Naɗe Tabarmar So: Ta Abu-Ubaida Sani


    Naɗe Tabarmar So

    1.         Allah mai yin halitta,
    Ban shi ba mai iya ta,
    Ka amshi addu’ata,
                Ka gyara zuciyata.

    2.         Ka yo daɗin salati,
    Ga manzo baban Fati,
    Saka da ahli baiti,
                Sahabu masu gata.

    3.         A zuci yau da hazzo,
    Gare ku ga shi na zo,
    Ku tattaro ku zozzo,
                Ga kukan zuciyata.


    4.         An karya duk lagona,
    An rusa tanadina,
    Na saɓa alƙawarna,
                Da nai ga zuciyata.

    5.         Na dai faɗi a baya,
    A SO ni ba ni ƙarya,
    Na SO na yo soyayya,
                Da dukka zuciyata.

    6.         A sannu-sannu sai ko,
    Kwatsam na faɗa tarko,
    Na SO da ke da ƙarko,
                An kame zuciyata.

    7.         Gidanmu sunka yarje,
    Har ma da kansu sun je,
    Gidansu don a aj je-
                Zance na soyayyata.

    8.         Ba ai musu ga su ba,
    Batunsu ba a yar ba,
    Murna da ba kaɗan ba,
                Na bar wa zuciyata.

    9.         Loton ina Gusau ne,
    Aiki ba na a zaune,
    Sai dai batun ku gane,
                Ya kame zuciyata.

    10.       Nakan yi saƙe-saƙe,
    Har ma na sa a waƙe,
    Fatana dai mu sarƙe,
                A SO da nuna gata.

    11.       Nai dukka tanadina,
    Na wasa kalmomina,
    Na tsara zantukana,
                Zan sami sahibata.

    12.       Har ma na tsara waƙa,
    Sunanta ne na saƙa,
    Da zummar in na miƙa,
                Ta amshi gayyatata.


    13.       Na laƙƙe wa yayanta,
    Don tambaya a kanta,
    Domin sanin halinta,
                Gudun saɓa ƙa’idarta.

    14.       Tun ma kafin mu gana,
    Na ba ta dukka ƙauna,
    Na ayyana a raina,
                Na ba ta zuciyata.

    15.       Na labarta ta sannan,
    Wurin abokanan nan,
    Nawa da malaman nan,
                Matsayin tauraruwata.

    16.       Bayan na je ni salla,
    Ita ma ta zo hamdalla,
    Na ƙagu dai a ƙalla-
                Na kalli jarumata.

    17.       Ranar salla na je ni,
    Gidansu don bayani,
    Mun keɓe ga ta ga ni,
                Na ba ta akkalata.

    18.       Gare ni ta amince,
    Murna kamar in zauce,
    A nan mu kai ta zance,
                Da ni da jarumata.

    19.       Kamar mu kwana zaune,
    Shauƙi da soyayya ne,
    Amma da nay yi aune,
                Na dafe zuciyata.

    20.       Gare ta na nazarta,
    Abin da na fahimta,
    A zuci mun bambanta,
                Da ni da sahibata.

    21        Aiki take da buri,
    Ni ko na yo inkari,
    Cikin salo da tsari,
                Gare ta jarumata.


    22.       In dai gajarce zance,
    Haka muka kasance,
    Ra’ayinmu a bambance,
                Ni da tauraruwata.

    23.       Washegari mun zauna,
    Mu kai hirar lumana,
    A ƙarshe nai bayana,
                Gare ta ‘yar uwata.

    24.       Cikin kurman baƙi ne,
    Salon da za ta gane,
    Na zayyano batu ne,
                Ƙoluluwar fahimta.

    25.       Na so a ruffe zance,
    Har ran da zai kasance,
    Karatunta ta kammalce,
                Ta huta sahibata.

    26.       Amma na yo tunani,
    Abin ko ya dame ni,
    Da shi na kwan na yini,
                A zuci ina tuna ta.

    27.       Idan a ce na share,
    Mu kai nisa a tare,
    Ƙarshe mun ka ware,
                Na cuci sahibata.

    28.       Tamkar fa yaudara ce,
    A ce wai mun kasance,
    Ƙarshe na zo na kauce,
                Na bar ta jarumata.

    29.       Na tuntuɓi ƙanina,
    Na ce ni ra’ayina,
    Kaza-kaza ke raina,
                Bamban da sahibata.

    30.       Ya ba ni shawararsa,
    Ya ce fa shi ganinsa,
    Idan mu kay yi nisa,
                To an riga an ɓata.


    31.       Na sam Nazifi nawa,
    Ya ce na yo komawa,
    In nemi sasantawa,
                Da ni da sahibata.

    32.       Na je ga ‘yar uwata,
    Wato nufi yayata,
    Ta nuna damuwarta,
                Ga ni da jarumata.

    33.       Abin ya cushen kayi,
    Na rassa yadda zan yi,
    Ƙarshe na ce abin yi-
                In samu sahibata.

    34.       Bayan isha mun zauna,
    Na furta ƙuddurina,
    Batun fahimtar juna,
                Da ni da jarumata.

    35.       Na ce na san da tun da,
    Kina da buri na gida,
    Yaya kike son sa tun da?
                Su’ali sahibata.

    36.       Wato me ra’ayinki?
    A kan aure, gidanki?
    Ya kike so ki gan ki?
                A nan na tambaye ta.

    37.       Ta ce miji na gari,
    Da zuri’ar alkairi,
    Nan ta tuƙe ba ƙari,
                Ga amsa tambayata.

    38.       Ta ce sai ni in fara,
    Abin da duk na tsara,
    In bayyana ƙarara,
                Na kalli sahibata.

    39.       A ƙarshe dai na furta,
    Ba na biɗar matata,
    Ta yo aiki da kanta,
                Na fita ta bar gidanta.


    40.       Na ce to yanzu amman,
    Ga fili na musamman,
    Ja ra’ayina kan wannan,
                Ko ki dawo jam’iyata.

    41.       Bayaninta kaɗan ne,
    Ta nuna taimako ne,
    Na ce in ko hakan ne,
                Tambaya sahibata-

    42.       Idan fa wagga aiki,
    Ba a biya gare ki,
    Ko sisi ba a ba ki,
                Za ki yi sahibata?

    43.       Ta ce ko za ta yi shi,
    Gare ta nai murmushi,
    Sannan na ja numfashi,
                Bayan na fuskance ta.

    44.       Idan miji na aiki,
    Sannan mata na aiki,
    Ki yi tunani da kanki,
                Ya ne fa zai zamanta?

    45.       Gidan ga za a kulle,
    Ɓarayi ko za su ɓalle,
    Ko katanga su tsalle,
                Ba mai hana su sata.

    46.       Ko mai gadi ya zauna,
    Domin guje wa ɓarna,
    To duk ciki wane na,
                Zai kama zuciyata?

    47.       Dubo batu na ƙaruwa,
    ‘Ya’yan sun fara taruwa,
    Gidan su wa ake kaiwa?
                Ya saɓa falsafata.

    48.       Yawo in har ka saba,
    Ba za ka so hani ba,
    Ƙarshe ka yo tababa,
                Ya karya ƙa’idata.


    49.       Abin da duk ake yi,
    Yaro harda yake yi,
    Shi ma ko za yana yi,
                Tarbiya ko lalata.

    50.       Yaron da anka kai shi,
    Wurin aiki to ko shi,
    Halaye na nan gare shi,
                Za ya ɗau manufata.

    51.       Idan mata ta zauna,
    Dutin dare mu auna,
    Gida miji ya kwana,
                Shi da ‘yan ɗiyanta.

    52.       Idan miji ya ƙosa,
    Juriyar ya kasa,
    Sabon aure ya kwasa,
                Ta ga an ware ta.

    53.       In amaryar ba ta aiki,
    Dukkan takardu na kirki,
    Zai kai su nata ɗaki,
                Mataimakiya ce ita.

    54.       Akwai gida a ƙalla,
    Idan aika anka ƙulla,
    Zuwa gidan ko walla,
                Ta yiwu a rasa ta.

    55.       Samun matar sai ƙila,
    Mijin mu ce ya-Alla,
    Akwai tarin wahala,
                Idan babu mata gida.

    56.       Ban da ma fa zargi,
    Da za a yo gare ki,
    Domin fitanki aiki,
                Haɗuwar maza da mata.

    57.       Ban da ma fa kishi,
    Ga shi miji da kanshi,
    Idan ya ga waninshi,
                Yana ɗumi da mata.


    58.       Idan katse labari,
    Na yo bayani tari,
    Na ce akwai inkari?
                Na tambai sahibata.

    59.       Ta fara yin bayani,
    Da zan bari gare ni,
    Na kwa ji ba gare ni,
                Kalaman sahibata.

    60.       A nan na sake lura,
    Ba saura na dabara,
    Sai ko in za na tsara,
                Ƙarya ga sahibata.

    61.       Wato na ɗai amince,
    Alhali yaudara ce,
    Bayan aure mu kece,
                Ni da sahibata.

    61.       Da dai ni nai ƙarya,
    Gwara shirin ya tsaya,
    Mutunci ya fi soyayya,
                Ba ni ƙarya ga mata.

    62.       Ban ce aiki ba kyau ba,
    Ba a yi ba shiri ba,
    Special plan ba,
                Shi ne ɗai mannufata.

    63.       Ni ba ni son tilastawa,
    ‘Yanci na nan ga kowa,
    Tunani na kan saɓawa.
                Kowa da tasa fahimta.

    64.       Ba ni zaɓi a ƙarshe,
    Na yi amai na lashe,
    Tabarmar so na kwashe,
                Da ɗai ta zam ƙanwata.

    65.       Na zaɓi in rasa ta,
    A kan dai in tauye ta,
    Ra’ayi in hana ta,
                Na haɗiye soyayyata.


    66.       Tuni na alƙawarta,
    Zan yi addu’a gareta,
    Samun miji irinta,
                Mai ra’ayin aikinta.

    67.       Ni ban yi yaudara ba,
    Ban ko saka a rai ba,
    Ni za a yaudaren ba,
                ‘Yanci ne manufata.

    68.       A nan ne zan taƙaita,
    Abu-Ubaida yai ta,
    Ɗan Sani za ni huta,
                In reni zuciyata.
    author/Sani, A-U.

    journal/Poem
    pdf-https://youtu.be/CyaIV1GUG_g

    paper-https://youtu.be/CyaIV1GUG_g

    Pages