An ce ‘garin so ba
ya nisa,’ ba don rashin nisa ko ƙalubale da ke
tattare da tafiyar ba, sai don shi so ‘mai hana ganin laifi ne.’ Duk da
kasancewarsa ‘makahon aiki,’ akan samu lokutan da maɗaci ke tarfuwa
cikin maɗinsa. Ɗaya daga cikin mafarin
irin waɗannan tangarɗa shi ne yarda da
da’ifan hadisan sheɗan game da
zamantakewa, musamman irin ta soyayya. Bahaushe na da samfuran ire-iren waɗannan kalaman da suka
shahara wurin raba kan masoya cikin maganganunsa na yau da kullum. Waɗannan baitoci sun
dubi kalaman da ke ƙasa a matsayin ‘Kwazazzabo A Hanyar Ƙauna’:
“Idan mace ta nuna
so, za ta sha wahala a hannun namiji!”
“Idan namiji ya
nuna so, zai sha wahala a hannun mace!”
Na yi tofin Allah-tsine
a waɗannan zantuka inda
a ƙarshe
na rufe da cewa: “A so shi ne nau ra’ayi!”
----------------------------------
Abu-Ubaida Sani
08133529736
----------------------------------
1. Kunne suka ɗau zance,
Sautin ga ya zan
mance?
2. Sautin ya ratsa
sifika,
Nan wayar da na ɗauka.
3. Ya doki fatar
kunne,
Ciki ya yi kan aune.
4. Ya ƙwanƙwasa wa dodo,
Gidansa can na na
gado.
5. A nan ya san babu
zama,
Ya
ɗauki saƙo shi ma.
6. Ya doshi fadar
kayi, (head)
Can ya je yak
kayi. (took to)
7. Sarki wato ƙwaƙwala,
A nan ya ba da
sanarwa.
8. Jini shi ne ɗan saƙo,
Ya kai shi saƙo-saƙo.
9. Sai zuciya ta yi
nauyi,
Sai duk jiki ya yi
sanyi.
10. Tunani sai ya yi
zarya,
Ya rinƙa yin gewanya.
11. Dukan jiki ya yi
lakwas,
Ya mai gudu sa’i
takwas.
12. Kogin tunani ya
kafe,
Kamar ƙanƙarar safe.
13. Miyon baki yai yauƙi,
Ɗacinsa ko ba sauƙi.
14. Idanduna sun yi ruwa,
Suna batun
lumshewa.
15. Lakar jiki ta yi
lakas,
Dukan jiki yai
mankas.
16. Na ji ni duk nai
lakus,
Ya mai wuni kan
kuskus.
17. “Idan mace tai
zurfi-
Kogi na so ta yi
laifi.
18. Za tai kwanan ƙunci,
Domin ta yo
ganganci.”
19. Wannan batu yai
muni,
Baƙi wulik a kamanni.
20. Tushensa ko sheɗan ne,
Salon ɓata zumunta ne.
21. Hanyar saɓa abota ne,
Tushen raba masoya
ne.
22. Mafarin tarzoma
ne,
Silan kai ga
rabewa ne.
23. Salon kau da
tunani ne,
Gwarin kai na
mutane ne.
24. Ko su mazan mene
ne?
Batun suke mui
aune.
25. “Bayyana so garaje
ne,
Nema wa kai wahala
ne.”
26. Me ya hana mu lura
ne?
Wanne za mu kama
ne?
27. Ni kam na san ƙarya ne,
So silan zama lau
ne.
28. Hanyar sada
zumunta ne,
Mafarin riƙon ƙauna ne.
29. Ina a ce dai mu
gane?
Mene ne son asali
ne?
30. Ina mu san yarda
ne?
Riƙon hanun juna ne?
31. Ina mu san marari
ne?
Tarairayar juna ne?
32. Ina mu san shauƙi na?
Da tai makon juna
ne?
33. Ina musan sa wa
ne-
A rai an zamto ɗai ne?
34. Ina mu san jigo
ne?
Sinadarin rayuwa
ne?
35. Ina mu san duk mai
so-
Ba ya cutar da
abin so?
36. Ina mu san mace
mai so-
Ba ta cutar da
mijin so?
37. Ina a san miji mai
so-
Bai cucin matar
mai so?
38. Ina a san in ga
so-
An zam ɗai dalilin so?
39. Na so a so a sanya
so,
Ya zam ana son mai
so.
0. Idan da so a san
da so,
A gane so da silan
so.
41. A samu sirrin riƙe so,
A ware so da
rashin so.
42. Kai zuciya akwai
batu,
Wasunsu ba su
ambatu.
43. Na sakaya na dunƙula,
Na cure na ko
mumula.
44. Na sallama wa
nazari,
Ya binciko shi
sarari.
45. Af! Na fara
sambatu,
Ba basmala farin
batu.
46. Ubangiji daɗo tsira,
Ga manzo baban
Zara.
47. Alaye duk saka da
su,
Sahabu jimlatan da
su.
48. Hamda Ilahu
Rahimi,
Kai ne ka tarfan
illimi.
49. Abu-Ubaida ne ya
yi,
A so shi ne nau
ra’ayi.
Juma’a, 04/01/2019
2:20am