Dr. G - Gareka Allah na zo neman dace,
Ganiyu in ban da kai zan
lalace,
Ga ni biÉ—ar tallafi zan yo
zance,
Ofisan sanya maraÉ—a kunyance,
Ojoro yau babu wurin jero
zance,
OÉ“É“asa! Biyo mu je
duniyar zance.
B - Bari
in faro batuna al’adance,
Babba sai Babba in yi
Hausance,
Bigi ai sai Bigi ko
Turance,
Bugin ƙirjina guda, ɗa na kasance.
I - Inkari
ba a yi haÉ—uwar nasara ce,
Ina maso kwancewa da zai
lalace?
Ina mai ƙullelliya da zai
susuce?
R - Rahama
ta farko dai ta addini ce,
Rabbi ya sa tab biyu
ilimi ta kasance,
Dr. L - Lamarin mutum kaÉ—ai sani wahala ce,
Lallai ko dabbobi wahalar
ninki ce,
Lallai kenan a
aure sai nagartacce.
A - Ai
na ga Prof. Bunza ya lamunce,
Abdullahi S.S.
Dakta ya ce –
A wagga hidima a
gaba ya kasance,
Allah san barka
Dakta ya angwance.
R - Rabbi
mai ikon ta da matacce,
Roƙo nake Ilahu ka
amince,
Rahamanu ka sa auren
rahama ce,
Rahimu sa a yo shi
nagarce.
A - Allah
sanya zuriyar ƙwarai ta kasance,
Ai kuwa a ga ‘yan É—iya na kwatance,
A fagen illimi ko lallai
sa yo fice,
Arrahamadu na roƙa ka amince.
B - Ba
su zaman lafiyan da ba ce-ku-ce,
Ba musu ba saɓanin zance,
Bar su tare har fa su
tsofance,
Ba su jika da taɓa-kunnen zance.
A - A
bisa goma É—aya É—oriya ce,
Abu-Ubaida nai baituka taƙaice,
Addu’a da fatan alkairi
ce,
Alhamdu SHATLAH na
kammalce.
August, 2017