1.
Nai
godiya ga maƙagina,
Da ya sa Humaira na same ki.
2.
Wace
bauta na yo mai kyawo ne,
Wane aiki nai shin me tsarki?
3.
Da
Allah ya duba buƙatuna-
A ciki ya ba ni ƙaunarki?
4.
Humaira
wai kin san mene?
Na sam naso na
halinki.
5.
A
da ina kallon kaina,
Ɗa nake mai halin
kirki.
6.
Ban
san ina fa da aibu ba,
Humaira sai da na same ki.
7.
A
nan na ga kyawun halaye,
Na gyara nawa irin naki.
8.
Da
farko dai ba kya gulma,
Don ke kin riƙe bakinki.
9.
Ba
ka giba ba zunɗe,
Wannan ba ya a halinki.
10. Wurin wani ba kya
yi da wani,
Zaɓar kyawun halinki.
11. Wurin wata ba kya
yi da wata,
Wannan ma na shaide ki.
12. Wurin wata ba kya
yi da wani,
Kowa ma na shaidan ki.
13. Wurin wani ba kya
yi da wata,
An ciri tuta an ba ki.
14. A’isha wai kin san
me ne?
Kin shero ni da kunyarki.
15. Da ma dai Manzo ya
sa,
Kunya cikin addininki.
16. Ash’ab kin ma san
me ne?
Kin burgen da kawaicinki.
17. Malam ya furta
hadisi,
Ko nan sai da na tuno ki.
18. Ya ce kawaici shi
ne,
Cikon halayen kirki.
19. A’isha na fara ƙaunar ki,
Tun da na gane riƙon kanki.
20. Ba kit taba kula
mazaje ba,
Kin riƙe dokar Sarkinki.
21. Wayyo! Ni kam na
faɗo,
Zan yo zancen nan gun ki.
22. A baya na so
soyayya,
Ɗan ɗis ne sha
kuruminki.
23. Sai kuma hali ya
bambanta,
Silan alfarmar samun ki.
24. Hani ga Allah
baiwa ce,
Na ga misali ni kanki.
25. To don Allah yafe
min,
Na dai daidaita tafarki.
26. Humaira ko da
suturarki,
Na nuna kyawon halinki.
27. Hijaban nan dogi
naki,
Da ke rufe sura ta jikinki.
28. Kaurinsu ya ko
cancanta,
Daidai umarnin Manzonki.
29. Duhunsu ya cika ƙima,
Ya nuna tsarkin halinki.
30. Da a ce dukka
Musulma,
Tana shiga fasalin taki.
31. Do alfasha za ta
ragu,
Za a samu mutan kirki.
32. Wasu ko na sanya
hijabi,
Amma sun kauce tafarki.
33. A fili su nuna na ƙwarai ne,
A zuci ko a sha mamaki.
34. Ke dai kin kauce
wannan,
Allah shi za ya biya ki.
35. Humaira mene ne
sirri?
36. Sinadari na
nutsuwarki?
37. Ciwon mace ai sai
mace,
Zan nemo alfarmarki-
38. Ki sanya aji na
musamman,
Domin koya kalamanki.
39. Yadda kike tsaro
zance,
Don mata su yi koyin ki.
40. Su ma ko sa ɗan burge,
Ko sa kwaikwayi halinki.
41. Humaira riƙon addininki,
Shi ne ya ƙaran ƙaunarki.
42. Kamun kai da
ibadarki,
Na kasa gane tamkarki.
43. Ba ma salla ga
kari ba-
Kushu’in yayin sallarki.
44. Nafilfilin da kike
tashi,
Sun ƙara mini ƙaunarki.
45. Kin san na miki
sunaye,
Har jaruma na kira ki.
46. Duba nai ga
ibadarki,
Azumi jiki ne a gare ki.
47. Kyautar da kike yi
Hummy,
Na nuna kyawon halin ki.
48. Sadakar nan da
kika saba,
Allah yi za ya biya ki.
49. Saliha da na ce
ran nan,
Siffa ce ta ɗabi’unki.
50. Kamila da na sanya
maki,
Daidai ne da salo naki.
51. Mumina da na ce ko
da ke,
Sharhi ne na ibadunki.
52. Natsattsiya na laƙa miki,
Daidai ne da kamalarki.
53. Zance na ƙwarai sadaka ne,
Ya zan ƙiyasta ladanki?
54. Ash’ab wai yaya
akai ne-
Hassada ba ta tsarinki?
55. A’isha mene ne
sirrin-
Baƙin hali ba ya ranki?
56. Humaira ya kika
soma ne-
Ganin waɗai bai tsarinki?
57. Hummy yaya kinka
yi ne-
Ƙyashi ba ya layinki?
58. Humaira yaya kika
soma-
Saurin
fushi bai damun ki?
59. Hajiya mene mafari
ne?
Abin wani bai damun ki?
60. Ke dai kin kama
halali,
Haram ba ya a ajandarki.
61. Ina ƙaunar ki Humaira,
Musamman domin zumuntarki.
62. Halin nan na
ziyararki,
Ya ƙara cusan ƙaunarki.
63. Fara’arki Babbar
Yarinya,
Ta ƙara sa ni ina son ki.
64. Humaira daure da
waɗannan,
Kar da ki sauya halin kirki.
65. Da kin haka Allah
zai so ki,
Albarka ko yana ba ki.
66. Ki yi mana addu’a
kullum,
Da ke da ni masoyinki.
67. Iyaye da ‘yan
uwanmu duka,
Da dukka musulmai ‘yan kirki.