Waƙar da aka shirya domin shiga gasar waƙa ta Ƙungiyar Marubuta Waƙoƙin Hausa Reshen Jihar Bauchi, wanda aka gabatar ranar 12-12-1439AH a ɗakin taro na Gwani Mukhtar da ke cikin fadar Mai Martaba Sarkin Misau
1.0 Gabatarwa
An
shirya wannan waƙa
domin shiga gasar da Ƙungiyar
Marubuta Waƙoƙin Hausa Reshen Jihar Bauchi ta
shirya wanda za a gabatar ranar 12-12-1439AH.
Da yake dokar gasar ta nuna za a waƙe
waƙa ne, sai wannan takarda ta ga
dacewar taɓo abin da ya daɗe
yana ci wa marubuta waƙoƙi da ma masu rerawa tuwo a ƙwarya. Wannan abu kuwa shi ne kushe
da tsangwama da suke samu daga al’umma ta ɓangarori
daban-daban. A bisa wannan ne kuma aka ƙulla
zaren tunanin waƙar.
A
cikinta an yi ƙoƙarin kawo muhimmancin waƙa har kimanin guda ashirin da uku.
Gudun kada a yi ta bugun jaki ba tare da an bugi taiki ba, sai aka yi ƙoƙarin
nuna cewa, waƙa hanjin jimina
ce, wato akwai na ci akwai na zubarwa. Da ma dai Bahaushe na cewa: “Kowane
allazi da nasa amanu.” Saboda haka, an yi ƙoƙarin bayyana cewa, waƙa na iya kasancewa ta ƙwarai yayin da kawai aka yi amfani da
kalamai da kuma manufa nagari. Koma bayan haka kuwa, sai dai a ce, Allah ya
kyauta!
2.0 Waƙar ‘Amfanin Waƙa’
1. Wahidun da shi ke sa a yo fice,
Wanda ko shi ne ke
kawo dace,
Wahidun daɗo salati ga
fitacce,
Wa ahlihi sahabu dukka
jimlace,
2. Allah ɗora ni a hanyarka ta dace,
Ana rawa ɗan makaɗi ko zai fice,
A yau jigon da ni
na ƙwanƙwance,
Amfani na waƙa ni za ni
fayyace.
3. Ƙabila idan
harshenta yam mace,
Ƙarancin mawaƙa ne da bincike,
Ƙorafi akan isar da
shi sirrance,
Ƙunshe cikin azanci
fasahar zance.
4. A ba da nishaɗi waƙa hanya ce,
A fanni na ilimi
ma ko tai fice,
Ai a faɗɗakarwa waƙa gwana ce,
Akan wa’azantar da
waƙa
tabbace.
5. Rumbun kalmomi waƙa ta kasance,
Ranar da sunka ɓace ga su killace,
Rumbu ko take na
al’adu tabbace,
Ran da ake nema to
ga su taskace.
6. Da waƙa har akan sa zuci
ta huce,
Da ɗai a bi daidai
bayan an kauce,
Da ran mawaƙi ya zamo a ƙuntace,
Da ya zube ga waƙa sai fa ya mance.
7. Akan ma kafa hujja da waƙa ga zance,
“Ai ma ma’anar kaza, kaza ta kasance-
Ai ko duba wane
kaza ma hakka ya ce,
A duba waƙarsa kaza a kuwa
tantance.”
8. A inda ma ake jin nauyin a yi zance,
Akan saka shi waƙa a isar kaikaice,
A da, da yanzu duk
waƙa
ta kasance,
Arziki da hanyar
samun masarufi ce.
9. Ka duba yanzu waƙa tamkar sana’a
ce,
Ka san ko ba riba
sai ribar zuba zance,
Kuma a siyasa yau
ita babbar jigo ce,
Kasuwa ta
farfaganda ko dillaliya ce,
10. A nan harshe waƙa tamkar maƙera ce,
Akan ƙeƙƙera ƙira amma fa na
zance,
Akan koyar da
harshe kenan a taƙaice,
A sigar waƙa, ga salon sarƙafa zance,
11. Ga masu kasuwa ko tallafi ta kasance,
Gama cikinta ne
ake ta tallace-tallace,
Ga sauran ɓangarorin adabi na
zance,
Gami da rubutacce
ko matallafiya ce.
12. A farko dai karan kanta ta kasance,
A ɓangare na adabin
baka da rubuce,
A cikin labarai waƙa takan kasance,
Akan ko rera ta
don a ƙayata zance.
13. Bincika tatsuniya ka gan ta tabbace,
Bibiyi wasanni
ciki waƙa ta yi fice,
Bukukuwan Hausa ko
waƙa
fitila ce,
Ba ta zama baya fim [1]a
zamanance.
14 Akan rera waƙa don
aikace-aikace,
Aikin noma, kitso,
daɓe ka ji zance,
A sannan ita
hanyar saka tarbiya ce,
Akan tsara ga yara
sannan a yi dace.
15. Takan zamo ita hanyar yaɗawa ce,
Takan baza harshe
a duniya yai fice,
Ta kan kasance ko
hanya ta yabo ce,
Tarihi har wa yau
waƙa
kan kundace.
16. Akan bayyano nufi a gwamnatance,
Ai nuni ga yadda
shirin zai kasance,
Ashirin da ukku ne
na kawo a taƙaice,
Amfani fa na waƙa mu ƙara bincike.
17. Rayuwarmu waƙa babbar hikima
ce,
Ruwa biyu gare ta
ko takan gurɓace,
Ranar da anka yo
mummunan zance-
Ranar an ɗauki alhaki,
babbar illa ce.
18. A taƙaice waƙa kenan takan
kasance,
A matsayi na hanya
ta kai wa ga dace,
A fa gefe guda ko
sila ta kaucewa ce,
Allah dai ya sa
Musulmai mu yi dace.
19. Ga tambaya, shin ka san ita iri-iri ce?
Ga jeranton
rukunen mui ta binkice:
Gargajiya waƙa fa a fari ta
kasance,
Ga ta ga wasanni
da aikace-aikace.
20. Akwai ta gargajiya ta bakka wacce,
Ake da buƙatar kayan kiɗi a taƙaice,
Akwai ko rubutatta
da ake rubuce,
Akwai ko ta zamani
ta situdiyo ce,
21. Sannan waɗan nan da munka lisafce,
Su ma sun fa
rarrabu iri-iri a taƙaice,
Sai ka je ka duba
don ƙara binkice,
Sansani na fagen
waƙa
faɗi yalwace.
22. Akwai farin jini ga mawaƙi da yin fice,
Allah ko ya ba shi
falsafar haɗa zance,
Ai idan ka ɗai taɓo shi ka shiga
zance,
Amon wuta da
harshen taragon zance.
23. Rabbana du’a’ina ga kai ka amince,
Rabbana dukan mawaƙanmu su dace,
Rabbi rahhamarka
ba su, su ni’imce,
Ranar da za a
tsaya za ko a tantance.
24. Wanda ka cin duddugensu har da yafice,
Wahabu ka shirya
shi hanyarka ta dace,
Wanda ko ya fanɗare sa shi ya
galgalce,
Wahabu mu da shi
tsakaninmu dangace.[2]
25. A ce masu tsangwamar sun layince,
A ce masu ƙorafin ko sun
wayince,
A ce masu ƙin jininmu sun
amince,
Ai ko za a ɗau ilimi haƙiƙa tabbace.
26. Ƙaramin mawaƙi nake ɗa gun sani,
Ƙanƙani Abu-Ubaida mai
so ya sani,
Ƙasata Misau ne ko
can aka san ni,
Ƙarƙashin Jahar Bauchi
ta kasance.
27. A SHATALAMƊA ne na wallafa
ta,
A kawo gyaran
kuren da ke a cikinta,
Ashirin da bakkwai
yawan baitukanta,
Alhamdulilla tamat
nan na cike zance.
3.0 Taƙaitaccen Sharhi
Waƙar ta kasance mai zubin ƙwar huɗu.
Adadin baitukanta ashirin da bakwai ne (27). An buɗe
waƙar ne da yabon Ubangiji da kuma
salati ga Manzo. Sannan tana da babban amsa amo na ‘ce’. Daga farko za a iya
zaton waƙar mai zubi guda ne ta siffar amsa
amo, musamman yayin da aka yi la’akari da yadda aka yi amfani da ‘ce’ a
matsayin ƙafiyarta tun daga
baiti na farko har zuwa na ashirin da biyar (25). Sai dai yayin da aka dubi
baiti na ashirin da shida (26) da kuma na ashirin da bakwai (27), sai a ga
cewa, lallai ƙafiyar ‘ce’ ta
kasance ne kawai babban amsa amo. Lura da wannan bayani kuwa, ƙaramin amsa amo da aka fi yin amfani
da shi cikin waƙar
shi ne ‘ce’. An yi amfani da wasu ƙananan
amsa amo, wato ‘ni’ a baiti na ashirin da shida (26) da kuma ‘ta’ a baiti na
ashirin da bakwai (27).
Baya
haka, an yi amfani da wasu salailai cikin waƙar.
Ɗaya daga ciki shi ne salon wasa da
harshe. Misalin wannan salo ya zo a baiti na tara (9) inda aka kawo kalmomin riba (haram) da kuma riba(r) (halal) a ɗango
na huɗu.
Akwai kuma wurare da aka yi amfani da karin magana da kuma salon magana. Misali
a baiti na biyu (2), an yi amfani da karin maganar da Bahaushe ke cewa: “Kowa
ma ya yi rawa balle ɗan makaɗi?”
A baiti na ashirin da ɗaya (21) kuwa, an yi
amfani da salon abuntawa, inda aka bayyana tarin ilimi da ke ɓangaren
waƙa a matsayin fili wanda ke da faɗi
da yalwa.
A
baiti na ashirin da huɗu (24), an yi amfani da
baƙar addu’a. A cikin baitin an yi
mummunar fata ga waɗanda suka ƙi shiryuwa. An yi amfani da kalmomi
masu sauƙi a matsayin tubalan ginin waƙar. Sannan ba a sanya kurman baƙi ba. Wannan ne kuma ya sa waƙar ta kasance mai sauƙin ganewa ga mai karatu. Wani salo da
aka yi amfani da shi kuma shi ne, tabbatar da zubi guda na harufan da ke buɗe
ɗangwayen
kowane baiti. Yayin da aka ɗauki abajadan farkon
baitukan, za a fahimci cewa rubutu aka yi, wato an rubuta: “WAƘAR DA AKA GABATAR A GASAR WAƘA.”
Kamar
yadda aro ya kasance abincin harshe, an yi amfani da salon aron kalmomi a cikin
wannan waƙa. An yi wannan
aro ne musamman daga kalmomin Ingilishi da kuma na Larabci. Misali, a baiti na
goma sha uku (13) an yi amfani da kalmar Ingilishi ta‘fim’ (sai dai an riga da an Hausantar da wannan kalma). Kalmomin
Larabci kuwa, tun a baiti na farko za a fara tsintar misalansu, kamar su
‘Wahidun’ da ‘ahlihi’ da dai sauran makamantansu.
Kamar
yadda aka bayyana a gabatarwa, babban jigon waƙar
shi ne fito da amfanin waƙa,
domin ƙarfafa wa marubuta da masu rera waƙoƙi
(da ke kan hanyar daidai) guiwa. Da ma dai sun daɗe
suna shan tsangwama daga al’umma. Irin wannan tsangwamar ce ma ta sa Fati da
Kamis suka nuna ƙorafinsu
a cikin waƙarsu mai suna Ranar Ɗaya
ga Watan Ɗaya.
Suna cewa:
Sai a ce kar ka
auri mai waƙa,
Mace ko namijinsu
su duka,
Maroƙa ne baƙar harka,
Ba a
bambance mu gun ƙyama.
Fati wai don muna
waƙar,
Aka sa mu cikin
sahun shirkar,
Iko daga Rabbana Ƙadir,
Waƙa ta zam abin ƙyama.
A
gaba kuwa, har suke nuna cewa, kyawun waƙa
ko rashin kyawunta ya danganci yadda aka samar da ita. Suna cewa:
Waƙa na kai mutum fa
wuta,
Idan a cikinta yai
wauta,
Tana kuma kai shi
aljannata,
Idan a cikinta yai
salama.
Ko me ka faɗi cikin waƙa,
Da shi za ai
hukuncinka,
In alkairi ka
sassaƙa,
In
sharri ne da shi shi ma.
A
cikin wani lamari mai kama da wannan, ga bisa dukkan alamu Aminu Ladan Abubakar
(ALA) da sauran ‘yan ɗaninsa sun kai bango ga
turar da ake musa, wanda har suka fitar da waƙa
mai suna HASBUNALLAHU… A cikinta sun
yi baƙar addu’a ga masu tsangwamar su da
hana su sakat. Suna cewa:
Muna da maƙƙiya wanda ka yarda
mun ka gan su,
Akwai na ɓoye wanda kawai
Rabbi kai ka san su,
Rugurguje shirinsu
ka maida shi bissa kansu,
Da sun kira ka
Allah don miƙa buƙatunsu,
Ka juyar da buƙatunsu ya
Zuljalalu.
Cutar Gloria har
cholera gami da tension,
Cutar hawan jini
har Typhoid in addition,
Cuta ta kuturta da
makanta a conclusion,
Cuta ta ƙanjamau mai hana ɗan Adam emotion,
Kowa sai ya amsa
amin Zuljalalu.
Cuta ta Asthma da
Koshorko ka sa gare su,
Cutar Pneumonia da
ƙarzuwa
cikin jikinsu,
Ciwo na karkare da
kurkunu ka sa gare su,
Cutar Malaria Feɓer sa ka kassara su.
Kowa sai ya amsa
amin Zuljalalu.
Cuta ta Anthraɗ Allah sa a
jikkunansu,
Cuta ta Glaucoma a
sa a maganansu,
Cuta ta Trachoma
maƙala
wa ijjiyarsu,
Ka mai da su
kurame ka ɗoɗe maganansu,
Kowa sai ya amsa
amin Zuljalalu.
A
cikin waƙar, sun nuna irin salon tsangwama da
ake musu wanda har ta kai sun kasance tamkar jemagu a cikin al’umma. Ga dai
abin da suke cewa:
Ya mai tsare
halitta mun zo ka taimake mu,
Ka ba mu kariya
kar wani ɗa ya addabe mu,
Allahu kai katanga
ta tsari ga magautanmu,
Masu bibiyar ɓatanci ga
sana’unmu,
Mun zamma sai ka
ce jemagu da iyalanmu,
Mun zamma mujiya a
cikin jinsin yarenmu,
Suna ta cin amanar
bayinka cikin hammu,
Sun shigga innuwar
al’adu addininmu,
Allahu don isarka
da mu kai kaƙ ƙage mu,
Ka ba mu kariya
don ƙaunar Abu Batulu.
Bayan
wannan babban jigo da ya shafi bayyana alfanun waƙa,
akwai wasu ƙananan jigogi da
suka danganci bayanin waƙa
karan kanta, musamman rukunnenta. Sannan an bayyana irin baiwa da mawaƙi ke da shi musamman ta fuskar
fasahar sarrafa zance. A ƙarshen
waƙar kuwa, an yi amfani da wasu
salailai da suka shafi rufewa. Sun haɗa
da bayyana sunan mawaƙi,
da bayyana ramzi da yawan baituka. Daga ƙarshe
kuma an rufe da godiya ga Ubangiji da kuma ambaton tamat!
4.0 Kammalawa
Haƙiƙa
za a iya cewa, gasar da wannan ƙungiya
mai albarka ta sanya ya kasance sara ne kan gaɓa.
Dalili kuwa shi ne, yayin da marubucin waƙa
ya tabbatar da ɗimbin amfanin da take da
shi, to sai dai ya kasance maganar da Bahaushe ke yi: “Sara da sassaƙa ba ya hana gamji toho.” Fata dai
ita ce, Allah ya shiryar da marubuta waƙoƙi kan hanya madaidaiciya tare da
karkata bakin alƙalummansu
zuwa rubuta kalaman da suka kasance masu soyuwa a gare shi.