Adashen Ƙauna 4 (C): Bege

    Adashen Ƙauna

    Waɗannan baitoci wani ɓangare ne na waƙar Adashen Ƙauna 4, wato ɓangaren “C.” Saboda haka, kada a yi mamakin kasancewa an fara baitukan ba tare da mabuɗi ba, ko kuma a ƙarshensu ba a kawo marufi ba. 

    Tun ina ƙirga sakanninmu,
    Har yawansu ya yo auki.

    Tun ina ƙirga daƙiƙunmu,
    Har yawansu ya zam ninki.

    Tun ina ƙirga awowi ma,
    Har suka zam sinki-sinki.

    Rabuwar da mun kai ni da ke-
    Na fara ƙirgen kwanaki.

    Har muka kai kan satuka,
    Wai yaushe ne zan gan ki?

    Duk kaina ya ɗau zafi,
    Humaira saboda tunaninki.

    Zuciya ta ta yi fushi,
    Burinta kawai ta iso gunki.

    Ƙwaƙwalwa ta ba ni kashe di,
    Lallai in je in nemo ki.

    Idona sun yi jugum zaune,
    Burinki kawai su yi kallonki.

    Hancina duk sun damu,
    Burinsu sui aiba da ƙamshinki.

    Kunnuwana sun yi lakwas su ma,
    Suna kewa na kalamanki.

    Bakina ba ya nishaɗi,
    Yana kewar amsa hirarki.

    Ƙafafuna ba sa harka,
    Sun yi rashi na zuwa gun ki.

    An kira meeting na ƙasa-da-ƙasa,
    Domin tattaunawa kanki.

    Hankali da tunani sun taru,
    A fadar ƙwaƙwalwa saraki.

    Zuciya ma ta samu zuwa,
    Sun tattauna batu kanki.

    Sun ce sam ba sa yarda-
    Da in nisa daga kallon ki.

    Sun yi barazana da yawa,
    A kai na in har na bar ki.

    Za su sako takunkumi,
    Domin kare muradunki.

    Suna da dakaru da yawa,
    Za su kare muradunki.

    Mantuwa sojan Tunani ne,
    Zai yaƙen wai domin ki.

    Zuciya ta ce Kaftin Haushi,
    Ya shirya don kare ki.

    Tabbas-tabbas na gane,
    Ba ni saki na ƙaunarki.

    Ba na wasa ko na kaɗan,
    Ba ni ga yarda in rasa ki.

    Don kuwa zan kasa sukuni,
    Zan fuskanci baƙin aiki.

    Ko shekaran jiya nai fama,
    Da nay yi sakoko da ƙaunarki.

    Tuni aka je yajin aiki,
    Majalisar kare muradunki.

    Kin ga idanu sun jona,
    Sun ce sulhu sai sun gan ki.

    Kunnuwa ma sun shiga yajin,
    Sun ce sam ba sa aiki.

    Sun shimfiɗa sharaɗoɗinsu-
    Shi ne ji na kalamanki.

    Hancina zai yi resigning,
    In har na nesanta wurinki.

    Ƙafafu ma sun yo warning,
    Za su yi komai dominki.

    Ga baki ya shiga yaji,
    Domin jaddada ƙaunarki.

    Ko jiya ma da na je sulhu,
    Ha ce sulhun sai ga ki.

    Hummy wai sai in mu haɗu,
    Domin ya ambaci sunanki.

    Na ce ya kira ki kamar zikiri,
    Yai ta faɗi mana sunanki.

    Ya ce ai sam haka bai yiwu,
    Shi atafir sai ya gan ki.

    Duniya ta yo zafi,
    Babu sukuni in ba ki.

    Rayuwa ta yo ƙunci,
    Ba walwala domin ba ki.

    Farin ciki ya yo nisa-
    Daidai kimar nisanki.

    Nishaɗi shi ma ya ƙaura,
    Tun da ya zo ya tarar ba ki.

    Murmushi kam yai hijira,
    Ba yi zama sai in ga ki.

    Annashuwa ta na ɗe kaya,
    Da kanta ta fita neman ki.

    Na ga Fara’a jiya na ta ƙwafi,
    Ranta ya koma kanki.

    Na ga Raha ya yi tagumi,
    Duk ya damu da kewarki.

    Numfashina ya sauya,
    A’isha domin kewarki.

    Bugun zuciyata ya ƙaru,
    Dalilin hakan kuwa nisarki.

    Tunanina yau a daskare,
    Kaifin ya koma wurinki.

    A’isha zan neman sulhu,
    A janye yajin aikinki.

    Na tanadi dalilai ƙwarara,
    Don gamsar da wakilanki.

    Kin ga dai ba son ra’ayi,
    A tilas ne na baro gunki.

    Na biyu na zo nan domin,
    Kare mutuncinmu da naki.

    Na uku nisantar juna,
    Ba ya rage mini ƙaunarki.

    Ko da a zahiri nai nisa,
    A zuci ina nan a wurinki.

    Kaih! Dalilan na da yawa,
    Na tabbata za su gamsarki.

    Ko ba komai ke tawa ce,
    Domin ni na zam naki.

    Ko ma mene ne kuwa dai-
    Zan kare miki ni ɗinki.

    Sai ki riƙe mini ke ɗina,
    Riƙe kanki a ni ɗinki.

    Sai mu riƙe mana mu ɗinmu,
    Ke tawa ce ni ko naki.

    Kin zama ke ɗin ni ɗina,
    Na zama ni ɗin ke ɗinki.

    Mun zama mu ɗin mu ɗinmu,
    Komanmu guda ba mai raki.

    Read: Adashen Ƙauna 3...

    author/Sani, A-U.

    journal/Poem
    pdf-https://youtu.be/DaseuGQDZGE

    paper-https://youtu.be/DaseuGQDZGE

    Pages