Alamomin Rubutun Hausa a Taƙaice

    bakake masu kugiya

     Alamomin rubutu na nufin ‘yan ɗigagga da zane-zane da ake amfani da su yayin rubutu. Waɗannan alamomi su ne ke gyara rubutu da sa masa tsarin da zai ba da damar karantuwa. Dalili kuwa shi ne:

    a. Alamomin rubutu ne ke nuna wurin da za a ɗan ja numfashi yayin karatu.

    b. Alamomin rubutu ne ke nuna wurin da za a dakata kafin a ci gaba da karatu.

    c. Alamomin rubutu ne ke sa a fahimta sannan a bambance tsakanin tambaya da umarni da bayani.

    A taƙaice, rubutun da ba a yi amfani da alamomin rubutu yadda ya kamata ba, zai kasance mai wahalar karantawa. Bayan haka, ba dole ne ma’ana/ma’anonin rubutun su fito a gane su cikin sauƙi ba. A ƙasa an kawo wasu daga cikin alamomin rubutun Hausa tare da taƙaitaccen sharhi game da kowanne.

    1. Aya (.)

    Aya alamar rubutu ce da ke nuna cikakkiyar tsayawa. Ana sanya wannan alama ne a ƙarshen jumla cikakkiya. Baya ga haka, ana sa ta ne a ƙarshen jumlar bayani (wato ba ta tambaya ko umarni ba. Misali:

    a. Audu ya je makaranta jiya.

    b. Amina ta tafi kasuwa.

    c. Malami yana koyar da yara karatu a cikin aji.

    2. Alamar Tambaya/Ayar Tambaya (?)

    Wannan alamar tambaya ma ana sa ta ne a ƙarshen cikakkiyar jumla, amma ta tambaya. Da zarar an tarar da wannan alamar rubutu, to a tabbatar da cewa tambaya ake yi. Misali:

    a. Wane ne ya je makaranta jiya?

    b. Wace ce ta tafi kasuwa?

    c. Wane ne yake koya wa yara katu a aji?

    Alamar Motsin Rai/Ayar Motsin Rai (!)

    Ana yin amfani da alamar motsin rai ne a ƙarshen jumla mai sosa rai ko kuma yayin da aka yi amfani da kalmomin motsin rai. Har ila yau, ana amfani da wannan alamar rubutu a ƙarshen jumlar umarni, musamman wadda ya kasance cikin tsawa. A ƙasa an kawo misalen wuraren da suka dace a yi amfani da alamar motsin rai:

    a. Hayya!

    b. Ɓace daga nan wurin!

    c. Yaron ya rasu!

    Lura: Duka waɗannan alamomin rubutu uku da aka ambata a sama (aya da alamar tambaya da alamar motsin rai) ana kiran su da suna “aya.” Yayin da aka sanya su cikin rubutu, to ana tashi ne da babban baƙi.

    4. Waƙafi (,)

    Wannan alama ce da ke nuna ɗan dakatawa da ake yi kafin a ci gaba da karatu. Yayin da aka ci karo da ita a cikin rubutu, ana ɗan jan numfashi ne sannan a ci gaba. Misali:

    a. Audu ya je makaranta jiya, amma yau bai samu damar zuwa ba.

    b. Amina ta tafiya kasuwa tun da safe, amma har yanzu ba ta dawo ba.

    c. Malam yana koyar wa ɗalibai karatu a aji, inda ya hore su da su mayar da hankali.

    Wuri na gaba da ake amfani da waƙafi shi ne yayin lissafo abubuwa masu nasaba da juna. A nan yana da kyau a lura da cewa, akwai masana da ba su aminta da a yi amfani da waƙafi domin lissafo abubuwa ba. Sun ba da dalilin cewa, harshen Hausa ba kamar na Ingilishi ba ne. A cewarsu, a maimakon a yi amfani da waƙafi, to za a yi amfani ne da “da” domin rarrabe abubuwan da ake lissafawa. Misali: Amina ta sayo alayyaho da yakuwa da kabewa da albasa. Yayin amfani da waƙafi wurin rabe abubuwan da ake lissaftawa kuwa, zai kasance kamar haka:

    a. Amina ta sayo alayyaho, yakuwa, kabewa da albasa.

    b. Cikin jakar akwai riga, wando, hula da agogo.

    c. Garuruwan da na taɓa ziyarta su ne Bauchi, Gombe, Yola, Ibadan, Legas da Benin.

    5. Waƙafi Mai Ruwa (;)

    Waƙafi mai ruwa tambakar waƙafi ne da aka yi wa ɗigo a sama. Ke nan a siffarsa, kamar an haɗa waƙafi ne da aya. Ana amfani da waƙafi mai ruwa ne a tsakiyar jumlar da ta kasance mai tsawo. Hakan zai ba da damar jan numfashi, wato tsawon jumlar ba zai kasance ya hana ta karantuwa ba. Misali:

    a. Abincin yana da yawa sosai; amma dai a zatona za su iya cinyewa.

    b. Duk faɗin makarantar nan ta Sakuwa; babu inuwar da za a zauna domin hutawaa

    c. Yaron ya taho da fara’arsa; amma tsoro ya hana shi ƙarasowa.

    6. Ruwa Biyu (:)

    Wannan alamar rubutu ne inda ake sa ɗigagga ɗaya a saman ɗaya. Wato kamar aya ce, amma ɗaya a saman ɗaya. Ana amfani da ruwa biyu ne yayin rubuta maganar wani ko wasu; ko kuma yayin rattabo wani abu kamar ba da misali. Misali:

    a. Audu ya ce: “Na sayi sabuwar riga.”

    b. Fatima: “Mene ne sunanka?”

    c. Ali ya daka masa tsawa: “Wuce ka ba ni wuri!”

    7. Alamar Zancen Wani (“”)

    Alamar zancen wani ya rabu kashi biyu. Akwai alamar buɗe zance da kuma alamar rufe zance. Ana amfani da su ne yayin rubuta zancen wani ko wasu. Ana rubuta zancen cikin waɗannan alamu. Idan aka lura da misalan da aka kawo a ƙarƙashin “a” da “b” da “c” da ke ƙasan 6, duk za a tarar da cewa an sanya zancen cikin alamar zancen wani.

    8. Baka Biyu ()

    Ana amfani da baka biyu ne domin ƙarin bayani a cikin rubutu. Yayin rubutu, akan sanya kalmar ko wani yankin zance cikin baka biyu a matsayin ƙarin bayani game da maganar da ake yi. Misali:

    a. Yaron nan (Musa) ya je makaranta jiya.

    b. Malimi (wanda ya wuce ɗazu) yana koya wa yara karatu a aji.

    c. Amina (‘yar gidan Malam Tanko) ta tafi kasuwa.

    9. Karan Jirge (/)

    Ana amfani da karan jirge ne wajen nuna zaɓi. Ana sanya shi tsakanin kalmomi biyu ko ɓangarorin magana biyu. Yayin da aka sanya shi, ana nufin duka ɓangarorin biyu suna ɗauke da ma’ana guda ko suna kan mizani guda. Wato dai suna zaman zaɓi ne. Misali:

    a. Cikin abincin nan akwai barkono/tonka.

    b. Yana jingine a jikin katanga/garu a waje.

    c. Ta ce ba ta son ganin yaro/yarinya a cikin ɗakin.

    10. Alamar Zarce (...)

    Alamar zarce ‘yan ɗigagga ne guda uku da ake sanyawa cikin rubutu. Ana sanya su ne domin a bayyana cewa magana ba ta ƙare ba; wato an katse ta ne kawai. Ana iya sanya alamar zance a wurin da aka so a ɓoye wata kalma ko wani zance bisa dalili na sakayawa. Ana kuma iya sanyawa bisa dalilin cewa cikaton zancen bayyananne ne; wato kowa ma ya san shi. A taƙaice, da zarar an yi amfani da alamar zarce, ya rage wa mai karatu ya cikace gurbin a zuciyarsa. Misali:

    a. Duk wani shugaban da ya sanya zalunci a gaba, to ranar lahira...

    b. Wanda bai ji bari ba…

    c. Ranar bukin nan za a yi shagalai. Kai! Allah dai ya kai mu...


    Pages