Waƙar jaje ga Dr. Yakubu
Aliyu Gobir game da hatsarin mota da ya yi ranar Laraba, 10 ga watan Janairu,
2018
1.
Na
yi shirin adda da wuƙaƙe,
Na ɗau gariyo hannuna.
2.
Na
ɗau sandata da
kulake,
Na saɓa takkwabi gefena,
3.
Na
ɗau mashina da na
gada,
Tsitaka na nan
hannuna.
4.
Barandamina
na wasa shi,
Na ɗau kibbau a
kwarina.
5.
Majaujawa
na ɗau wannan,
Al’amuda na sanya
gefena.
6.
Na
ɗau baka na riƙe zarto,
Gatari na nan
hannuna.
7.
Na
sha ɗamarar kayan
sulke,
Babbar garkuwa ke
hannuna.
8.
Na
yo huci, zumbur zabura,
Na bar Sakkwato
dangina.
9.
In
na yi taku sai an girgiza,
Za ka ga ramin
sawu na.
10. In na hau dutse
sai ya dangaza,
Za ka ga garin
bayana.
11. In na bi daji sai
ya bushe,
Za ka ga tsirrai
sun ƙuna.
12. Idan na bi kogi
sai ya tsotse,
Tsabar zafin ƙalbina.
13. Idan na ga tsuntsu
sai ya faɗo,
Don hucin
numfashina.
14. Yau dai ko ni ko
ita,
Ta taɓa gefen rayina.
15. Ba mai ba ni baki
in tsaya,
Ana tsoron zafin
raina.
16. Ina tafiya sai na
yi birki,
Abin mamaki a
gabana.
17. Tsohuwa da rufi na
gani,
Ta tare hanya
wurin bi na.
18. Na ɗano kibiya na taɓe baka,
Na saita ta da
mashin hannuna.
19. Na zaro takobina ɗin nan,
Na ɗaga sandar dukana.
20. Kan na ɗau sauran kaya,
Kalamanta sukash
shiga kunnena.
21. “Idan ka kar ni
gidan duniya,
Lahira tabbas ka ƙuna!
22. Ni sunana ikilasi,
Tawakkali kuwa laƙabina.
23. Kana da buƙatar taimako,
Ka bi ni ka ji su
kalamaina.
24. Ka yi shirin yaƙi na gani,
Bai taimakonka
tunanina.
25. Tsautsayi da kake
nema,
Tai tafiyarta
wurin kwana.
26. Sannan jakadar
Allah ce,
Ba ta da laifi ɗan ɗana.
27. Tsautsayi da kake
kallo,
Ba ta dare sai dai
rana.
28. Domin idan ta
ziyarce ka,
Ga kai Allah na ƙauna.
29. Ka san tana rikiɗar siffa,
Fara ko baƙa mummuna.”
30. Na zare ido na
shiga thinking,
Don su biyu ne a tunanina.
31. Muguwa mai baƙin kaya,
Ita ats tsautsayi
guna.
32. Mai zuwa da farin
kaya,
Nasara sunanta
tunanina.
33. Ikilasi sai ta yi ɗan tari,
Ta katse dukka
tunanina.
34. “Mace ɗaya ce ba biyu ba,
Takan sauya ne ɗan ɗana.
35. In dai gajarce ma
zance,
Ɗiya ce ‘ya ta
cikina.
36. A har kullum in ta
zo ta,
Burinta ana tuna
sunana.
37. Idan ma an manta
iklas,
Tawakkali duk ɗai na.
38. Idan ta zo da
farin kaya,
An fi yin
tunanina.
39. Idan ta sanya baƙin kaya,
Akan ma manta
sunana.
40. Ga shi kamar kai a
yanzu,
Feɗes! Ka manta zancena.”
41. Na yo ‘yar ajiyar
zuci,
Kalaman sun tafa ƙalbina.
42. Na mai da kibau
cikin kwari,
Na sauƙe kayan yaƙina.
43. Ta yi murmushi ta
matso kusa,
Ta yo furucin ƙarshe guna:
44. “Duk wani mai so
ya tsira,
Ya bibiyi dukka
kalamaina.
45. Ya je makaranta biɗar saura,
Malam ya san
zancena.
46. Manta ni baƙin jahilci ne,
Dole ake tuna
sunana.
47. Ƙaryata ni ko kafirci
ne,
Dole a yarda da
zancena.
48. Ziyarar ‘yata
tilas ne,
Kasance cikin
ko-ta-kwana.
49. Ba shirin yin yaƙi ba,
Shirin tunanin
sunana.
50. Ni ko zan zo a
gareka,
In shiga cikin
zuci in zauna.
51. In sanyaya maka
tunani,
In sa ka ji rai ya
bar ƙuna.”
52. Tana faɗin haka sai ta ɓace,
Ɓat! Ba ta a
gabana.
53. Na yi lankwat na
yo kasaƙe,
Kalaman sun shiga
rayina.
54. Ashe lallai na yo
wauta,
Na so fita
addinina.
55. Dalilin ma kenan
da ya sa,
Na manta gishiri
girkina.
56. Na fara baiti
tor-tor-tor,
Ba godiyan
mahaliccina.
57. Na fara waƙa sar-sar-sar,
Ba salatin mazona.
58. Yafe Allah na
tuba,
Sallu alaihi
manzona.
59. Daɗo tsira da
amincinka,
Gare shi macecin
rayina.
60. Saka da iyalai da
sahabbai,
Da masu bin sa da ƙauna.
61. Na yi addu’a ya
Allah,
Ƙara lafiya da
tsawon kwana.
62. Ga malam tare da
imani,
A. Y. Gobir
limamina.
63. Ƙara masa arziki da
buɗi,
Da juriyar
addinina.
64. Shiryar da zuriya
tasa,
Su zam mariƙa addinina.
65. Da mu da shi da
iyalanmu,
Ka sa ranar ƙarshen kwana-
66. Furucin ƙarshe daga
bakinmu,
Shahada ce mai
hana ƙuna.
67. Amin Allahu ka
amsa,
Ba don mu ba maƙagina.
68. To a nan zan ja
birki,
Na tattare duk
‘yan kayana.
69. Abu-Ubaida ɗa ga Sani,
Ga matambayin
sunana.
70. Yawan baitukanta
saba’in ne.
Mi ta nazari dangina.