau, idan
iyaye suka mutu suka bar marayu sai ‘yan’uwa su sa musu ido suna taggayara,
babu ilimin addini balle na zamani, ba su samun tarbiyya balle su amfani kansu
da al’umma baki ɗaya. A yau
idan ba ka da abin hannunka, babu ɗan’uwa mai kusantarka domin ba a
samun komai wurinka. Hatta shawara a kan wasu al’amurra na rayuwa ba a yi da
kai balle ka san halin da ‘yan’uwa suke. Su kuwa ‘yan’uwa masu abin hannunsu
sun keɓe kansu ba
su buƙatar kowa ya ziyarce su don gudun a aza
musu lalura.
Zamantakewa tsakanin masu mulki da
talakawa kuwa ya sauya fasali a yau. A maimakon kare haƙƙin
talakawa da mutuncinsu, masu mulki sun sanya ƙafa sun
shure wannan ɗawainiya
da ya ratayu a kansu. Sun kasa tsare mutuncin talakawa, sai cin amana da danne
haƙƙoƙinsu da ma
barazana ga rayukansu. Masu mulki sun ƙi
su jawo talakawansu ga jiki domin sanin halin da suke ciki. A dalilin haka, su
kuwa talakawa sun bijire ba su ganin mutunci da darajar masu mulki balle su yi
musu biyayya. Talakawa sai muguwar addu’a suke yi wa masu mulki saboda danne haƙƙoƙinsu
da ake yi. Zamantakewa ya taɓarɓare ta
yadda sai an kashe haki kafin yabanya ya sami walwala.
3.1 Dalilan Taɓarɓarewar
Zamantakewar Hausawa a Yau
A bayanin da ya gabata, an bayyana
cewa, kyakkyawar yanayin zamantakewar Hausawa a jiya ya samu gindin zama ne
saboda riƙo da wasu ɗabi’u da
al’ada da addini suka amince da su, kamar gaskiya da riƙon amana,
zumunci, haƙuri, taimakon juna, da makamantansu. A duk
lokacin da al’umma suka rasa ire-iren waɗannan al’adu, ko
suka yi rauni a rayuwarsu, tilas halin zamantakewar wannan al’umma ya taɓarɓare. Wasu
daga cikin abubuwan da nake ganin sun taimaka wajen haifar da wannan taɓarɓarewa na
zamantakewar Hausawa a yau sun haɗa da:
3.1.1 Yawaitar Zalunci
Saɓanin inda
aka fito, a yau galibin al’ummar Hausawa burinsu bai wuce tara abin duniya ko
ta halin-ƙaƙa (halat
ko haram). Masu kuɗi sun rage taimakon na ƙasa
gare su. Su kuwa masu mulki sai danne haƙƙin
talakawa idan sun shigo hannunsu. Shugabannin yanzu sun daina wakiltar
talakawansu, babban burin akasarinsu shi ne su wawari dukiyar talakawa da suka
shigo hannunsu a matsayin amana ta yadda ko bayan sun sauka ba za su talauce ba
daga su har jikokinsu. A kan haka, a yau matsananciyar adawa ta wanzu tsakanin
shugabanni da waɗanda ake
shugabanta, sai kallon-kallo ake yi wa juna. A yau, a gida guda ma idan wani
abin amfani ya shigo hannun wani daga cikin gidan wanda za a raba kowa ya amfana,
sai ka iske wannan da kayan ya shigo hannunsa ya wawuri wanda ya fi na
saura.
3.1.2 Rashin Haƙuri da Juriya
A yau
rashin haƙuri da juriya ya yi tasiri ainun a
tsakanin al’ummar Hausawa. Tashin hankula ya yawaita a tsakanin ma’aurata,
koyaushe sai an yi sulhu saboda yawan faɗace-faɗace. {arin
tabbatar da wannan zance shi ne, a leƙa kotunan
alƙalai za a ga yawan ƙararrakin
da ake shigarwa a kowane yini waɗanda suka shafi ma’aurata ne (Gusau
1991). Zawarawa sun yawaita a kowane sashe na gari. A unguwa ɗaya sai ka
sami zawarawa bila’adadin an sako su, wanda galibi saboda rashin haƙuri
da juriya ne. Ko a baya-bayan nan ma, hukumar Hisba ta kano ta fitar da ƙididdigan
yawaitar zaurawa da ake samu.
3.1.3 Zamani (Samuwar Intanet da
Finafinai)
Idan aka
yi la’akari da muhawarar masana da manazarta a kan alfanu da koma baya da
fina-finai suke samar wa, za a iya cewa, fina-finan Hausa sun kasance hanjin
jimina, akwai na ci a kwai na zubarwa. Haƙiƙa
fina-finan suna taimakawa ta ɓangarori da dama. Ali, (2004) ya ce,
a tsawon ƙarnuka biyu da suke wuce, samuwar
fina-finan Hausa shi ne hanyar haɓaka tattalin arziki mafi girma da
ya samu ga al’ummar Hausawa. Sai dai duk da haka, manazarta irin su; Iyan-tama,
(2004) da Alkanawy, (2000) suna ganin samuwar finafinan Hausa yana da illa ga
al’ummar Hausawa.
Daga cikin
illolin finafinan akwai ɓatar da al’ada. Al’adar kuwa ta haɗa da
zamantakewa. Samuwar finafinan ya sanya Hausawa kwaikwayon salon rayuwar wasu
al’ummu na daban, kamar Turawa da Indiyawa. Wato an mance da irin zamantakewar
Hausawa na cuɗe-ni-inp-cuɗe-ka
(Chamo, 2004; Ɗangambo, 2013; Guibi da Bakori, 2013).
Kiyawa, (2013) ya nuna cewa, finafinan sun ci karo da addinin Musulunci sannan
suna rusa ruhin auratayya da zamantakewa ta gari. Sannan akwai tarin manazarta
da suke da wannan ra’ayi (finafinai sun taka rawargani wurin taɓarɓarewar
zamantakewa ta gari). Sun haɗa da: Mwani da Ƙanƙara,
(2013) da Mai’aduwa, (2013) da Sulaiman (2013) da Ɗan
Maigoro, (2013) da Gwammaja, (2013) da Abdullahi da Maidabino, (2013) da Inuwa,
(2013).
A ɗaya ɓangaren
kuma, samuwar intanet ta shagaltar da da dama daga cikin Hausawa, musamman
matasa. Ta wannan kafa sukan ɗauki ɗabi’u
daban-daban na baƙin al’ummu musamman Turawa. Sauran illolin
kafar sun haɗa da yaɗa muguwar
farfaganda da jita-jita, da ɓata lokaci da kuma kalle-kallen
batsa (‘Yartsakuwa, 2017).
3.1.4 Rashin Gaskiya da Amana
‘Yan
kasuwa sun bijire wa gaskiya, sai son cin amana da yaudara da cin ɓatacciyar
riba da ɓoye
abubuwan sayarwa sai sun yi tsada. A yau, idan mai dukiya ya jawo talaka cikin
arzikinsa domin kowa ya amfana, sai talakan ya sa rashin gaskiya da cuta, ko
kuma shi mai arzikin ya riƙa danne haƙƙin
yaron nasa. A yau idan ka ba wani saƙon kaya ko
kuɗi ya kai
ma wani wuri ko ya adana maka har na tsawon wani lokaci, sai ya ci amanarka ya ƙi
kai saƙon ko ya salwantar da ajiyar da ka ba shi.
A yau mai gaskiya bai cika tasiri a mafi yawan kotunan shari’ummu ba, sai dai
wanda ya fi ƙarfin ba da abin hannunsa. Mata ta ci
amanar mijinta, miji ya ci amanar matarsa. Masu mulki da shugabanni sun murje
ido sun yi babakere da handamar dukiyar talakawa da aka ba su amana. Babu
gaskiya da amana tsakanin abokai da ‘yan uwa, ga abubuwa nan dai duk sun taɓarɓare. Ba
manufata ba ne da wannan bayanai cewa, babu kyakkyawar zamantakewa baki ɗaya a ƙasar
Hausa a yau ba, sai dai don yin hannunka-mai-sanda ga al’ummarmu domin a farga
ta yadda za a shawo kan matsalar tun abin bai yi muni sosai ba. Maikadara,
(2012) ya yi tsokaci kan wasu daga cikin halayen rashin gaskiya da ke faruwa a
yau.
4.0 Hanyoyin Farfaɗo
da Zamantakewar Hausawa
Haƙiƙa
za a iya cewa, taɓarɓarewar da
zamantakewar Hausawa ta yi a yau bai yi munin da za a kasa samar da hanyoyin da
za a warware matsalar ba muddin an himmatu da gaskiya. Dole iyaye su farga
wajen cusa kyakkyawar tarbiyya tagari a zukatan ‘ya’yansu ta yadda za su rayu
bisa turba madaidaiciya da za ta amfani al’umma, kamar gaskiya da mana, ladabi
da biyayya ga na gaba, sai kuma uwa-uba haƙuri wanda
aka ce shi ne gishirin zaman duniya.
Su kuwa malamai tilas su taka irin
tasu rawa wajen gargaɗi a kan hani da horo na koyarwar addini da
al’ada a kan irin zalunce-zaluncen da ya yi katutu a rayuwarmu ta yau. Haka
zalika su ci gaba da bayyana wa jama’a irin mummunar sakamakon da ke tattare da
aikata miyagun ɗabi’u da
al’adau ga masu aikata su. Har wa yau, dole gwamnati ta sanya ido ga harkokin
shari’a ta yadda za a daidaita adalci ga kowa, da kuma hukunta duk wanda ya
aikata ba daidai ba. Su kuwa sauran mutane kowa ya tsaya ya tsarkake zuciyarsa
da halayyanrsa ta yadda rayuwarmu za ta sake komawa ga turba mai tsarki da muka
gada daga magabatan da suka wuce.
5.0 Kammalawa
Zamantakewa
abu ne da ya shafi illahirin rayuwar mutane, idan ya inganta, rayuwar al’umma
ce za ta kyautatu, idan kuma ya lalace, rayuwar al’umma ce za ta taɓarɓare baki ɗaya. A taƙaice
ana iya cewa, tun asali al’ummar Hausawa suna da ingantaccen tsari na
zamantakewa a tsakaninsu da kuma sauran jama’a masu maƙwabtaka da
su. Sai dai kuma, babban abin takaici a yau shi ne, wannan kyakkyawar halayya tana
fuskantar gagarumar barazana na taɓarɓarewa.
Wannan kuwa yana faruwa ne saboda son kai da kwaɗayin tara
abin duniya, da rashin gaskiya da amana da haƙuri da ya
mamaye al’ummarmu ta wannan zamani. Sai dai ana cewa, ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba, ma’ana za a iya bin wasu hanyoyi da aka ambata a baya
wataƙila a shawon kan matsalar ta yadda
al’ummarmu za ta sake ginuwa kamar inda aka fito.
Manazarta
Abdullahi,
I. da Maidabino, I. B. (2013). Rawar da fina-finan hausa suke takawa wajen ɓata al’adun Hausawa:
Nazari daga fina-finai biyu Ƙara’i da Babban Yaro. A cikin
Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa).
Zariya: Ahmadu Bello University Press.
Alhassan,
H. da wasu (1982) Zaman Hausawa. Islamic Publications Bureau, Mushin, Lagos
Ali,
B. (2004). Historical reɓiew of films and Hausa drama, and their
impact on the origin, development and growth of the Hausa home ɓidious
in Kano. In Adamu, A. U. et al (eds).
Hausa Home Videous: Technology, Economy and Society. Kano: Gidan Dabino
Publishers.
Al-kanawy,
A. S. (2004). Fina-finan Hausa: Faɗakarwa ko shagaltarwa? In Adamu, A. U. et al (eds). Hausa Home Videous: Technology,
Economy and Society. Kano:
Gidan Dabino Publishers.
Bugaje, H. M. (2013), “Tarbiyya da Zamantakewar Hausawa: Jiya da Yau.” Mu}alar da aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Tsangayar
Fasaha, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar adua, Katsina.
Bunza,
A.M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Limited, Surulere Lagos.
Bunza, U.A. (2012),
“Tarbiyya a Cikin Adabin Hausa: Tsokaci da
Karin Magana.”
Mu}alar da aka buga a cikin Kada Journal of Liberal Arts, Ɓol: 7 No. 1,
Faculty of Arts, Kaduna State University, Kaduna.
C.N.H.N. (1981)
Rayuwar Hausawa.
Littafin da Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero Kano ta wallafa.
Chamo,
I.Y. (2004) “Tasirin Al’adun Turawa
a cikin Finafinan
Hausa”. A cikin Hausa Home Videos: Technology,
Economy, and Society, Jami’ar Bayero Kano.
Countries and their Cultures Forum (CCF),
(2009). Hausa. Retrieɓed on 21 September 2016 from: http://www.city-data.com/forum/ - world-forums
Ɗan gambo, H. A. (2013). Gurɓacewar al’adun
hausa a yau: Dalilansu da hanyoyin magance su. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa).
Zariya: Ahmadu Bello University Press.
[anyaya, B. M. (2007). “Karin
Maganar Hausa.” Sakkwato: Makarantar Hausa.
Ɗan
Maigoro, A. (2013). Tashin gwauron zabin fina-finan Hausa da taɓarɓarewar al’adun
Hausawa a goshin ƙarni na 21. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International
Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu
Bello University Press.
Gada,
N. M. (2014). Kutsen baƙin al’adu cikin hidimar aure a Sakkwato. Kundin digiri
na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato
Guibi,
I. I. da Bakori, A. D. (2013). Rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa
wajen ruguza al’adun Hausawa. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International
Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu
Bello University Press.
Gumel, (1992). “Tarbiyya da [angoginta a Wa}o}in Baka na Hausa”. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Afirka
da Al’adu, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Gusau,
S.M. (1999) “Tarbiyya
a Idon Bahaushe” A cikin Algaita Journal of Hausa
Studies. Jami’ar Bayero Kano. Ɓolume 1 No 1.
Gwammaje,
K. D. (2013). Kitso da ƙwarƙwata: Wakilcin al’adun Hausawa a
fina-finan Hausa. A cikin Bunza, A. M. da
wasu (editoci). Exepts of International
Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu
Bello University Press.
Inuwa,
U. A. (2013). Kutsen baƙin al’adu cikin fina-finan Hausa da yadda suke gurɓata al’adun
Bahaushe. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci).
Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa).
Zariya: Ahmadu Bello University Press.
Iyan-tama,
H. L. (2004). Matsayin fina-finan Hausa a Musulunci. In Adamu, A. U. et al (eds). Hausa Home Videous: Technology,
Economy and Society. Kano:
Gidan Dabino Publishers.
Ka’oje, U. I. (2006)
Tarbiyya a Ƙagaggun Labaran
Hausa : Nazari kan ‘Ya’yan
Hutu na Malama Bilkisu Funtuwa. Kundin digirin farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
Kiyawa,
H. A. (2013). Tsokaci a kan wasu matsalolin fina-finan Hausa wajen ɓata tarbiyya. A
cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci).
Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa).
Zariya: Ahmadu Bello University Press.
Koko, H. S. (2011). Hausa Cikin Hausa. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari Sakkwato: Nijeriya.
Magaji, A.
(1999) “Kunya da
Mutunta Mutane a Al’adar Bahaushe” A cikin Algaita Journal of Hausa
Studies, Jami’ar Bayero Kano.
Mai’aduwa,
A. A. (2013). Taɓarɓarewar al’adun
Hausawa a yau: Nazari a kan fina-finan Hausa. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa).
Zariya: Ahmadu Bello University Press.
Maikadara, I. B. (2012). “Tarbiyya a Rubutattun Wa}o}in Hausa na {arni na Ashirin”. Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Malumfashi, I. & Nahuce,
M.I. (2014). Kamusun Karin Maganar Hausa.
Kaduna: Garkuwa Media Services.
Mwani,
J. A. L. da Ƙanƙara,
I. S. (2013). The
role of films in moral decadence among Hausa yourth and the emergence of ƙauraye miscreant actiɓities
in Katsina. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa).
Zariya: Ahmadu Bello University Press.
Ƙamusun Hausa (2006). Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan
Nijeriya na Jami’ar Bayero Kano
Sani, A-U. & Abdullahi, M. (2016). Global
Growing Impact of Hausa and the Need for its Documentation. Being a paper
presented at the 29th Annual Conference of Linguistic Association of
Nigeria (LAN) on Language and Linguistic Diɓersity: Documentation and Reɓitalization
of Minority Languages for Sustainable Development, at the University of Jos,
Plateau State, from 5th to 9th December, 2016
Sulaiman,
A. I. (2013). Ta’addancin fyaɗe a fina-finan Hausa: Tsokaci kan tasirin fina-finan
hausa ga taɓarɓarewar al’adu yau.
A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci).
Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa).
Zariya: Ahmadu Bello University Press.
‘Yartsakuwa,
U. D. (2017). Zumunci a yanar gizo: harshen sadarwa tsakanin matasa a shafin
whatsapp. Kundin nemen digirin farko (B.A Hausa) a ƙarƙashin Sashen
Nazarin Harshunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.