Da
kalula a hannuna,
Da
zogi a hannuna,
Da
ciwo a jikana,
Da ƙunci ƙalbina,
Da
zafi a jinina,
Da
haushi ƙirjina,
Da
tunani kayina,
Da
buri zucina,
Na baro duniyata.
Da
likita gabana,
Da
Tsaure gefena,
Da
Khalid ta samana,
Da
idanu duk kaina,
Na baro duniyata.
Na
dubi muhallina,
Wurin
dai kwancina,
Na
gane wurin dai na,
Nai
tsam da tunanina,
Don hango duniyata.
Zuci
ne tai fama,
Baƙin ciki da nadama,
Ƙwaƙwalwa ta bi ita
ma,
Duk
jiki sai kyarma,
Na mararin duniyata.
Rai
da ya tumbatsa,
Zuciyata
sai ta matsa,
Ƙwaƙwalwa ko ta watsa,
Tun
gaban ma in kintsa,
Tuni na wuce duniyata.
A
duniyar ba mugu,
Sai
dama babu hagu,
Ba
‘yan uba ko shegu,
Ba
hassada in ka ɗagu,
Wani abu sai duniyata.
Ba
miskili ko raggo,
Kowa
aiki ya agogo,
Can
gaskiya tai zango,
Halin
ƙwarai
yai zango,
Da lumana a duniyata.
Idan
gari ya waye,
Duhun
dare ya yaye,
Ka
so ganin tsuntsaye,
Da
ke ta yin gewanye,
Suna waƙe duniyata.
Idan
ka ja numfashi,
Ya
gauraye ka da ƙamshi,
Idonka
yai wani lumshi,
Saboda
daɗin ƙamshi,
Ku so ganin duniyata.
A
duk gefen hanya,
Dashe
an sassanya,
Fulawowi
ga bishiya,
Ganyensu
lif-lif sun tsaya,
Ka kwan kallo duniyata.
Ga
gulbi ga ƙorama,
Gudanar
ruwa mai ni’ima,
Idan
ka ta da kai sama,
Gajimare
sun yi laima,
Dubun ni’ima duniyata.
Ka
kalli namun daji,
Bayan
gari nan jeji,
Ga
nan duwatsu daji,
Ga
itatuwa nan daji,
Daɗin gani duniyata.
Idan
rana ta tsala,
Cikin
gari da walwala,
Kowa
garin ba matsala,
Zaman
garin ba wahala,
Da walwala duniyata.
Fuskar
kowa sai fara’a,
Wadatar
zuci da dabi’a,
Halin
ƙwarai
ga ɗa’a,
Matan
mazan sun sa’a,
Zamantakewa duniyata.
Ba
faɗa ba gaba,
Ba a
sata ba fargaba,
Ba a
fashi babu daba,
Ba
ka ga mai laifi ba,
Ba kurkuku duniyata.
Kun
san aikin ‘yan sanda?
Suna
zaga gida-gida,
Akwai
matsala wanga gida?
Domin
su taimaki gida.
Ba criminal duniyata.
Idan
dare ya soma,
Idan
ka ta da kai sama,
Jerin
taurari a sama,
Tsakaninsu
ba gardama,
Kamar al’ummar duniyata.
Ina
cikin jin daɗi,
A
duniya mai daɗi,
Tamkar
mashiyi na maɗi,
Kwatsam!
Katsewar daɗi,
Sai na baro duniyata.
Tun
kafin na baro ma,
Nakan
ji dai sama-sama,
Har
jiki ya yi dama,
Zuciya
ta shirya ma,
Don baro duniyata.
Nan
kuwa a hannuna,
Kamar
ruwa ke gudana,
Na
ji sanyi a hannuna,
Na ƙi motsa jikina,
Rabina na duniyata.
Ashe
jini ke malala,
A ƙasa yana dalala,
Likitoci
sun shagala,
Yayin
wannan tultula,
Ni ko ina duniyata.
Cike
bokiti da ruwa,
Aka
zo don gogewa,
Ruwan
tuni ya rinewa,
Jini
ya yo komawa,
Sannan na baro duniyata.
Likitoci
sun ruɗe hala,
Suna
tambayar sila,
Na
neman salsala,
Kawai
dai sun wahala,
Amsa na duniyata.
In
dai taƙaita labari,
Na
dawo duniyar sharri,
Da
ke da ɗumbin garari,
Ga
ko mugun sharri,
Nitsuwa sai duniyata.
Wani
nawa ya ji ni,
Ina
faman guna-guni,
Na
kushe halin zamani,
Da
yabon duniyata ni,
Ba na kushen duniyata.
Ya zo
domin tambaya,
Game
da wagga duniya,
Kawai
sai nai dariya,
Na
ta da kai samaniya,
Niyar zuwa duniyata.
Zuwanta
ai ba wahala,
Buƙata kawai ka samu
sila,
Kafin
ka ankara walla,
Tuni
da kai an lula,
Sauƙa sai duniyata.
Ba
na buƙatar mota,
Tafiya
babu jigata,
Kafin
ido ya ƙifta,
Kafin
mashi ya gifta,
Na kai ga duniyata.
Idan
ka harba bindiga,
Daidai
sanda na ruga,
Kafin
harsashi ya shiga,
Tuni
fa ni nakan riga,
Ƙulewa duniyata.