Da
fari zan sako Allah ne Mahaliccin mu,
Mai
ba mu kariya da ke amsa buƙatunmu,
Da
mun yi addu’a zai amsa mana roƙonmu,
Ƙaro daɗin
basira Allah a ƙwaƙwalenmu,
Allah
ƙaro salati ga shi dai manzonmu,
Haɗa
da dukka sauran sabban manzonmu,
Har
da alaye da tabi’ai magabatanmu,
Ka
ba mu kariya Jalla tsare imaninmu,
Mu zamma masu gaskiya ba ɗai
musu ba.
A
yau dai zance ne tsubi-tsubi gare mu,
Sai
dai babu lokaci na haska zuciyarmu,
Za
mu tsakuro ne kaɗan na ƙwaƙwalwarmu,
Sai
dai fatar da mun kai a gane madosarmu,
Ba a karanta kawai matsayin labari ba.
Akwai
damuwa guda da ta mamaye ƙalbinmu,
Jama’armu
ga shi har yau sun kasa fahimtarmu,
Sun
kasa fassaran ƙwarai ga halin nan
namu,
Wannan
ya sa a yau muke feɗe salailanmu,
A rayuwa na tare bai kyauttu da zargi
ba.
Wanda
ya ce shi to ba shi ba ne gare mu,
“Man
ƙala ana…” zance daga manzonmu,
Wannan
dalili kenan na rurrufe zancenmu,
Za
dai mu ba da labari kaɗan daga harkarmu,
Da fatan a fahimta ba a karanta a aje
ba.
Shigar
mu jami’ar nan farko na rayuwarmu,
Mun
ƙwallafa ƙaunar ‘yan kwas a zuciyarmu,
Mun
ka fara nemo su don haɗi na kanmu,
Da
mun tarar guda ƙauna
ko jinin jikinmu,
Amma a wagga hali ba mu samu haɗin
kai ba.
A
nan sabon nazari ya zo ga zuciyarmu,
Mun
ka iske H.O.D. domin ya taimake mu,
A
nan ya ba mu lambobin duk ‘yan uwanmu,
Har
2go sannan muka bi ‘yan uwanmu,
Abin baƙin
ciki sam ba a nuna haɗin kai ba.
Da
anka yo gwajin farko ag gare mu,
Waɗanda
sunka faɗi
sun fi addadinmu,
Wani
har ya tambaye ni menene abin damu?
Ya
ga na damu, gashi ko twenty na samu,
Na ce me amfani nai ‘yan uwa ba su
samu ba?
Bayan
mun fara ɗan sabo da waɗansunmu,
Har
littafansu muke karɓa ‘yan uwanmu,
Mu
kofe musu note daga namu don su samu,
Idan
ko har assignment aka bayar gare mu,
Ba za mu yi mu bar saura ba su samuba.
A
kwan a tashi mun samo haɗi na kanmu,
Tutorial group muka
sa don ya agaje mu,
Ashe
wani sabon artabu ne hakan gare mu,
Zuwan
ganin-dama ake ta yi gare mu,
Amma muka jure ba mu nuna fusata ba.
Bayan
tutorial ko wassu su iske mu,
Su
ba da uzzururrukan ƙarya
ag gare mu,
Dole
muj jiyo kunya gunsu ‘yan uwanmu,
Mu
ɓata
lokacin da ya dace da karatunmu,
Duk wannan ba ya sa gobe su gyara ba.
Wasu
har suna jin haushi ma gare mu,
Ganin
yadda muke ɓarna na lokacinmu,
Mu
ko tausayi ya hana nuna zuciyarmu,
Daɗinta
ma a sannan ba jama’a tuli gare mu,
Sai dai a zuciya ba mu so a rinƙa yin haka ba.
A
sa’ilin ko ba sisters a tsakanin mu,
Mahaɗarmu
conɓocation sannan marabarmu,
Baban
dalilinmu a nan shi ne filosofinmu,
A
taimakon brothers ba tsangwama gare mu,
Ba kamar na sisters da za a ba wa sharhi
ba.
Mun
riga a da can mun sa wa zukatanmu,
Mun
biye wa tsantsar kunya da ke jininmu,
Ba
mu iyya ko da kallon ‘yan uwanmu,
Walau
a kan hanya ne ko suna gabanmu,
Tsangwamar da hakka ya ja ba ƙarama ce ba.
Kullum
in mun ka dawo hostel matsuguninmu,
Abokai
ka ɓulɓulowa
da ƙorafi gare mu,
Wai
mun ido huɗɗu da su mun kau da kanmu,
Ga
shi ba mu rantsuwa don mun hani ga kanmu,
Haka suke taffiya ba tare da sun yarda
ba.
A
yau da gobe har jama’a su kai yawa gare mu,
Waya
a kan waya har ya yo yawa gare mu,
Ko
mun yo bayanin haka ba a tausayin mu,
An
manta da ko mu ma akwai aiki gabanmu,
Mun zi mu karɓi
takarda ba mu yi bauta ba.
Duba
an kasa gane ajistin da ke gare mu,
Dan
mun ce ba mu sani ba sai a tsangwame mu,
Wai
mun sani ba mu son koyar da ‘yan uwanmu,
Mu
ma fa ɗalibai
ne sai an koyar mu samu,
Mutane muke ba a haife mu da sani ba.
A
ƙarshe rayuwa ta fara tsaurara gare
mu,
Zaman
school gaba ɗaya
yaf fice a kanmu,
Akwai
ma lokacin da muka ɗauki tarkacenmu,
Ana
fa jarrabawa muka koma garinmu,
Ba don hakan ba ko da rai bai huta ba.
Halan
wani zai ga kamar raki gare mu,
Mu
ko mun ga ma ɗunbin na ƙoƙarinmu,
Mun
yi juriya kuma mun danne zuciyarmu,
Don
har malamai na ba da shawara gare mu,
Bai kyautu mai ka a ce ya samu ɗai
ka ba.
Babu
lokacin hutu sam a ajandunmu,
Lokacin
morokon wane na karatunmu,
Lokacin
ƙara’in wance na assamenmu,*
Lokacin
kallon ball wane tuttoriyanmu,*
Sun cinye lokacinsu namu ba su ƙyale ba.
Duk
waɗanga
hali mun danne zukatanmu,
Sai
kwatsam ko ga shi an ta da zuciyarmu,
Rainin
hankali wayo an ka yo gare mu,
Sai
dai mun ba da shawara a birni na tunaninmu,
Gemun da ba fari, ba a sa masa lalle
ba.
Ku
yi haƙƙuri da mu sisters, gare mu,
Za
mu so sannan idan kun ka fahimce mu,
Ilahu
ya sani darajar ku ag gurinmu,
Ku
ne wayayun ƙwarai mu ag
gurinmu,
Ba masu tantama da hukuncin Allah ba.
Hankalinku
ne ya sa kuka kama zukatanmu,
Kun
tsare mutucinku ta koyarwar manzonmu,
Masu
taƙamar wayewa dabbobi ne gare mu,
Sun
bijirce wa tarbiyyar addini al’adunmu,
Za su yi da-na-sani ba ko da nisa ba.
Ubaida
martabarki da girma take gare mu,
Ko
don fa sunanki da ya kama zuciyarmu,
Sumayya
ƙoƙarinki
ne ya kama hankalinmu,
Tarbiyya
irin taki da shiga ta addininmu,
Da ikon Rabbana rayuwa ba ta muku ciwo
ba.
Sa’adatu
kin zamo kamar ‘yar uwa gare mu,
Ƙoƙari
a rayuwarki ya kama hankalinmu,
A’isha
haƙiƙa
kina a tunaninmu,
Kina
da son karatu da tambaya gare mu,
Ya Allah ya ba ku janna ba da hisabi
ba.
Ku
miƙa gaisuwar nan ga elder sistarmu,
Zamanta
gidan aure ya sa ta zama antinmu,
Ku
ci gaba da kauce wa dukkanin haramu,
Za
ku kai ga nassara ga dukkanin alamu,
Ba wai burgewa a jami’a kawai ba.
Su
ce da mu ƙauyawa mu ce su
batsattsu,
Su
ce da mu primitiɓe
mu
ce su watsattsu,
Hulɗa
da mu su yanke ga Jalla tasu ta datsu,
Ko
dai su tuba duniya ko kabari su matsu,
Manzo ya nuna haka ba ƙirƙira
nake ba.
Duk
wacce ke tunƙaho wai ita ta
waye,
Tana
da samari tuli har tana tawaye,
Tsaya
rayuwa ta ja buƙatarsu
ta janye,
Ta
zam tamkar matatta bayan ga ta a raye,
Wanda bai bi Allah ba, ba ya ga da daɗi
ba.
Wasu
lokuta muna ba ku sharwarinmu,
Mu
ma muna biɗa ko shawara ku ba mu,
Hakka
ne zaman tare don cika burinmu,
Allah
ya ba mu sa’a ya ƙara
taimakon mu,
Ya sanya wagga boko ba a banza za mu
yo ba.
Arba’in
ne baitukanta mun yi accumulation,
Sadaukarwa
ga sisters ne da sun ka yo adhesion,
Waɗanda
su ga Allah ne sun ka yo retention,
A
kan shi kaɗai yake ba da acƙuisition,
Allah da mu da su duka ka ba mu
cigaba.