Gabatarwa
Mutane
na cewa, tun farkon ɓullowana Allah ya sa mini
haske da ƙyalƙyali da za a iya kwatanta shi da
walwalin-waliyo, tamkar dai na sunduƙin
Ƙolin-Ƙoliyo.
Kasancewar haka ne ma, taurari da dama kan kai caffa farfajiyata, wani lokacin
har cikin da’irar da nakan zagaye yayin murnar haihuwar giwa
a dokar jeji. Sai
dai, ban taɓa ko da mafarkin marabtar ɗaya
daga jikin taurarin a matsayin Zara ba. Ba ina nufin raina haskensu ba ne, a’a,
kawai ina gudun yanka wa kare ciyawa ne, musamman da yake a lokacin na kasance
a filin dagan da alƙalami
shi ne babban makami. Ko ba komai za a mini uzuri kasancewar ba a tauna taura
biyu a baki guda. Toh! Sanin kowa ne dai sai an kula kashi yake ɗoyi,
to da yake ban sanya a ka ba (wai in ji ɓarawon
tagiya), sai na zamana sayau.
Adashen
ƙauna, waƙa ce ta biyu (wanda ta farkon ita ce Asusun Ƙauna)
da na ƙaga domin nuna cewa, Allah ne bai
kawo lokaci mafi dacewa da in tsunduma kogin iyon zamantakewa ba domin linƙayar da kan kai ga bagiren aure. Sannan
a maimakon yaudarar kaina da na wata, da ma cacar lokaci da aljihu, gwara in yi
tanadin abubuwan da watakila sun salwanta har zuwa lokacin dafafutukan zai zama
mai tushe da madogara. Na nuna cewa, lokaci na zuwa da zan shigo tsarin, kuma
ma har watakila in taka rawa da baza mai ban mamaki.
Ana
bikin duniya ake na kiyama, saboda haka ne na yi amfani da wannan dama wurin
isar da saƙwannin faɗakarwa
da jan hankali zuwa ga ma’aurata da ma waɗanda
ke kan hanya, dangane da kyautata zamantakewa. Tun da ma dai, taɓarɓarewar
zamantakewar aure abu ne da ya daɗe
yana ci mini tuwo a ƙwarya,
wai Allah wadarai naka ya lalace (inji jakin gida da ya ga na dawa). A ƙarshen waƙar kuwa, na nuna kasancewana tilo a
jiki da zuciya, tare da ƙaguwar
ganin na marabci abokiyar rayuwa, duk da kuwa a lokacin ban kawo tunanin kowa
ba (har a zahiri ba a duniyar waƙa
ba kawai). Sai kuma na kammala waƙar
da barkwanci inda nake zolayar wannan tauraruwa da a lokacin tsara waƙar babu ita.
Bayan
na kammala wannan waƙa
tare da ɗora
ta a intanet, na faɗa wa abokaina da dama
cewa; da yardar Ubangiji kashi na uku na wannan waƙa zai fito ne da sunan mataimakiyar. Fatana a kullum, Allah ya
sa mu riƙa tuna akwai haƙƙoƙin zamantakewa da addini ya wajabta a
kanmu. Allah ya sa mu ɗauki rayuwar aure bauta,
ba kamar yadda sau da dama ake kallon sa a matsayin filin kokuwar nuna isa da
gadara tare da sauƙe
fushi da ɓacin rai ba.
Sadaukarwa
Waɗannan
baituka sadaukarwa ne ga
masu tunani nagari da karɓar
shawarwari nagari da kuma aikata aiki nagari.
Adashen Ƙauna
2
Ya Mahaliccin
talikai,
Da ya sanya mutane
ke buki.
A yo aure a yi
haihuwa,
Yayinsu biyun fa
ana buki.
Ka ba ni basira
Rabbana,
Yau na karkata
zancen buki.
Kai daɗin tsira ga
Nabiyina,
Da wurinsa mu kai
koyin buki.
Duk da kafinsa ana
buki,
Ga shi muka ɗau darasin buki.
A baya kaɗan nai tsokaci,
Kan maganar nan ta
buki.
Adashe ni na raɗa mata,
Adashen ƙauna ko buki.
Kashi na biyu na
taho da shi,
Ga batun nan dai
zancen buki.
Na faɗa miki yau zan
jaddada,
Ina tanadin ranar
buki.
Tanadi na kuɗi gefe guda,
A gefen ko sai
tsarkin jiki.
Ba jiki kaɗai ba da zuciya,
In tsare har ranar
buki.
Tuni na kulle
makullen zuciya,
Mabuɗi na hannunta
miki.
Akalata na nan ga
ke,
Ja ni mu je ranar
buki.
Asirkan nan da a kai
mani,
Igiyun duk an damƙa maki.
Kin riƙi sitiyarin
zuciya,
Tuƙa ni a sannu har
buki.
Me kike shayi ya
sahiba?
Ai kin nasara an
bar maki.
Ba mai ƙwace ni a gu naki,
Muna nan tare mu
sha buki.
Ta yiwu mui zance
kaɗan,
Ko tattauna batu
na arziki.
Ko mui yi hirar
illimi,
Da wata ɗiya ta arziki.
Amma ba mu batu na
SO,
Wannan na tara
maki.
Ba ƙauna ba marrari,
Babu zumuɗi sai ga ke.
Ba hirar SO
kowace,
Sai in hirar nan
da ke.
Ki sha kuruminki
kina da ni,
Sam ba ni wulaƙantar da ke.
A zamanmu da ke za
ai batu,
Maraɗa sa yo kassaƙe.
Na ƙi duk hirar
dandali,
Na tanada zan yo
wa ke.
Na ƙi wasa ko da
zolaya,
Da mace, duk na
tara wa ke.
Ko da te-te ina
maki,
In har nai aure da
ke.
Ko a-sha-ruwa ko
kike biɗa,
Na tsuntsaye a sha
da ke.
Ko da langa kike
biɗa,
Sai in ɗana lako duk wa
ke.
Kai! Ko dungure na
kule,
Na wuntsila don
faranta wa ke.
Idan aiki na gida
kuwa,
Ban bari ya
wahalshe da ke.
Ko in taya ki a
zahiri,
Wato aikin mu yi
ni da ke.
Koko in yi kwance
in bar ki can,
Amma in yi ta ziga
ga ke.
Ko Ɗanmaraya yana faɗin,
A wurin yaƙi bai yin sake.
In soja suna can
kan wuta,
Shi ko zai nan gun
fake,
Amma zai ta kiɗi wa su,
Da zuga alhali dai
fake.
Ban fita hira in
daɗe waje,
Alhali gida na bar
ki ke.
Ban fita waje don
daɗi in ci,
A gida kuwa lami
shi da ke.
Ba ni bin ra’ayina
duka,
Alhali na ƙi naki ke.
Ba ni hana maki
walwala,
Alhali ni ko ina
sake.
A gare ki zan yi ɗawainiya,
A taƙaice za ni kula da
ke.
Lafiyarki za ni
kula da ta,
Cinki, shanki duk
ba sake.
Za mu rinƙa zaman hira da
ke,
Mui almara ni da
ke.
Za mu yo barkwanci
da ke,
Fara’a kullum ni
da ke.
Idan akwai wata
damuwa,
Za mu tattauna ta
ni da ke.
Idan na kuskure
gaskiya,
Zan saurari batunki
ke.
Idan kika kauce
gaskiya,
Ni ko zan nusantar
da ke.
Son kai ke sanya
hayaniya,
To mu guje masa ni
da ke.
Lalaci kasalar
zuciya,
Mu guje su kadda
mu yo sake.
Ziga na ƙawaye kar ki ji,
Har ‘yan uwa masu ɓatar da ke.
Ki lura da halin
duniya,
Kar daɗi ya ɓatar da ke.
Haƙƙin aure ki bar
sake,
Sauƙina ya ruɗar da ke.
SO da nake nuna wa
ke,
Kul ya sakankantar
da ke.
Kar ki ji ke sai
lalama,
Girman kai ya ɓatar da ke.
Kar ki ji kin
zarce faɗa,
Kin fi ƙarfin a nusar da
ke.
Kar ki ji kin wuce
tambaya,
Sannan abin a hana
wa ke.
Kar ki ji ke in
kin ka so,
Abu dole-a-dole a
ba wa ke.
Banda gadara
tutiya,
Na kin mallaki mai
aurenki ke.
Ban da kallon
rayuwar-
Wasu, me ya talo
ma ke?
Kar da ki zam
almubazzara,
Addini ya yi hani
ga ke.
Na hore ki da
godiya,
Ga nufin Allah duk
ga ke.
Matsala ta gida ta
tsaya ga mu,
Kadda waninmu ya
ji ga ke.
Addini ko ki sa
gaba,
Kar shagala ta
gusar da ke.
Idan kin kama
wanan batu,
Da ma saura da na
tsallake.
Rayuwarmu na daɗi ƙwarai,
Wane mai santin
rake.
Za mu zaga
wuri-wuri,
Da ziyara duk ni
da ke.
Za ni kai ki
gari-gari,
Mu buɗe ido duk ni da
ke.
Za mu je bakin
ruwa,
Da wurin hutu mu
shantake.
Za mu kallon namun
dawa,
Halittun Allah
sassake.
Na daɗe kewarki farin
gani,
Zuciya na hasko da
ke.
Fara, baƙa wa yas sani?
Allah ne zai ba ni
ke.
Watakila ana ta
hari ga ke,
Fatsansu kikan
tsattsallake.
Sai tawa fatsar
zinariya,
Zan saƙala in saƙalo da ke.
Allah sada mu da
lafiya,
Da imani ni da ke.
A nan ne zan ja in
tsaya,
Amma da batu da na
tsallake.
Sai a gaba in mun
haɗu,
Inda zancen nan
zan cike.
Af! Na tuna ya Gimbiya,
Tambaya ɗaya zan yo wa ke-
Ya bayanin
KISHIYA?
Ma’ana abokiyar
zama ga ke?