Bulaliya



    A gai da masu sa’a,
    Da sun ka taki sa’a,
    Gare su babu a’a,
    Sannan ba a bara’a.


    Wannan samu na sa’a,
    Ya sa su ba su É—a’a,
    Girma na kai sana’a,
    Samu ne ko É—abi’a?

    Ko na ƙi juya harshe,
    In na fito Bahaushe,
    Na dunƙulo na ƙunshe,
    Tuni ƙwaƙwalwa ka cushe.

    Sunkuyo nan É—auki zance,
    Domin salon raÉ—a ce,
    Cikin tarnaƙi rubuce,
    Mu bar bami can kurumce.

    Idan ka bauta wa Allah,
    Ka yo dukan farilla,
    Domin biÉ—ar É—ai falala,
    Ka sam hujja a ƙalla.

    Mai bibiyan iyaye,
    Ga su da bai tawaye,
    Hujja garai a waye,
    Hidima, ciki da yaye.

    Wanda ko ya ƙuƙuta,
    Aiki tuƙuru da bauta,
    Domin ya fanshi mota,
    Dalili garai ba wauta.

    Mai aiki da ya bautu,
    Mai yin zufa ya jigatu,
    Domin É—ai ya suturtu,
    Hujjarsa ta fahimtu.

    Mai kai wuni a rana,
    Ba ji ba gani ba magana,
    Domin gida ya gina,
    Hujjarsa taƙ ƙwaraina.

    Mai yin aikin kuÉ—inshi,
    Ko nema don a ba shi,
    Ko ma ya amshi bashi,
    Ya kammala ya tashi-

    Ya miƙa duk kuɗinshi,
    Kayan shayi a ba shi,
    Ya sarrafa da kanshi,
    Shayin ya ba karenshi –

    Kai ka ji kayan haushi!
    Kawai ya fara haushi,
    Da me ya fi karenshi?
    Wadai da tir gare shi.

    To ga shi ko karenshi,
    Da ake aiki dominshi,
    Ya bararraje abinshi,
    Banza ta zo gare shi.

    Yunwa da ta ciyo shi,
    Ya duba nan gabanshi,
    Bai ciyuwa gare shi,
    A nan banzan fushinshi.

    Mai shi ya kar kuÉ—inshi,
    Ba yadda zai riƙe shi,
    Saura ko ba su son shi,
    Gwanjon wani? Tur da shi!

    Nan hankali zai zo garesu,
    Da zai sa tsana na kansu,
    Sun yo tsiya wa kansu,
    Allah wadai tunaninsu.

    Kafin mu sa addini,
    Yiwo kallo gare ni,
    Tukun da ƙwaƙwalwar tunani?
    In e, to yo bayani.

    Na yo zubin karen ne?
    Koko na mai karen ne?
    Mai tanadin shayin ne?
    Da bai tuno goben ne?

    To dakata saurara,
    Duka wannan gadara,
    Da ma dukan dabara,
    Kakkausa anka tsikara.

    Idan akwai sikeli,
    Ƙwaƙwalwa, ku hau da goli,
    Shi ne zai ja sikeli,
    Ko don zane misali.

    Gwara buhun siminti,
    Kai, gwamma a ba ni minti,
    Halan na É—an yi santi,
    GWANJON banza ga kanti!


    Jaɓa a dai kiyaye,
    Da zarar damar ta janye,
    Inuwar ta kau, kya yi tsaye,
    Karan jan aji ya karye.

    Da addinin Allah ne,
    Abin samin lada ne,
    Da bin uwa uba ne,
    Wannan harkar lada ne.

    Da ma a ce gida ne,
    Na san wurin zama ne,
    Da mota ce zan gane,
    Abin hawa a je ne.

    Amma fa duk shiru ne,
    STUPID! Taƙamar ta me ne?
    Me ke hanun kare ne?
    Da kuikuyo zai tsugune?

    Ƙarshe cikon bayani,
    Allah da yai zamani,
    Ya tsawata ruÉ—in zamani,
    Idan an ƙi sai ran bayani.


    Pages