Na tsara waɗannan ‘yan baitoci ne a matsayin
barka da salla ga A’isha (Humaira). Bayan shauƙin soyayya da ya ja ni zuwa ga
tunanin baitukan, a ɓangare guda shauƙin adabi da ke zuciyata ya taimaka wajen
ingizo mini jeranton kalaman da zan yi rubdugun salailai da su. A bisa wannan
dalili, bayan kasancewar ‘yan baitocin saƙon soyayya, suna zaman wata maƙera ta
sarrafa harshe da luguden kalmomi. A taƙaice, an ƙuduri jifan tsuntsaye biyu ne
da dutse guda.
1. Hamdan Allah Rahimi,
Baiwar da ka min rai
yai fari.
2. Ka ƙaran basira zuciya,
Ninkinta ya zam wane ɗari.
3. Ka ƙara salati Rabbana,
Ga manzon tsira ɗahiri.
4. Alaye da sahabu sa-
Dukanmu masoya zikiri.
5. Humaira ƙalamna ke nufi,
Da na bayyana son ta a
sarari.
6. Hotonki na salla ya iso,
Abin da ido ke marrari.
7. Sun zaga ƙwaƙwalwa tai yabo,
Ganinsu ya sa zuci
marmari.
8. A kullum ina daɗa godiya,
Ilahu ya ban damar
ciri.
9. Na banke maza da guda-guda,
Da kowa ke faman hari.
10. Samunki ya sa na wuce maza,
Kaɗan ya hana mini
fahari.
11. Son da nake miki ya cika,
Yawansa ya kai ai
nazzari.
12. Zan so ki da baki da zuciya,
In ɗauke ki mu zaga
gari-gari.
13. Duk matsalarki fada mini,
In saurare ki da
hamzari.
14. Son da nake miki baɗini,
Tuni ya ninka na zahiri
15. Son da nake miki A'isha,
Girmansa ya wuce
nazari.
16. Ya riƙa yai tozo ƙaho,
Na ga son har ya yo
ƙari.
17. Ƙarinsa na harbe mahassada,
Da mai gulmar mu da
makiri.
18. Humaira son ki ya kumbura,
Zuciya ta cika ba wuri,
19. An ce ƙuncin zuciya,
Cuta ce da ba ta da
makkari,
20. Ni na samo magani,
Humaira ke ce sinadari.
21. Ash'ab ba ni da walwala,
Son ki ya saka mini
sasari.
22. Walwalata guda sai in da ke,
Zumuɗi har da su
mazzari.
23. Idan ba kya kusa ban nitso,
Kamar na hau borin
giri.
24. Riƙe ni in samo nitsuwa,
Kada sonki ya sa a
sakan mari.
25. Kallonki ne 'yancin zuciya,
Da ke kulle ta dawo
sarrari.
26. Na so ki, ki so ni mu yo ta so,
A sonki na ƙaro
kuzzari.
27. Na shirya, shirya mu je,
Shirinmu kar ya yi
jinkiri.
28. Riƙen in riƙe ki mu zam guda,
Riƙon mu yi ƙamƙam ya
maƙari.
29. Tsaya in tsaya mu yi tsaitsaye,
Mu tsare matsalar duk
mai hari.
30. Ki zo na zo mu zamo haɗe,
Zamanmu ya zam zakkar
gari.
31. Ki shigo na shigo mu shige ciki,
Shigarmu cikin nai wa
shiri.
32. Miƙo na miƙe mu miƙa gaba,
A gano mimmiƙarmu a
sarari.
33. Doso na doso mu doshi-
Zamanmu da ba rabuwa
har kakari.
34. Hanga na hango mu hangi-
Zaman da masoya duka ke
hari.
35. Abu ga Ubaida yake batu,
Na Humaira masoyin
zahiri.
36. Barka da salla kau na yi,
Cikin zantukanga
ƙiri-ƙiri.